Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Religious Zeal

726 ayoyi · 5 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Saboda haka, kada ku shari’anta kome tun lokaci bai yi ba. Ku jira sai Ubangiji ya zo. Zai bayyana abin da yake a ɓoye a cikin duhu a sarari, zai kuma tone nufin zukatan mutane. A lokacin ne fa kowa zai karɓi yabo daga wurin Allah daidai gwargwado.

  2. To, fa ’yan’uwa, ga zancen waɗannan abubuwa, na misalta su ne ga kaina, da kuma Afollos saboda ku, don ku yi koyi da mu a kan abin da ake nufi da cewa, “Kada ku zarce abin da yake a rubuce.” Ta haka, ba za ku yi taƙama da wani mutum fiye da wani ba.

  3. Wa ya ce ka fi sauran mutane? Me kuma kake da shi, wanda ba karɓa ka yi ba? In kuma karɓa ka yi, me ya sa kake taƙama kamar ba karɓa ba ne ka yi?

  4. Kun riga kun sami duk abin da kuke nema! Kun riga kun yi arziki! Kun zama sarakuna, kun kuma zama haka ɗin ba tare da mu ba! Da a ce kun riga kun zama sarakuna mana da sai mu zama sarakuna tare da ku!

  5. Gama a ganina fa, Allah ya baje mu manzanni a ƙarshen jerin gwanon, a matsayin mutanen da aka hukunta ga mutuwa a filin wasanni. Mun zama abin kallo ga dukan duniya, ga mala’iku da kuma mutane.

  6. Mun zama masu wauta saboda Kiristi, ku kuwa kuna da hikima sosai a cikin Kiristi! Ba mu da ƙarfi, amma ku kuna da ƙarfi! Ana girmama ku, mu kuwa ana ƙasƙantar da mu!

  7. Har yă zuwa wannan sa’a, yunwa da ƙishirwa muke ciki, muna sanye da tsummoki, ana wulaƙanta mu, ba mu kuma da gida.

  8. Muna aiki da gaske da hannuwanmu. In aka la’anta mu, mukan sa albarka. In aka tsananta mana, mukan jimre;

  9. in aka ɓata mana suna, mukan mayar da alheri. Har yă zuwa wannan lokaci, mu ne kamar jujin duniya, abin ƙyamar kowa.

  10. Ba don in kunyata ku ba ne na rubuta wannan, sai dai don in gargaɗe ku a kan cewa ku ’ya’yana ne, ƙaunatattu.

  11. Ko da kuna da iyayen riƙo dubu goma cikin Kiristi, ba ku da ubanni da yawa, gama a cikin Kiristi Yesu, na zama mahaifi a gare ku, ta wurin bishara.

  12. Saboda haka, ina roƙonku ku yi koyi da ni.

  13. Saboda wannan dalili ina aika muku Timoti, ɗana, wanda nake ƙauna, mai aminci kuma a cikin Ubangiji. Zai tunashe ku game da yadda za ku bi Kiristi Yesu da kuma yadda ya yi daidai da yadda nake koyarwa a ko’ina, a kowace ikkilisiya.

  14. Waɗansunku suna tsammani ba zan zo wurinku ba har suna ɗagankai.

  15. Amma in Ubangiji ya yarda zan zo wurinku ba da daɗewa ba. Sa’an nan zan bincike ko masu wannan yawan ɗagan kan nan suna da wani iko.

  16. Gama mulkin Allah ba cika baki ba ne, sai dai ga iko.

  17. Wanne kuka fi so in na zo? Kuna so in tsananta muku ko in zama mai hankali da kuma sauƙinkai?

  18. Saboda haka, sai mu kiyaye Bikin ba da burodi mai tsohon yisti ba, ba kuma da yisti na ƙeta da mugunta ba, sai dai da burodi marar yisti na sahihanci da na gaskiya.

  19. ’Yan’uwa, abin da nake nufi shi ne, lokaci ya rage kaɗan. Daga yanzu, waɗanda suke da mata ya kamata su yi rayuwa kamar ba su da su;

  20. waɗanda suke kuka kuma kamar ba kuka suke yi ba, waɗanda suke farin ciki kuwa kamar ba farin ciki suke yi ba. Waɗanda suka sayi abu su yi kamar ba nasu ba ne;

  21. masu amfani da kayan duniya kuwa, kada su duƙufa a cikinsu. Gama duniyan nan a yadda take mai shuɗewa ce.

  22. Zan so ku ’yantu daga damuwa. Mutum marar aure ya damu ne da al’amuran Ubangiji, yadda zai gamshi Ubangiji.

  23. Amma mutumin da yake da aure yakan damu ne da al’amuran wannan duniya, yadda zai gamshi matarsa

  24. hankalinsa a rabe yake. Mace marar aure ko kuwa budurwa ta damu ne da al’amuran Ubangiji. Nufinta shi ne ta ba da kanta ga Ubangiji cikin jiki da ruhu. Amma mace da take da aure ta damu ne da al’amuran wannan duniya, yadda za tă gamshi mijinta.

  25. In waɗansu suna samun wannan taimako daga gare ku, ashe, mu ba mu fi cancanta mu samu ba? Amma ba mu yi amfani da wannan ’yancin ba. A maimakon haka, mun jure da kome, domin kada mu hana bisharar Kiristi yaɗuwa.