Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Religious Zeal

726 ayoyi · 5 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Na umarta a tsarkake ɗakunan, sa’an nan na mayar da kayan gidan Allah a cikin ɗakunan, tare da hadayun hatsi da kuma turare.

  2. A waɗannan kwanaki, na ga mutane a Yahuda suna matse ruwan inabi a ranar Asabbaci suna kuma kawo hatsi suna labta su a kan jakuna, tare da ruwan inabi, ’ya’yan inabi, ɓaure da kaya iri-iri. Suna kuma kawowa dukan wannan cikin Urushalima a ranar Asabbaci. Saboda haka na gargaɗe su a kan sayar da abinci a wannan rana.

  3. Mutane daga Taya waɗanda suke zama a Urushalima suna shigar da kifi da kaya iri-iri na ’yan kasuwa suna kuma sayar da su a Urushalima a ranar Asabbaci wa mutanen Yahuda.

  4. Sai na tsawata wa manyan Yahuda na ce musu, “Wanda irin mugun abu ke nan kuke yi, kuna ƙazantar da ranar Asabbaci?

  5. Kakanninku ba su yi irin waɗannan abubuwa ba, har Allahnmu ya kawo dukan masifun nan a kanmu da kuma a kan wannan birni? Yanzu kuna tsokanar fushi mai yawa a kan Isra’ila ta wurin ƙazantar da Asabbaci.”

  6. Sa’ad da inuwar yamma ya fāɗo a ƙofofin Urushalima kafin Asabbaci, na umarta a rufe ƙofofi kuma kada a buɗe sai Asabbaci ya wuce. Na kafa waɗansu mutanena a ƙofofin don kada a shigo da wani kaya a ranar Asabbaci.

  7. Sau ɗaya ko biyu, ’yan kasuwa da masu sayar da kowane irin kaya suka kwana waje da Urushalima.

  8. Amma na ja kunnensu na ce, “Me ya sa kuke kwana kusa da katanga? In kuka ƙara yin haka, zan kama ku.” Daga wannan lokaci har zuwa gaba ba su ƙara zuwa a ranar Asabbaci ba.

  9. Sai na umarci Lawiyawa su tsarkake kansu su kuma tafi su yi tsaron ƙofofi don a kiyaye ranar Asabbaci da tsarki. Ka tuna da ni saboda wannan shi ma, ya Allahna, ka nuna mini jinƙai bisa ga madawwamiyar ƙaunarka.

  10. Ban da haka, a waɗannan kwanakin na ga mutanen Yahuda waɗanda suka auri mata daga Ashdod, Ammon da Mowab.

  11. Rabin ’ya’yansu suna yaren Ashdod ko kuwa wani yare na waɗansu mutane, ba su kuwa san yadda za su yi Yahudanci ba.

  12. Na tsawata musu na kuma kira la’ana a kansu. Na bugi waɗansu mutane na kuma ja gashin kansu. Na sa suka yi rantsuwa da sunan Allah na ce, “Kada ku ba da ’ya’yanku mata aure ga ’ya’yansu maza, ba kuwa za ku auri ’ya’yansu mata wa ’ya’yanku maza ko wa kanku ba.

  13. Ba don aure-aure irin waɗannan ne Solomon sarkin Isra’ila ya yi zunubi ba? A cikin yawancin al’ummai babu sarki kamar sa. Allahnsa ya ƙaunace shi, Allah kuma ya mai da shi sarki a kan dukan Isra’ila, amma duk da haka baren mata suka rinjaye shi ga zunubi.

  14. Yanzu za mu ji cewa ku ma kuna yin duk wannan mugunta kuna zama marasa aminci ga Allahnmu ta wurin auren baren mata?”

  15. Ɗaya daga cikin ’ya’yan Yohiyada maza, ɗan Eliyashib babban firist, surukin Sanballat mutumin Horon ne. Na kuwa kore shi daga wurina.

  16. Da sai in ji daɗi duk zafin da nake sha ban hana maganar Mai Tsarkin nan cika ba.

  17. Ko yanzu haka shaidata tana sama; wanda zai tsaya mini yana sama.

  18. Ka tashi, ya Ubangiji, kada ka bar wani yă yi nasara; bari a hukunta al’ummai a gabanka.

  19. Ka buge su da rawar jiki, ya Ubangiji; bari al’ummai su sani su mutane ne kurum. Sela

  20. Sa’an nan na ce, “Ga ni, na zo, kamar yadda yake a rubuce game da ni cikin littafi.

  21. Ina sha’awar aikata nufinka, ya Allahna; dokar tana cikin zuciyata.”

  22. Na yi shelar adalcinka cikin babban taro; ba na rufe leɓunana, kamar yadda ka sani, ya Ubangiji.

  23. Ba na ɓoye adalcinka cikin zuciyata; ina maganar amincinka da cetonka. Ban ɓoye ƙaunarka da gaskiyarka a gaban taron jama’arka mai girma ba.

  24. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Maskil ne na ’Ya’yan Kora maza. Kamar yadda barewa take marmarin ruwan rafuffuka, haka raina yake marmarinka, ya Allah.

  25. Raina yana ƙishin Allah, Allah mai rai. Yaushe zan tafi in sadu da Allah ne?