Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Religious Zeal

726 ayoyi · 5 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Na dubi marasa aminci da ƙyama, gama ba sa yin biyayya da maganarka.

  2. ’Ya’yan itacen adali itacen rai ne, kuma duk mai samun rayuka mai hikima ne.

  3. Duk waɗanda ba sa bin doka yabon mugaye suke yi, amma waɗanda suke yin biyayya da doka suna gāba da mugaye ke nan.

  4. Kada ka cika yin adalci, fiye da kima, kada kuma ka cika yin hikima, don me za ka hallaka kanka!

  5. Duk abin da hannunka yake yi, ka yi shi da dukan ƙarfinka, gama a cikin kabari in da za ka, babu aiki ko shirye-shirye, ko sani, ko hikima.

  6. Ba kawai Malami ya kasance mai hikima ba, amma kuma ya koyar da mutane. Ya yi tunani ya kuma yi binciken da ya tsara karin magana masu yawa.

  7. Malami ya yi bincike don yă sami kalmomin da suka dace, kuma abin da ya rubuta daidai ne da kuma gaskiya.

  8. Mutane da yawa za su zo su ce, “Ku zo, bari mu haura zuwa dutsen Ubangiji, zuwa gidan Allah na Yaƙub. Zai koya mana hanyoyinsa, domin mu yi tafiya cikin hanyoyinsa.” Dokar za tă fito daga Sihiyona, maganar Ubangiji daga Urushalima.

  9. Ki zo, ya gidan Yaƙub, bari mu yi tafiya a hasken Ubangiji.

  10. Sa’an nan na ji muryar Ubangiji tana cewa, “Wa zan aika? Wa zai tafi mana?” Sai na ce, “Ga ni! Ka aike ni!”

  11. Mutanenku za su sāke gina kufai na da su kuma daga tsofaffin harsashai; za a ce da ku Masu Gyaran Katangar da ta Rushe, Masu Farfaɗo da Tituna da kuma Wuraren zama.

  12. Ya yafa sulke a matsayin rigar ƙirji, da hulan kwanon ceto a kansa; ya sa rigunan ɗaukar fansa ya kuma nannaɗe kansa da kishi kamar a cikin alkyabba.

  13. “Ki tashi, ki haskaka, gama haskenki ya zo, ɗaukakar Ubangiji ya taso a kanki.

  14. Saboda Sihiyona ba zan yi shiru ba, saboda Urushalima ba zan huta ba, sai adalcinta ya haskaka kamar hasken safiya, cetonta kuma ya haskaka kamar fitila mai haske.

  15. Na sa matsara a kan katangarki, ya Urushalima; ba za su taɓa yin shiru ba, dare da rana. Ku da kuke kira bisa sunan Ubangiji, kada ku ba kanku hutu,

  16. kuma kada ku ba shi hutu sai ya kafa Urushalima ya kuma mai da ita yabon duniya.

  17. Da ma kaina maɓulɓulan ruwa ne idanuna kuma maɓulɓulan hawaye! Da sai in yi kuka dare da rana saboda mutanena da aka kashe.

  18. Da ma a hamada ina da wurin da matafiye za su sauka, don in bar mutanena in tafi in bar su; gama dukansu mazinata ne, taron mutane marasa aminci.

  19. “Sun tanƙwasa harshensu kamar baka, don su harba ƙarya; ba da gaskiya ba ne suke nasara a cikin ƙasar. Sukan tashi daga wannan zunubi zuwa wancan; ba su san ni ba,” in ji Ubangiji.

  20. Amma in ba ku saurara ba, zan yi kuka a ɓoye saboda girmankanku; idanuna za su yi kuka mai zafi, suna zub da hawaye ƙwarai, domin zan kwashe garken Ubangiji zuwa zaman bauta.

  21. Ban gudu zaman mai yin maka kiwo ba; ka sani ban marmarin ranan nan ta masifa ba. Abin da ya fito daga leɓunana kuwa, a bayyane suke gare ka.

  22. Ya kamata a sāka wa alheri da mugunta? Duk da haka sun haƙa mini rami. Ka tuna cewa na tsaya a gabanka na kuma yi magana a madadinsu don ka janye fushinka daga gare su.

  23. Amma in na ce, “Ba zan ambace shi ba ba zan ƙara yin magana da sunansa ba,” sai in ji maganarsa a cikina kamar wuta, wutar da aka kulle a ƙasusuwana. Na gaji da danne ta a cikina; tabbatacce ba zan iya ba.

  24. Sai Irmiya ya ce wa dukan fadawa da kuma dukan mutane, “Ubangiji ya aiko ni in yi annabci gāba da wannan gida da wannan birni dukan abin da na faɗa.

  25. Yanzu sai ku gyara hanyoyinku da kuma ayyukanku ku yi biyayya da Ubangiji Allahnku. Sa’an nan Ubangiji zai yi juyayi ya kuma janye masifar da ya furta zai kawo a kanku.