Jesus
An kuma san shi da: Jesus Christ, Immanuel, Emmanuel, Christ
Ayoyin da suka ambaci Jesus
Ba ka gaskata cewa ina cikin Uba, Uba kuma yana cikina ba? Kalmomin da nake gaya muku ba na kaina ba ne. Ai, Uban da yake raye a cikina ne yake aikinsa.
Ku gaskata ni sa’ad da na ce ina cikin Uba, Uba kuma yana cikina. Ko kuwa ku gaskata ni saboda ayyukan banmamakin su kansu.
Gaskiya nake gaya muku, duk wanda yake da bangaskiya gare ni, zai yi abubuwan da ni nake yi. Zai ma yi abubuwa masu girma fiye da waɗannan, don zan tafi wurin Uba.
Kuma zan yi duk abin da kuka roƙa cikin sunana, don Ɗan ya kawo ɗaukaka ga Uban.
Za ku iya roƙe ni kome a cikin sunana, zan kuwa yi.
“In kuna ƙaunata za ku yi biyayya da umarnina.
Zan kuwa roƙi Uba, zai kuwa ba ku wani Mai Taimakon da zai kasance tare da ku har abada,
Ruhun gaskiya. Duniya ba ta iya karɓarsa, don ba ta ganinsa ba ta kuma san shi ba. Amma kun san shi, saboda yana zama tare da ku zai kuma kasance a cikinku.
Ba zan bar ku marayu ba; zan zo wurinku.
Ba da daɗewa ba, duniya ba za tă ƙara ganina ba, amma za ku gan ni. Don ina raye, ku ma za ku rayu.
A ranan nan za ku sani ina cikin Uba, ku kuma kuna cikina, ni kuma ina cikinku.
Duk wanda yake da umarnaina yana kuma yin biyayya da su, shi ne wanda yake ƙaunata. Wanda yake ƙaunata kuwa Ubana zai ƙaunace shi, ni ma zan ƙaunace shi, in kuma bayyana kaina gare shi.”
Sai Yahuda (ba Yahuda Iskariyot ba) ya ce, “Ubangiji, me ya sa za ka bayyana kanka gare mu amma ba ga duniya ba?”
Yesu ya amsa ya ce, “Duk mai ƙaunata, zai yi biyayya da koyarwata. Ubana zai ƙaunace shi, za mu kuwa zo wurinsa mu zauna tare da shi.
Wanda ba ya ƙaunata ba zai yi biyayya da koyarwata ba. Waɗannan kalmomin da kuke ji ba nawa ba ne; na Uba ne da ya aiko ni.
“Duk wannan na faɗa ne yayinda ina tare da ku.
Amma Mai Taimako, Ruhu Mai Tsarki, wanda Uba zai aiko cikin sunana, zai koya muku kome, zai kuma tuna muku duk abin da na faɗa muku.
Salama na bari tare da ku; salamata nake ba ku. Ba kamar yadda duniya take bayarwa nake ba ku ba. Kada zuciyarku ta ɓaci kada kuma ku ji tsoro.
“Kun dai ji na ce, ‘Zan tafi in kuma sāke dawo wurinku.’ In har kuna ƙaunata, za ku yi farin ciki cewa za ni wurin Uba, domin kuwa Uban ya fi ni.
Na faɗa muku tun kafin yă faru, domin in ya faru, ku gaskata.
Ba zan ƙara yi muku magana ba, gama mai mulkin duniyan nan yana zuwa. Ba shi da iko a kaina,
amma dole duniya ta koya cewa ina ƙaunar Uba, ina kuma yin yadda Ubana ya umarce ni. “Ku zo, mu bar nan.
“Ni ne kuringar inabi na gaskiya, Ubana kuwa shi ne manomin.
Yakan sare kowane reshe a cikina da ba ya ’ya’ya, amma yakan ƙundume kowane reshe da yake ba da ’ya’ya, domin yă ƙara ba da ’ya’ya.
Kun riga kun zama masu tsabta saboda maganar da na yi muku.