Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Religious Zeal: General references

121 ayoyi · 5 fannoni

Ayoyi game da General references

Tace bisa littafi
  1. Amma in kuka ga ba za ku iya bauta wa Ubangiji ba, sai ku zaɓa yau wanda za ku bauta masa, ko allolin da kakanninku suka bauta musu a hayin Kogin Yuferites, ko kuma allolin Amoriyawa, waɗanda kuke zama a cikin ƙasarsu. Amma da ni da gidana, Ubangiji ne za mu bauta wa.”

  2. Sai mutanen suka amsa suka ce, “Allah ya kiyashe mu da rabuwa da Ubangiji Allahnmu, har a ce mu bauta wa waɗansu alloli!

  3. Amma sarki ya ce wa Arauna, “A’a, dole in biya ka saboda waɗannan. Ba yadda zan miƙa wa Ubangiji Allahna hadayun ƙonawa da bai ci mini kome ba.” Sai Dawuda ya saya, ya kuma biya masussukar, da shanun a bakin shekel hamsin na azurfa.

  4. Dawuda ya gina wa Ubangiji bagade a wurin, ya kuma miƙa masa hadaya ta ƙonawa, da hadaya ta salama. Sa’an nan Ubangiji ya amsa addu’o’in a madadin ƙasar, aka kuma kawar wa Isra’ila annoban.

  5. “Kai kuwa, in ka yi tafiya a gabana da mutunci a zuci da kuma gaskiya, kamar yadda Dawuda mahaifinka ya yi, ka yi dukan abin da na umarta, ka kuma yi biyayya da ƙa’idodina da kuma dokokina,

  6. Ko da yake bai cire masujadai da suke kan tuddai ba, zuciyar Asa ta kasance da aminci ɗungum ga Ubangiji dukan kwanakinsa.

  7. Na sani, Allahna, cewa kakan gwada zuciya, kakan kuma gamsu da mutunci. Dukan waɗannan abubuwa na bayar da yardar rai da kuma kyakkyawar niyya. Yanzu kuma da farin ciki na ga yadda mutanenka waɗanda suke a nan da yardar rai suka ba ka.

  8. Dukan Yahuda suka yi farin ciki game da rantsuwar domin sun yi rantsuwar gabagadi. Suka nemi Allah da gaske, suka kuma same shi. Saboda haka Ubangiji ya ba su hutu a kowane gefe.

  9. Duk da haka an sami wani abin kirki a wurinka, gama ka kawar da ginshiƙan Ashera a ƙasar, ka kuma sa zuciyarka a kan neman Allah.”

  10. A yi duk abin da Allah na sama ya ce don haikalin Allah na sama, sai a yi shi da himma. Me zai sa a jawo wa sarki da ’ya’yansa fushin Allah?

  11. Ko yanzu haka shaidata tana sama; wanda zai tsaya mini yana sama.

  12. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Maskil ne na ’Ya’yan Kora maza. Kamar yadda barewa take marmarin ruwan rafuffuka, haka raina yake marmarinka, ya Allah.

  13. Raina yana ƙishin Allah, Allah mai rai. Yaushe zan tafi in sadu da Allah ne?

  14. Amma ga waɗanda suke tsoronka, ka ɗaga tuta don a buɗe gāba da baka. Sela

  15. Ku rera ga Ubangiji, ku yabe sunansa; ku yi shelar cetonsa kowace rana.

  16. Ku furta ɗaukakarsa a cikin al’ummai, manyan ayyukansa a cikin dukan mutane.

  17. Ku faɗa cikin al’ummai, “Ubangiji yana mulki.” Duniya ta kahu daram, ba za a iya matsar da ita ba; zai yi wa mutane hukunci da gaskiya.

  18. Kishina ya cinye ni ɗungum, gama abokan gābana sun yi biris da maganganunka.

  19. ’Ya’yan itacen adali itacen rai ne, kuma duk mai samun rayuka mai hikima ne.

  20. Duk abin da hannunka yake yi, ka yi shi da dukan ƙarfinka, gama a cikin kabari in da za ka, babu aiki ko shirye-shirye, ko sani, ko hikima.

  21. Mutanenku za su sāke gina kufai na da su kuma daga tsofaffin harsashai; za a ce da ku Masu Gyaran Katangar da ta Rushe, Masu Farfaɗo da Tituna da kuma Wuraren zama.

  22. “Ki tashi, ki haskaka, gama haskenki ya zo, ɗaukakar Ubangiji ya taso a kanki.

  23. Na sa matsara a kan katangarki, ya Urushalima; ba za su taɓa yin shiru ba, dare da rana. Ku da kuke kira bisa sunan Ubangiji, kada ku ba kanku hutu,

  24. kuma kada ku ba shi hutu sai ya kafa Urushalima ya kuma mai da ita yabon duniya.

  25. Waɗanda suke da hikima za su haskaka kamar hasken samaniya, waɗanda kuma suka jagoranci waɗansu da yawa zuwa adalci, za su zama kamar taurari har abada abadin.