Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Visions

137 ayoyi · 32 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Cikinsa kuwa akwai kowace irin dabba mai ƙafa huɗu da masu ja da ciki na duniya da kuma tsuntsayen sararin sama.

  2. Sa’an nan wata murya ta ce masa, “Bitrus, ka tashi. Ka yanka ka ci.”

  3. Bitrus ya ce, “Sam, Ubangiji! Ban taɓa cin wani abu marar tsarki ko marar tsabta ba.”

  4. Muryar ta yi magana da shi sau na biyu ta ce, “Kada ka ce da abin da Allah ya tsarkake marar tsarki.”

  5. Wannan ya faru har sau uku, sai nan da nan aka ɗauke mayafin zuwa sama.

  6. Tun Bitrus yana cikin tunani game da ma’anar wahayin nan, sai ga mutanen da Korneliyus ya aika sun sami gidan Siman suna kuma tsaye a ƙofar.

  7. “Ina a birnin Yoffa ina addu’a, sai ga wahayi ya zo mini. Na ga ana sauko da wani abu kamar babban mayafi daga sama ta kusurwansa huɗu, ya kuma sauko inda nake.

  8. Da dare Bulus ya ga wahayin wani mutumin Makidoniya yana tsaye yana roƙonsa cewa, “Ka zo Makidoniya ka taimake mu.”

  9. Wata rana da dad dare, Ubangiji ya yi magana da Bulus a cikin wahayi ya ce, “Kada ka ji tsoro; ka ci gaba da yin magana, kada ka yi shiru.

  10. na ga Ubangiji yana magana. Ya ce mini, ‘Maza! Ka bar Urushalima, gama ba za su yarda da shaidarka game da ni ba.’

  11. Jiya da dare wani mala’ikan Allahn da nake nasa nake kuma bauta wa ya tsaya kusa da ni

  12. Sai na juya don in ga muryar da take magana da ni. Da na juya kuwa sai na ga alkukan fitilu bakwai na zinariya.