Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Religious Zeal

726 ayoyi · 5 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Domin ba abubuwan da ido yake gani ne muke dubawa ba, sai dai marasa ganuwa. Gama abubuwan da ake gani masu saurin wucewa ne, marasa ganuwa kuwa, madawwama ne.

  2. Saboda haka, niyyarmu ita ce, mu gamshe shi, ko muna a duniya cikin jikin nan, ko ba mu nan.

  3. To, da yake mun san ko mene tsoron Ubangiji yake, muna ƙoƙari mu rinjaye mutane. Yadda muke kuwa, yana sane a sarari ga Allah, ina kuma fata yana nan a sarari a lamirinku.

  4. In hankalinmu a taɓe yake, ai, saboda Allah ne, in kuwa cikin hankalinmu muke, ai, saboda ku ne.

  5. Ƙaunar Kiristi a gare mu, ita take mallakarmu, saboda haka mun tabbata, da yake wani ya mutu saboda dukan mutane, ashe kuwa, mutuwarsu ce dukansu.

  6. Duk wannan kuwa daga Allah ne, wanda ya sulhunta mu da kansa ta wurin Kiristi, ya kuma ba mu hidimar sulhu,

  7. Saboda haka, mu jakadu ne na Kiristi, sai ka ce Allah kansa yake magana ta wurinmu. Muna roƙonku a madadin Kiristi. Ku sulhuntu da Allah.

  8. Ba ma sa abin tuntuɓe wa kowa, domin kada hidimarmu ta zama abin zargi.

  9. A maimakon haka, duk abin da muke yi, muna yin shi ne don mu nuna cewa mu masu hidimar Allah ne. Muna yin haka cikin jimrewa, da shan wahala, da shan wuya, har da shan masifu.

  10. Da shan dūka, da shan dauri, da yawan hargitsi, da yawan fama, da rashin barci, da kuma yunwa.

  11. Da cikin tsarki, da fahimta, da haƙuri, da kirki, da cikin Ruhu Mai Tsarki, da cikin ƙauna mai gaskiya,

  12. da cikin magana mai gaskiya, da kuma cikin ikon Allah. Muna riƙe da makaman adalci dama da hagu,

  13. ta wurin ɗaukaka da ƙasƙanci, da cikin ɓata suna, da kuma cikin yabo. Cikin faɗin gaskiya, an ɗauke mu masu ƙarya,

  14. mu sanannu ne, duk da haka an ɗauke mu kamar ba a san mu ba, muna mutuwa, duk da haka a raye muke, an ba mu horo, duk da haka ba a kashe mu ba,

  15. cikin baƙin ciki, duk da haka kullum cikin murna muke. Cikin matalauta, duk da haka muna azurtar da mutane da yawa. Ba mu da kome, alhali kuwa kome namu ne.

  16. Ya ku Korintiyawa, mun yi muku magana a sake, muka kuma saki zuciya da ku ƙwarai.

  17. Ku saki zuciya da mu. Ba mu yi wa kowa laifi ba, ba mu ɓata kowa ba, ba mu cuci kowa ba.

  18. Ku dubi abin da wannan baƙin ciki irin na tsoron Allah ya kawo muku mana, ya sa ku marmarin aikatawa, da nuna cewa kun yi kuskure, ya sa kuka yi fushi, kuka kuma ji tsoro, ya sa kuka sa zuciya, kuka kuma sa aniya, ya sa kuna a shirye ku ga an yi horon da ya dace. Game da wannan sha’ani kam, lalle ta kowace hanya kun nuna cewa ba ku da laifi.

  19. To, ’yan’uwa, muna so ku san abin da alherin Allah ya ba wa ikkilisiyoyin Makidoniya.

  20. Gama sun sha wuya sosai saboda tsananin wahalar da suka shiga, har yawan farin cikinsu ya kai su ga yin alheri ta bayarwa ga waɗansu, ko da yake suna cikin tsananin talauci.

  21. Gama ina shaida cewa sun bayar daidai gwargwadon iyawarsu, har ma fiye da ƙarfinsu. Su kansu,

  22. sun roƙe mu sosai don su sami damar yin bayarwa a wannan hidima ga tsarkaka.

  23. Ba su yi yadda muka za tă ba, sai ma suka fara ba da kansu ga Ubangiji, sa’an nan sai suka ba da kansu gare mu bisa ga nufin Allah.

  24. Ina gode wa Allah, wanda ya sa a zuciyar Titus, irin kula da nake da shi dominku.

  25. Ba kawai ya yarda yă je wurinku kamar yadda muka roƙe shi yă yi ba, amma ya so yă zo kamar yadda ya riga ya yi niyya.