Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Visions: To Moses

5 ayoyi · 32 fannoni

Ayoyi game da To Moses

  1. A can mala’ikan Ubangiji ya bayyana a gare shi cikin harshen wuta, a ƙaramin itace. Musa ya lura cewa ko da yake wuta na ci ƙaramin itacen, amma bai ƙone ba.

  2. Sai Musa ya ce, “Wannan abin mamaki ne, don me wannan itace bai ƙone ba? Bari in matso kusa in gani.”

  3. “Bayan shekaru arba’in suka wuce, sai mala’ika ya bayyana ga Musa cikin harshen wuta a ɗan itace a hamada kusa da Dutsen Sinai.

  4. Sa’ad da ya ga haka, ya yi mamakin abin da ya gani. Da ya yi kusa domin ya duba sosai, sai ya ji muryar Ubangiji ta ce,

  5. ‘Ni ne Allahn kakanninka, Allah na Ibrahim, Ishaku, da kuma Yaƙub.’ Sai Musa ya yi rawan jiki don tsoro, bai kuwa yi karambanin dubawa ba.