Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Afflictions of the Wicked

95 ayoyi · 20 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Saboda haka Ubangiji Allahnsa ya miƙa shi ga sarkin Aram. Arameyawa suka ci shi a yaƙi, suka kuma kwashe mutanensa da yawa a matsayin ’yan kurkuku, suka kawo Damaskus. Ya kuma ba da shi ga sarkin Isra’ila, wanda ya jijji masa a yaƙi.

  2. A rana ɗaya Feka ɗan Remaliya ya kashe sojoji dubu ɗari da dubu ashirin a Yahuda, domin Yahuda sun yashe Ubangiji Allah na kakanninsu.

  3. Zikri, wani jarumin Efraim, ya kashe Ma’asehiya ɗan sarki, Azrikam hafsa mai lura da fada, da kuma Elkana, mataimakin sarki.

  4. Isra’ilawa suka kame kamammu daga ’yan’uwansu mata, ’ya’ya maza da kuma ’ya’ya mata dubu ɗari biyu. Suka kuma kwashe ganima mai yawan gaske, waɗanda suka kwasa zuwa Samariya.

  5. Cikin lokacin wahalarsa Sarki Ahaz ya ƙara zama marar aminci ga Ubangiji.

  6. “Amma nan da nan, da suka sami hutu, sai suka sāke aikata abin da yake mugu a idonka. Sai ka yashe su ga hannun abokan gābansu don su yi mulki a kansu. Sa’ad da suka yi kuka kuma gare ka, ka ji daga sama, cikin jinƙanka kuma ka fisshe su sau da sau.

  7. “Ka gargaɗe su su dawo ga dokarka, amma suka yi fariya, suka bijire wa umarnanka. Suka yi zunubi game da farillanka waɗanda ta wurinsu ne mutum zai rayu in ya yi biyayya da su. Cikin taurinkai suka juye bayansu daga gare ka, suka zama masu taurinkai, suka kuma ƙi su saurara.

  8. Dukan kwanakin ransa mugu yana shan wahala, wahala kaɗai zai yi ta sha.

  9. Ɓacin rai da baƙin ciki sun cika shi, kamar sarkin da yake shirin yaƙi,

  10. “Ko da yake mugunta tana da daɗi a bakinsa kuma yana ɓoye ta a harshensa,

  11. ko da yake ba zai iya rabuwa da ita ba, yana kuma ajiye ta a bakinsa,

  12. duk da haka abincin da ya ci zai zama da tsami a cikin cikinsa; zai zama kamar dafin maciji a cikinsa.

  13. Zai haras da dukiyar da ya haɗiye; Allah zai sa cikinsa yă haras da su.

  14. Zai sha dafin maciji; sarar maciji mai dafi za tă tashe shi.

  15. Ba zai ji daɗin koguna da rafuffuka masu kwarara da zuma da madara ba.

  16. Dole yă ba da abin da ya yi gumi kafin yă samu, ba zai ci ba; ba zai ji daɗin ribar da ya samu daga kasuwancinsa ba.

  17. “Duk da haka, sau nawa fitilar mugu take mutuwa? Sau nawa bala’i yake auka masa, ko Allah ya taɓa hukunta mugu cikin fushi?

  18. Azaban mugu da yawa suke, amma ƙaunar Ubangiji marar ƙarewa kan kewaye mutumin da ya dogara gare shi.

  19. amma Ubangiji yakan yi dariyar mugaye, gama ya sani ranarsu tana zuwa.

  20. Allah, yana mulki har abada, zai ji su yă kuma azabtar da su, Sela mutanen da ba sa taɓa canja hanyoyinsu kuma ba sa tsoron Allah.

  21. Amma Allah zai harbe su da kibiyoyi; nan da nan za a buge su su fāɗi.

  22. Zai juya harshensu a kansu yă kuma kawo su ga hallaka; duk waɗanda suka gan su za su kaɗa kai, suna musu ba’a.

  23. Dukan mutane za su ji tsoro; za su yi shelar ayyukan Allah su kuma yi tunanin abin da ya aikata.

  24. Saboda haka mutanensu sun juya gare su suna kuma shan ruwa a yalwace.

  25. Duba yadda suka hallaka farat ɗaya, razana ta share su gaba ɗaya!