Skip to content

Beth-shean

5 verses

32.5000, 35.5000 Duba a Google Maps

Ayoyin da suka ambaci Beth-shean

  1. A yanki tsakanin Issakar da Asher, Manasse yana da waɗannan wurare, Bet-Sheyan, Ibileyam da ƙauyukanta, da mazaunan Dor da ƙauyukanta, da mazaunan En Dor da ƙauyukanta, da mazaunan Ta’anak da ƙauyukanta, da mazaunan Megiddo da ƙauyukanta (Na uku cikin jerin shi ne Nafot).

  2. Mutanen Yusuf suka amsa suka ce, “Ƙasar kan tudu ba ta ishe mu ba, ga kuma Kan’aniyawan da suke zama a filin, da waɗanda suke Bet-Sheyan da ƙauyukanta, da waɗanda suke Kwarin Yezireyel, duk suna da keken yaƙin ƙarfe.”

  3. Amma Manasse ba su kori mutane Bet-Sheyan ko Ta’anak ko Dor ko Ibileyam ko Megiddo tare da ƙauyukansu ba, gama Kan’aniyawa sun dāge su zauna a wannan ƙasa.

  4. Ba’ana ɗan Ahilud, shi ne a Ta’anak da Megiddo, da kuma dukan Bet-Sheyan biye da Zaretan ƙasa da Yezireyel, daga Bet-Sheyan zuwa Abel-Mehola a ƙetaren Yokmeyam;

  5. A iyakokin Manasse akwai Bet-Sheyan, Ta’anak, Megiddo da Dor, tare da ƙauyukansu. Zuriyar Yusuf ɗan Isra’ila ta zauna a waɗannan garuruwa.