Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Religious Zeal: Exemplified by Paul

423 ayoyi · 5 fannoni

Ayoyi game da Exemplified by Paul

Tace bisa littafi
  1. Nan take ya fara wa’azi cikin majami’u cewa Yesu Ɗan Allah ne.

  2. Dukan waɗanda suka ji shi suka yi mamaki suka ce, “Ba shi ne mutumin da ya tā-da-na-zaune-tsaye a kan masu kira bisa ga wannan sunan a Urushalima ba? Ba ya zo nan ne don yă kai su a matsayin ’yan kurkuku ga manyan firistoci ba?”

  3. Duk da haka Shawulu ya yi ta ƙara ƙarfi, ya kuma rikitar da Yahudawan da suke zaune a Damaskus, ta wurin tabbatar musu cewa, Yesu shi ne Kiristi.

  4. Bayan kwanaki masu yawa, sai Yahudawa suka haɗa baki su kashe shi,

  5. amma Shawulu ya sami labarin shirinsu. Dare da rana suka yi fakonsa a ƙofofin birnin don su kashe shi.

  6. Amma almajiransa suka ɗauke shi da dare suka saukar da shi a cikin kwando ta taga a katanga.

  7. Da ya zo Urushalima, ya yi ƙoƙarin shiga cikin almajiran amma dukansu suka ji tsoronsa, ba su gaskata cewa tabbatacce shi almajiri ba ne.

  8. Amma Barnabas ya ɗauke shi ya kawo shi wurin manzanni. Ya gaya musu yadda Shawulu a kan hanyarsa ya ga Ubangiji kuma cewa Ubangiji ya yi magana da shi, da yadda a Damaskus ya yi wa’azi ba tsoro a cikin sunan Yesu.

  9. Saboda haka Shawulu ya zauna tare da su yana kai da kawowa a sake a cikin Urushalima, yana magana gabagadi a cikin sunan Ubangiji.

  10. Ya yi magana ya kuma yi muhawwara da Yahudawa masu jin Hellenanci, amma suka yi ƙoƙarin kashe shi.

  11. Yana miƙewa tsaye, sai Bulus ya yi musu alama da hannu ya ce, “Mutanen Isra’ila da kuma ku Al’ummai da kuke wa Allah sujada, ku saurare ni!

  12. Allahn mutanen Isra’ila ya zaɓi kakanninmu; ya kuma sa mutanen suka yi bunkasa yayinda suke zama a ƙasar Masar, da iko mai girma ya fitar da su daga ƙasar,

  13. ya kuma jure da halinsu har shekara arba’in a cikin hamada,

  14. ya tumɓuke ƙasashe bakwai a Kan’ana ya kuma ba da ƙasarsu gādo ga mutanensa.

  15. Dukan wannan ya ɗauki kusan shekaru 450. “Bayan wannan, Allah ya ba su alƙalai har zuwa zamanin annabi Sama’ila.

  16. Sa’an nan mutanen suka nemi a ba su sarki, Allah kuwa ya ba su Shawulu ɗan Kish, na kabilar Benyamin, wanda ya yi mulki shekaru arba’in.

  17. Bayan an kau da Shawulu, sai ya naɗa Dawuda ya zama sarkinsu. Ya kuma yi shaida game da shi cewa, ‘Na sami Dawuda ɗan Yesse, mutum ne da nake so a zuciyata; shi zai aikata dukan abin da nake so.’

  18. “Daga zuriyar mutumin nan ne Allah ya kawo wa Isra’ila Mai Ceto Yesu, kamar yadda ya yi alkawari.

  19. Kafin zuwan Yesu, Yohanna ya yi wa’azin tuba da baftisma ga dukan mutanen Isra’ila.

  20. Yayinda Yohanna yake kammala aikinsa ya ce, ‘Wa kuke tsammani ni nake? Ba ni ne shi ba. A’a, amma yana zuwa bayana, wanda ko takalmansa ma ban isa in kunce ba.’

  21. “Ya ku ’yan’uwa, ’ya’yan Ibrahim, da ku kuma Al’ummai masu tsoron Allah, a gare mu ne fa aka aiko wannan saƙon ceto.

  22. Mutanen Urushalima da masu mulkinsu ba su gane da Yesu ba, duk da haka cikin hukunta shi suka cika kalmomin annabawan da ake karantawa kowane Asabbaci.

  23. Ko da yake ba su same shi da wani dalilin da ya kai ga hukuncin kisa ba, suka roƙi Bilatus yă sa a kashe shi.

  24. Sa’ad da suka aikata duk abin da aka rubuta game da shi, sai suka saukar da shi daga itacen suka kuma sa shi a kabari.

  25. Amma Allah ya tashe shi daga matattu,