Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Christ Jesus

607 ayoyi · 25 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ba su gane cewa yana yin musu magana game da Ubansa ba ne.

  2. Saboda haka Yesu ya ce, “Sa’ad da kuka ɗaga Ɗan Mutum, a sa’an nan ne za ku san cewa ni ne wannan da na ce nake. Ni kuwa ba na yin kome ni kaɗai, sai in dai faɗi abin da Uba ya koya mini.

  3. Wanda kuwa ya aiko ni yana tare da ni; bai bar ni ni kaɗai ba, domin kullum ina aikata abin da ya gamshe shi.”

  4. Sa’ad da yake cikin magana, da yawa suka ba da gaskiya gare shi.

  5. Amma domin ina faɗin gaskiya, ba kwa gaskata!

  6. Akwai waninku da zai iya haƙaƙƙewa na taɓa yin zunubi? In kuwa gaskiya na faɗa, me ya sa ba kwa gaskata ni?

  7. Wanda yake na Allah, yakan ji abin da Allah yake faɗi. Abin da ya sa ba kwa jin sa kuwa shi ne don ku ba na Allah ba ne.”

  8. Sai waɗansu daga cikin Farisiyawa suka ce, “Mutumin nan ba daga Allah yake ba, don ba ya kiyaye ranar Asabbaci.” Amma waɗansu suka yi tambaya suka ce, “Yaya mutum mai zunubi zai yi irin abubuwan banmamaki haka?” Sai ra’ayinsu ya sha bamban.

  9. A ƙarshe suka sāke koma ga makahon suka ce, “Kai fa, me ka gani game da shi? Idanunka ne fa ya buɗe.” Sai mutumin ya ce, “Tab, ai, shi annabi ne.”

  10. Ni ne ƙofar; duk wanda ya shiga ta wurina zai sami ceto. Zai riƙa shiga yă fita yă kuwa sami wurin kiwo.

  11. Ɓarawo yakan zo don yă yi sata ne kawai da kisa da kuma ɓarna. Ni kuwa na zo ne don su sami rai, su kuma same shi a yalwace.

  12. “Ni ne makiyayi mai kyau. Makiyayi mai kyau yakan ba da ransa domin tumakin.

  13. Abin da ya sa Ubana yake ƙaunata ke nan, domin ina ba da raina, in ɗauko shi kuma.

  14. Ba mai karɓe mini rai, ina dai ba da shi. Ina da iko in ba da shi, ina da iko in ɗauko shi kuma. Wannan umarni kuwa daga wurin Ubana na karɓo shi.”

  15. Da yawa daga cikinsu suka ce, “Yana da aljani, yana kuma hauka. Don me za ku saurare shi?”

  16. Amma waɗansu suka ce, “Kai, waɗannan kalmomi ba na mai aljani ba ne. Anya, aljani yana iya buɗe idanun makaho?”

  17. Amma waɗansunsu suka je wurin Farisiyawa suka gaya musu abin da Yesu ya yi.

  18. Sai manyan firistoci da Farisiyawa suka kira taron Majalisa. Suka yi tambaya suna cewa, “Me muke yi ne? Ga mutumin nan yana yin abubuwan banmamaki masu yawa.

  19. In fa muka ƙyale shi ya ci gaba da haka, kowa zai gaskata da shi, Romawa kuma su zo su karɓe wurinmu su kuma ƙwace ƙasarmu.”

  20. Duk mai ƙaunar ransa, zai rasa shi, duk mai ƙin ransa a wannan duniya, zai kiyaye shi har yă zuwa rai madawwami.

  21. Duk wanda zai bauta mini dole yă bi ni, inda kuma nake, a can bawana zai kasance. Ubana zai girmama wanda yake bauta mini.

  22. Amma ni, sa’ad da aka ɗaga ni daga ƙasa, zan ja dukan mutane gare ni.”

  23. Ya faɗa haka ne don yă nuna irin mutuwar da zai yi.

  24. Sai taron suka ce, “Ahab, Dokarmu ta gaya mana cewa, Kiristi zai kasance har abada, to, yaya za ka ce, ‘Dole ne a ɗaga Ɗan Mutum?’ Wane ne wannan ‘Ɗan Mutum’?”

  25. Na zo cikin duniya a kan ni haske ne, don duk wanda ya gaskata da ni, kada yă zauna a cikin duhu.