Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da High Places

21 ayoyi · 43 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. “ ‘Kaito! Kaitonki, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Bugu da ƙari a kan dukan waɗansu muguntarki,

  2. kin gina wa kanki ɗakunan sama da gidajen tsafi a kowane dandali.

  3. A kowane titi kin gina ɗakin tsafi kika kuma wulaƙanta kyanki, kina miƙa jikinki da ƙarin fasikanci ga duk mai wucewa.

  4. Kin yi karuwanci da Masarawa, maƙwabtanki masu kwaɗayi, kika tsokane ni har na yi fushi da ƙarin fasikancinki.

  5. Saboda haka na miƙa hannuna gāba da ke na kuma rage iyakarki; na ba da ke ga abokan gābanki masu haɗama, ’yan matan Filistiyawa, waɗanda suka sha mamaki saboda halinki na lalata.

  6. Kin kuma yi karuwanci da Assuriyawa, domin ba kya ƙoshi; kai ko bayan wannan, ba ki ƙoshi ba.

  7. Sai kika ƙara fasikancinki da ya haɗa da ƙasar cinikin Babilon, amma duk da haka ba ki ƙoshi ba.

  8. “ ‘Kina da rashin ƙarfi a zuci, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, sa’ad da kika yi duk waɗannan abubuwa, kina yi kamar karuwar da aka watsa!

  9. Sa’ad da kika gina ɗakunan samanki a kowane gefen titi kika kuma gina ɗakunan tsafinki a kowane dandali, ba kamar karuwa kike ba, domin kin karɓi kuɗi.

  10. “ ‘Ke mazinaciyar mace! Kin gwammace baƙi a maimakon mijinki!

  11. Kowace karuwa kan karɓi kuɗi, amma kina ba da kyautai ga dukan kwartayenki, kina ba su cin hanci don su zo wurinki daga ko’ina don alherai marasa ƙa’ida.

  12. Saboda haka cikin karuwancinki kin sha bamban da saura; babu wanda yake binki saboda alheranki. Ke dai dabam ce, gama kikan biya kuma ba mai biyanki.

  13. “ ‘Saboda haka, ke karuwa, ki ji maganar Ubangiji!

  14. Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa domin kin zubar da dukiyarki kika bayyana tsiraicinki cikin fasikancinki da kwartayenki, kuma saboda dukan gumakan banƙyamarki, kuma saboda kin ba su jinin ’ya’yansu,

  15. saboda haka zan tattara dukan kwartayenki, waɗanda kike jin daɗinsu, waɗanda kike ƙauna da waɗanda kike ƙi. Zan tattara su gāba da ke daga dukan kewaye zan kuma tuɓe ki a gabansu, za su kuwa ga dukan tsiraicinki.

  16. Zan hukunta ki da hukuncin matan da suke zina da kuma waɗanda suke zub da jini; zan kawo hakkin jini na fushina da kuma fushin kishina.

  17. Sa’an nan zan miƙa ki ga kwartayenki, za su kuwa rurrushe ɗakunan samanki su kuma farfashe ɗakunan tsafinki. Za su tuɓe miki tufafinki su kuma kwashe kayan adonki masu kyau su bar ki tsirara tik.

  18. Za su kawo taron jama’a a kanki, waɗanda za su jajjefe ki da dutse su sassare ki gunduwa-gunduwa da takubansu.

  19. Za su ƙone gidajenki su kuma hukunta ki a idon mata masu yawa. Zan kawo ƙarshen karuwancinki, ba za ki kuma ƙara biyan kwartayenki ba.

  20. Sa’an nan fushina a kanki zai huce fushin kishina kuma ya kwanta; zan huce ba kuwa zan ƙara yin fushi ba.

  21. “ ‘Domin ba ki tuna da kwanakin ƙuruciyarki ba amma kika husatar da ni da waɗannan abubuwa, tabbatacce zan sāka miki alhakin ayyukanki, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Ba kin ƙara lalata ga dukan waɗansu ayyuka masu banƙyamarki ba?