Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Visions: To Paul

10 ayoyi · 32 fannoni

Ayoyi game da To Paul

  1. Bayan mulkin Rehobowam ya kahu kamar sarki ya kuma yi ƙarfi, shi da dukan Isra’ila suka yi biris da dokar Ubangiji.

  2. Domin sun yi rashin biyayya ga Ubangiji, saboda haka Shishak sarkin Masar ya yaƙi Urushalima a shekara ta biyar ta Sarki Rehobowam.

  3. Da kekunan yaƙi dubu ɗaya da ɗari biyu da kuma mahayan dawakai dubu haɗe da mayaƙan Libiyawa, Sukkatawa da kuma Kushawa waɗanda suka wuce ƙidaya suka zo tare da shi daga Masar,

  4. ya ci biranen katanga na Yahuda har zuwa Urushalima.

  5. Da ya yi kusa da Damaskus a kan hanyarsa, ba zato ba tsammani sai wani haske daga sama ya haskaka kewaye da shi.

  6. Yanzu ka tashi ka shiga cikin birnin, za a kuma gaya maka abin da dole za ka yi.”

  7. Da dare Bulus ya ga wahayin wani mutumin Makidoniya yana tsaye yana roƙonsa cewa, “Ka zo Makidoniya ka taimake mu.”

  8. Wata rana da dad dare, Ubangiji ya yi magana da Bulus a cikin wahayi ya ce, “Kada ka ji tsoro; ka ci gaba da yin magana, kada ka yi shiru.

  9. na ga Ubangiji yana magana. Ya ce mini, ‘Maza! Ka bar Urushalima, gama ba za su yarda da shaidarka game da ni ba.’

  10. Jiya da dare wani mala’ikan Allahn da nake nasa nake kuma bauta wa ya tsaya kusa da ni