Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Visions

137 ayoyi · 32 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ku ji wannan, ku da kuke tattake masu bukata kuka kori matalautan ƙasar.

  2. Kuna cewa, “Yaushe Sabon Wata zai wuce don mu sayar da hatsi, Asabbaci ta wuce, don mu sayar da alkama?” Mu yi awo da ma’aunin zalunci mu ƙara kuɗin kaya mu kuma cutar da mai saya,

  3. mu sayi matalauta da azurfa masu bukata kuma da takalmi, mu sayar da alkamar haɗe da yayi.

  4. Na ga Ubangiji yana tsaye a gaban bagade, ya kuma ce, “Bugi kan ginshiƙan don madogaran ƙofa su girgiza. Saukar da su a kan dukan mutane; waɗanda ba su mutu ba zan kashe su da takobi. Ba mutum guda da zai tsere, babu wani da zai tsira.

  5. Sa’an nan Ubangiji ya amsa ya ce, “Ka rubuta wannan ru’uya ka bayyana ta a fili a kan alluna don mai shela yă ruga da ita, yă kai.

  6. Da dare, na ga wahayi, a gabana kuwa ga mutum a kan jan doki! Yana tsaye a cikin itatuwa masu furanni, a bayansa a cikin itatuwan ci-zaƙi, a bayansa kuwa akwai dawakai masu ruwan ja, ruwan ƙasa-ƙasa da kuma ruwan fari.

  7. Sa’an nan ya nuna mini Yoshuwa babban firist a tsaye a gaban mala’ikan Ubangiji, Shaiɗan kuma yana tsaye a damansa don yă tuhume shi.

  8. Ya tambaye ni ya ce, “Me ka gani?” Na amsa, na ce, “Na ga wurin ajiye fitilan zinariya da kwano a kai, da kuma fitilu bakwai a kansa, da butocin kai wa fitilu mai guda bakwai.

  9. Sai ya tambaye ni ya ce, “Me ka gani?” Sai na amsa na ce, “Na ga naɗaɗɗen littafi mai firiya, tsawonsa ƙafa talatin da fāɗinsa kuma ƙafa goma sha biyar.”

  10. Na sāke ɗaga kai sama, sai ga kekunan yaƙi guda huɗu a gabana suna fitowa tsakanin duwatsu guda biyu, duwatsun tagulla!

  11. Sai mala’ikan Ubangiji ya bayyana gare shi, tsaye a dama da bagaden turare.

  12. Da ya fito, bai iya yin musu magana ba. Sai suka gane, ya ga wahayi ne a haikali, domin ya dinga yin musu alamu, amma ya kāsa yin magana.

  13. amma ba su sami jikinsa ba. Sun dawo sun faɗa mana cewa, sun ga wahayi na mala’iku, da suka ce yana da rai.

  14. “Bayan shekaru arba’in suka wuce, sai mala’ika ya bayyana ga Musa cikin harshen wuta a ɗan itace a hamada kusa da Dutsen Sinai.

  15. Sa’ad da ya ga haka, ya yi mamakin abin da ya gani. Da ya yi kusa domin ya duba sosai, sai ya ji muryar Ubangiji ta ce,

  16. ‘Ni ne Allahn kakanninka, Allah na Ibrahim, Ishaku, da kuma Yaƙub.’ Sai Musa ya yi rawan jiki don tsoro, bai kuwa yi karambanin dubawa ba.

  17. Da ya yi kusa da Damaskus a kan hanyarsa, ba zato ba tsammani sai wani haske daga sama ya haskaka kewaye da shi.

  18. Yanzu ka tashi ka shiga cikin birnin, za a kuma gaya maka abin da dole za ka yi.”

  19. A Damaskus kuwa akwai wani almajiri mai suna Ananiyas. Ubangiji ya kira shi a cikin wahayi ya ce, “Ananiyas!” Ananiyas ya amsa, “Ga ni, ya Ubangiji.”

  20. Ubangiji ya ce masa, “Je gidan Yahuda da yake a Miƙaƙƙen Titi ka yi tambaya ko akwai wani mutum daga Tarshish mai suna Shawulu, gama ga shi yana addu’a.

  21. Cikin wahayi ya ga wani mutum mai suna Ananiyas ya zo ya sa hannuwansa a kansa don yă sāke samun ganin gari.”

  22. Wata rana wajen ƙarfe uku na yamma ya ga wahayi. A sarari ya ga wani mala’ikan Allah, wanda ya zo wajensa ya ce, “Korneliyus!”

  23. Wajen tsakar rana kashegari yayinda suke cikin tafiyarsu suna kuma dab da birnin, sai Bitrus ya hau bisan rufin gida yă yi addu’a.

  24. Yunwa ta kama shi ya kuwa so yă ci wani abu, yayinda ake shirya abinci, sai wahayi ya zo masa.

  25. Ya ga sama ya buɗe ana kuwa saukowa wani abu ƙasa kamar babban mayafi zuwa duniya ta kusurwansa huɗu.