Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Afflictions of the Wicked

95 ayoyi · 20 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Waɗansu suka zama wawaye ta wurin hanyoyinsu na tayarwa suka kuwa sha wahala saboda laifofinsu.

  2. Zan yi muku dariya sa’ad da masifa ta same ku, zan yi muku ba’a sa’ad da bala’i ya same ku,

  3. sa’ad da bala’i ya sha kanku kamar hadiri, sa’ad da masifa ta share ku kamar guguwa, sa’ad damuwa da wahala suka mamaye ku.

  4. da yake ba su karɓi shawarata ba suka kuwa yi kunnen ƙashi ga tsawatata,

  5. za su sami sakayyar abubuwan da suka yi su kuma ƙoshi da sakayyar makircinsu.

  6. Kada ka ji tsoron masifar da za tă faru farat ɗaya ko lalacin da yakan auka wa mugaye,

  7. gama Ubangiji zai zama ƙarfin halinka zai kuwa kiyaye ƙafarka daga fāɗawa a tarko.

  8. Saboda haka masifa za tă fāɗa farat ɗaya; za a hallaka shi nan da nan, ba makawa.

  9. Dukan kwanakinsa aikinsa damuwa ce da ɓacin zuciya; ko da dare ma hankalinsa ba a kwance yake ba. Wannan ma ba shi da amfani.

  10. Amma mutanen ba su juyo wurin wanda ya buge su ba, balle su nemi Ubangiji Maɗaukaki.

  11. wannan zunubi zai zama muku kamar bango mai tsayi, tsagagge da yake kuma fāɗuwa, da zai rushe nan da nan, ba tsammani.

  12. Cikin ɗan lokaci ƙasa da shekara guda ku da kuke tsammani kuna da kāriya za ku yi rawar jiki; girbin ’ya’yan inabi zai kāsa, girbin ’ya’yan itatuwa kuma ba zai zo ba.

  13. “A banza na hukunta mutanenku; ba su yi gyara ba. Takobinku ya cinye annabawanku kamar zaki mai jin yunwa.

  14. Ya Ubangiji, idanunka ba sa ganin gaskiya? Ka buge su, amma ba su ji zafi ba; ka ragargaza su, amma suka ƙi su gyara. Fuskarsu ta ƙeƙashe fiye da dutse suka ƙi su tuba.

  15. Me ya sa kuke kuka a kan mikinku, wahalarku da ba ta da magani? Domin laifinku da girma yake da kuma zunubanku masu yawa na yi muku waɗannan abubuwa.

  16. “Ki yi kuka, ya Heshbon, gama an hallaka Ai! Ku tā da murya ku yi kuka, ya mazaunan Rabba! Ku sa tufafin makoki; ku ruga nan da can a cikin katanga, gama Molek zai tafi bauta, tare da firistocinsa da kuma fadawansa.

  17. Zan kawo razana a kanki daga waɗanda suke kewaye da ke,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. “Za a kore kowannenku, babu wani da zai tattara masu gudun hijira.

  18. “ ‘Yanzu ƙazantarki ita ce lalaci. Domin na yi ƙoƙari in tsabtacce ke amma ba ki tsabtattu daga ƙazantarki ba, ba za ki ƙara yin tsabta ba sai hasalata a kanki ya kwanta.

  19. Zan yi hukunci a kansa da annoba da kuma zub da jini; zan yi ruwa mai yawa da ƙanƙara da kibiritu mai cin wuta a kansa da a kan sojojinsa da kuma a kan al’ummai masu yawa da suke tare da shi.

  20. Ta haka zan nuna girmana da kuma tsarkina, zan sanar da kaina a gaban al’ummai masu yawa. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji.’

  21. “Na bar ku da yunwa a kowace birni, da kuma rashin abinci a kowane gari, duk da haka ba ku juyo gare ni ba,” in ji Ubangiji.

  22. “Na kuma hana muku ruwan sama tun shuke-shuken suna wata uku kafin lokacin girbi. Na sa aka yi ruwan sama a wani gari, sai na hana a yi a wani gari. Wata gona ta sami ruwan sama; wata gona kuma ta bushe.

  23. Mutane suna tangaɗi daga gari zuwa gari suna neman ruwa amma ba su sami isashen ruwan sha ba, duk da haka ba ku juyo gare ni ba,” in ji Ubangiji.

  24. “Sau da yawa na ɓata gonakinku da fumfuna da kuma cuta. Fāri suka cinye itatuwanku na inabi da na ɓaure, da na zaitun duk da haka ba ku juyo gare ni ba,” in ji Ubangiji.

  25. “Na aiko muku annoba yadda na yi a Masar. Na karkashe samarinku da takobi, tare da kamammun dawakanku. Na cika hancinku da warin sansaninku, duk da haka ba ku juyo gare ni ba” in ji Ubangiji.