Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Religious Zeal

726 ayoyi · 5 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. wato, don ni da ku mu ƙarfafa juna ta wurin bangaskiyarmu.

  2. Ina so ku sani ’yan’uwa cewa na yi shirin zuwa wurinku sau da dama (amma aka hana ni yin haka sai yanzu). Na so in zo domin in sami mutane wa Kiristi a cikinku, kamar yadda na yi a cikin sauran Al’ummai.

  3. Ina da hakki ga Hellenawa da waɗanda ba Hellenawa ba, ga masu hikima da kuma marasa azanci.

  4. Shi ya sa na yi himma sosai in yi muku wa’azin bishara ku ma da kuke a Roma.

  5. Gama a ciki-cikina ina farin cikin da dokar Allah;

  6. Ina faɗin gaskiya a cikin Kiristi ba ƙarya nake yi ba, lamirina ya tabbatar da wannan a cikin Ruhu Mai Tsarki.

  7. Ina da baƙin ciki mai yawa da kuma rashin kwanciyar rai marar ƙarewa a zuciyata.

  8. Gama da so na ne, sai a la’anta ni a kuma raba ni da Kiristi saboda ’yan’uwana, waɗannan na kabilata,

  9. ’Yan’uwa, abin da zuciyata take so da kuma addu’ata ga Allah saboda Isra’ilawa shi ne su sami ceto.

  10. Gama na shaida su a kan suna da kishi bin Allah, sai dai kishinsu ba a bisa sani ba.

  11. Da yake ba su san adalcin da yake fitowa daga Allah ba suka kuma nemi su kafa nasu, sai suka ƙi miƙa kai ga adalcin Allah.

  12. Ina magana da ku ne fa Al’ummai. Tun da yake ni manzo ne ga Al’ummai, ina taƙama da aikin nan nawa,

  13. da fata zan rura kabilata a ta kowace hanya su ji kishi har ma yă sa in ceci waɗansunsu.

  14. Kada ku zama marasa himma, sai dai masu himma a ruhaniyarku, kuna bauta wa Ubangiji.

  15. Na rubuta muku gabagadi a kan waɗansu batuttuwa, don in sāke tuna muku su, saboda alherin da Allah ya ba ni

  16. in zama mai hidimar Kiristi Yesu ga Al’ummai da aikin firist na yin shelar bisharar Allah, don Al’ummai su zama hadaya mai karɓuwa ga Allah, tsattsarka ta wurin Ruhu Mai Tsarki.

  17. Saboda haka ina taƙama cikin Kiristi Yesu a cikin hidimata ga Allah.

  18. Ba zan yi karambani in faɗi kome ba sai dai abin da Kiristi ya aikata ta wurina a jagorantar da Al’ummai su yi biyayya ga Allah ta wurin abin da na faɗa da kuma aikata

  19. ta wurin ikon alamu da ayyukan banmamaki, da kuma ikon Ruhun Allah. Ta haka daga Urushalima har yă zuwa kewayen Illirikum, na yi wa’azin bisharar Kiristi.

  20. Labudda, burina shi ne in yi wa’azin bishara inda ba a san Kiristi ba, don kada yă zama ina gini ne a kan tushen da wani ya kafa.

  21. Sai dai kamar yadda yake a rubuce, “Waɗanda ba a faɗa musu labarinsa ba za su gani, waɗanda kuma ba su ji ba za su fahimta.”

  22. Wannan ne ya sa sau da yawa aka hana ni zuwa wurinku.

  23. Amma yanzu da babu sauran wurin da ya rage mini in yi aiki a waɗannan yankuna, da yake kuma shekaru masu yawa ina da marmari in gan ku,

  24. ina shirin yin haka in na tafi Sifen. Ina fata in ziyarce ku yayinda nake wucewa don ku raka ni can, bayan na ji daɗin zama tare da ku na ɗan lokaci.

  25. Yanzu kam, ina hanyata zuwa Urushalima don in kai gudummawa ga tsarkaka a can.