Tsallake zuwa abun ciki

Jesus

3,872 ayoyi · 6 'yan gida

An kuma san shi da: Jesus Christ, Immanuel, Emmanuel, Christ

Ayoyin da suka ambaci Jesus

Tace bisa littafi
  1. Na gama ka da Allah, da Kiristi Yesu, da kuma zaɓaɓɓun mala’iku, ka kiyaye waɗannan abubuwa ƙwarai da gaske, kada ka nuna bambanci.

  2. Duk waɗanda suke ƙarƙashin bauta, ya kamata su ɗauki iyayengijinsu a kan sun cancanci girmamawa matuƙa, don kada a ɓata sunan Allah da kuma koyarwarmu.

  3. In wani yana koyarwar ƙarya bai kuma yarda da sahihiyar koyarwar Ubangijinmu Yesu Kiristi da kuma koyarwa ta tsoron Allah ba,

  4. Na umarce ka, a gaban Allah mai ba da rai ga kome, da kuma Kiristi Yesu wanda yayinda yake ba da shaida a gaban Buntus Bilatus ya yi kyakkyawar shaida,

  5. ka kiyaye wannan umarni ba tare da wani aibi ko abin zargi ba har yă bayyanuwar Ubangijinmu Yesu Kiristi,

  6. wanda Allah zai kawo a daidai lokaci, Allah, mai albarka wanda yake kaɗai Mai Mulki, Sarkin sarakuna da Ubangijin iyayengiji,

  7. Bulus, manzon Kiristi Yesu ta wurin nufin Allah, bisa ga alkawarin rai wanda yake cikin Kiristi Yesu,

  8. Zuwa ga Timoti, ƙaunataccen ɗana. Alheri, jinƙai da salama daga Allah Uba da kuma Kiristi Yesu Ubangijinmu, su kasance tare da kai.

  9. Saboda haka kada ka ji kunyar ba da shaida game da Ubangijinmu, ko kuwa ka ji kunyata, ni da nake ɗan sarƙa saboda shi. Sai dai ka haɗa kai tare da ni cikin shan wahala saboda bishara ta wurin ikon Allah,

  10. wanda ya cece mu ya kuma kira mu ga rayuwar tsarki ba saboda wani abin da muka yi ba sai dai saboda nufinsa da kuma alherinsa. An ba mu wannan alheri cikin Kiristi Yesu tun fil azal,

  11. amma yanzu an bayyana ta ta wurin bayyanuwar Mai Cetonmu, Kiristi Yesu, wanda ya hallaka mutuwa ya kuma kawo rai da rashin mutuwa a sarari ta wurin bishara.

  12. Shi ya sa nake shan wahalar da nake sha. Duk da haka ba na jin kunya, domin na san wanda na gaskata da shi, na kuma tabbata cewa yana iya kiyaye abin da na danƙa masa amana don wancan rana.

  13. Abin da ka ji daga gare ni, ka kiyaye shi kamar tsarin sahihiyar koyarwa, cikin bangaskiya da ƙauna cikin Kiristi Yesu.

  14. Bari Ubangiji yă yi wa iyalin Onesiforus jinƙai, domin sau da dama yakan wartsakar da ni, bai kuma ji kunyar sarƙoƙina ba.

  15. Bari Ubangiji yă sa yă sami jinƙai daga Ubangiji a wancan ranar! Ka sani sarai yadda ya taimake ni a hanyoyi dabam-dabam a Afisa.

  16. Kai kuma, ɗana, ka yi ƙarfi cikin alherin da yake cikin Kiristi Yesu.

  17. Ka jure wa shan wahala tare da mu kamar soja mai kyau na Kiristi Yesu.

  18. Ka yi tunani a kan abin da nake faɗi, gama Ubangiji zai ba ka ganewa cikin dukan wannan.

  19. Ka tuna da Yesu Kiristi, wanda aka tā da shi daga matattu, zuriyar Dawuda, wanda shi ne bisharata,

  20. Saboda haka nake jure kome saboda zaɓaɓɓu, domin su ma su sami ceton da yake cikin Kiristi Yesu, tare da madawwamiyar ɗaukaka.

  21. Ga wata magana tabbatacciya, “In muka mutu tare da shi, za mu rayu tare da shi;

  22. in muka jimre, za mu yi mulki tare da shi. In muka yi mūsunsa, shi ma zai yi mūsunmu;

  23. in ba mu da aminci, shi dai mai aminci ne, domin shi ba zai iya mūsun kansa ba.”

  24. Ka riƙa tuna masu da haka, ka kuma gama su da Allah, kada su yi jayayya a kan maganganu, don ba ta da wani amfani, sai ɓad da masu ji kawai take yi.

  25. Duk da haka, ƙaƙƙarfan tushen nan na Allah yana nan daram, an hatimce shi da wannan rubutu, “Ubangiji ya san waɗanda suke nasa,” da kuma, “Duk wanda ya bayyana yarda ga sunan Ubangiji, to, dole yă yi nesa da aikata mugunta.”