Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Religious Zeal

726 ayoyi · 5 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ta haka zan koyar wa masu laifi hanyoyinka, masu zunubi kuma za su komo gare ka.

  2. Amma ga waɗanda suke tsoronka, ka ɗaga tuta don a buɗe gāba da baka. Sela

  3. Gama na jimre da ba’a saboda kai, kunya kuma ta rufe fuskata.

  4. Ni baƙo ne a cikin ’yan’uwana, bare kuma ga ’ya’yan mahaifiyata maza;

  5. gama himma da nake yi wa gidanka yana ƙunata, kuma zagi na masu zaginka yana fāɗuwa a kaina.

  6. Tun ina yaro, ya Allah, ka koya mini har wa yau ina furta ayyukanka masu banmamaki.

  7. Ko sa’ad da na tsufa da furfura, kada ka yashe ni, ya Allah, sai na furta ikonka ga tsara mai zuwa, ƙarfinka ga dukan waɗanda suke zuwa.

  8. Har yaushe abokan gāba za su yi mana ba’a, ya Allah? Maƙiya za su ci gaba da ɓata sunanka har abada ne?

  9. Ka tuna da yadda abokin gāba ya yi maka ba’a, ya Ubangiji, yadda wawaye suka ɓata sunanka.

  10. Kada ka ba da ran kurciyarka ga namun jeji; kada ka manta har abada da rayukan mutanenka masu shan azaba.

  11. Ka kula da alkawarinka, domin akwai tashin hankali a kowane lungu mai duhu na ƙasar.

  12. Kada ka bar waɗanda ake danniya su sha kunya; bari matalauta da mabukata su yabe sunanka.

  13. Ka tashi, ya Allah, ka kāre muradinka; ka tuna yadda wawaye suka yi maka ba’a dukan yini.

  14. Kada ka ƙyale surutan ban haushi na maƙiyanka, ihun abokan gābanka, waɗanda suke ci gaba da yi.

  15. Wane ne zai yi gāba da mugaye domina? Wane ne zai ɗauki matsayi ya yi gāba da masu aikata mugunta domina?

  16. Ku rera ga Ubangiji, ku yabe sunansa; ku yi shelar cetonsa kowace rana.

  17. Ku furta ɗaukakarsa a cikin al’ummai, manyan ayyukansa a cikin dukan mutane.

  18. Ku faɗa cikin al’ummai, “Ubangiji yana mulki.” Duniya ta kahu daram, ba za a iya matsar da ita ba; zai yi wa mutane hukunci da gaskiya.

  19. Kowace safiya zan rufe bakunan dukan mugaye a ƙasar; zan yanke kowane mai aikata mugunta daga birnin Ubangiji.

  20. Ba gare mu ba, ya Ubangiji, ba gare mu ba amma ga sunanka yă sami ɗaukaka, saboda ƙaunarka da amincinka.

  21. Me ya sa al’ummai suke cewa, “Ina Allahnsu?”

  22. Fushi ya kama ni saboda mugaye, waɗanda suka keta dokokinka.

  23. Lokaci ya yi da za ka yi wani abu, ya Ubangiji; ana karya dokarka.

  24. Hawaye suna malalowa daga idanuna kamar rafi, gama ba a biyayya da dokarka.

  25. Kishina ya cinye ni ɗungum, gama abokan gābana sun yi biris da maganganunka.