Skip to content

Chaldea

9 verses · 2 known names

An kuma san shi da: Chaldeans

30.9600, 46.1000 Duba a Google Maps

Ayoyin da suka ambaci Chaldea

  1. Ku bar Babilon, ku gudu daga Babiloniyawa! Ku yi shelar wannan da sowa ta farin ciki ku kuma furta shi. Ku aika shi zuwa iyakokin duniya; ku ce, “Ubangiji ya fanshi bawansa Yaƙub.”

  2. Saboda haka za a washe Babiloniyawa; dukan waɗanda suka washe ta za su ƙoshi,” in ji Ubangiji.

  3. “Zan sāka wa Babilon da dukan mazaunan Babilon a idanunku saboda dukan muguntar da suka aikata a Sihiyona,” in ji Ubangiji.

  4. Bari abin da aka yi wa jikinmu yă kasance a bisa Babilon,” in ji mazaunan Sihiyona. “Bari jininmu yă kasance a kan waɗanda suke zama a Babilon,” in ji Urushalima.

  5. Ruhu ya ɗaga ni sama ya kuma kawo ni ga masu zaman bauta a ƙasar Babilon cikin wahayin da Ruhun Allah ya bayar. Sa’an nan wahayin da na gani ya rabu da ni,

  6. Sai kika ƙara fasikancinki da ya haɗa da ƙasar cinikin Babilon, amma duk da haka ba ki ƙoshi ba.

  7. da ɗamara a gindinsu da rawuna a kansu suna kaɗawa falfal; dukansu sun yi kamar jarumawan kekunan yaƙin Babiloniyawa ’yan Kaldiya.

  8. Nan da nan da ta gan su, sai ta yi sha’awarsu ta aika da ’yan aika zuwa wurinsu a Kaldiya.

  9. Babiloniyawa da dukan Kaldiyawa, mutanen Fekod da Showa da Kowa, da dukan Assuriyawa, samari masu bansha’awa, dukan gwamnoni da manyan sojoji, hafsoshin keken yaƙin da mutane masu manyan matsayi, dukansu a bisa dawakai.