Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Passover

161 ayoyi · 14 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ɗan Mutum zai tafi kamar yadda yake a rubuce game da shi, amma kaiton mutumin da ya bashe Ɗan Mutum! Zai fi masa, da ba a haife shi ba.”

  2. Yayinda suke cin abinci, sai Yesu ya ɗauki burodi, ya yi godiya, ya kakkarya, ya ba wa almajiransa, yana cewa, “Ku karɓa, wannan jikina ne.”

  3. Sai kuma ya ɗauki kwaf ruwan inabi, ya yi godiya, ya kuma miƙa musu, dukansu suka sha daga ciki.

  4. Sai ya ce musu, “Wannan jinina ne na alkawari, wanda aka zubar da shi saboda mutane da yawa.

  5. Gaskiya nake gaya muku, ‘Ba zan ƙara sha daga ’ya’yan inabi ba, sai ranan nan, da zan sha shi sabo a mulkin Allah.’ ”

  6. Yanzu fa, al’ada ce a lokacin Bikin, a saki ɗan kurkuku guda wanda mutane suka roƙa.

  7. Kowace shekara, iyayen Yesu sukan je Urushalima don Bikin Ƙetarewa.

  8. Da Yesu ya cika shekaru goma sha biyu, sai suka tafi Bikin bisa ga al’ada.

  9. Bayan Bikin, da iyayen suka kama hanya don su koma gida, sai Yesu, yaron nan, ya tsaya a Urushalima, ba da saninsu ba.

  10. Su kuwa sun ɗauka yana tare da su, saboda haka, suka yi ta tafiya har na yini guda. Sa’an nan suka fara nemansa cikin ’yan’uwansu da abokansu.

  11. Da ba su gan shi ba, sai suka koma Urushalima nemansa.

  12. Bayan kwana uku, sai suka same shi a filin haikali zaune a tsakiyar malamai, yana sauraronsu yana kuma yi musu tambayoyi.

  13. Dukan waɗanda suka ji shi, suka yi mamakin fahimtarsa, da amsoshinsa.

  14. Da iyayensa suka gan shi sai suka yi mamaki. Mahaifiyarsa ta ce masa, “Ɗana, don me ka yi mana haka? Ni da mahaifinka duk mun damu muna nemanka.”

  15. Sai ya ce, “Don me kuke nemana? Ba ku san cewa, dole in kasance a gidan Ubana ba?”

  16. Amma ba su fahimci abin da yake faɗin musu ba.

  17. Sai ranar Bikin Burodi Marar Yisti ta kewayo, wato, ranar hadayar ɗan ragon kafara na Bikin Ƙetarewa.

  18. Sai Yesu ya aiki Bitrus da Yohanna, ya ce musu, “Ku je ku yi shirye-shiryen Bikin Ƙetarewar da za mu ci.”

  19. Suka tambaye shi suka ce, “Ina kake so mu je mu yi shirin?”

  20. Ya amsa ya ce, “Sa’ad da kuka shiga cikin gari, za ku sadu da wani mutum yana ɗauke da tulun ruwa. Ku bi shi zuwa gidan da zai shiga.

  21. Ku ce wa maigidan, Malam ya aike mu mu ce maka, ‘Ina ɗakin baƙi, inda ni da almajiraina za mu ci abincin Bikin Ƙetarewa?’

  22. Zai nuna muku wani babban ɗakin sama a shirye. Nan za ku yi shirin.”

  23. Sai suka tafi, suka kuma iske kome kamar yadda Yesu ya faɗa musu. Sai suka shirya Bikin Ƙetarewa.

  24. Da lokaci ya yi, sai Yesu ya zauna tare da manzanninsa don cin abinci.

  25. Sai ya ce musu, “Na yi marmari ƙwarai don in ci wannan Bikin Ƙetarewa tare da ku, kafin in sha wahala.