Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Miracles

338 ayoyi · 37 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Makafi suna gani, guragu suna tafiya, ana warkar da waɗanda suke da kuturta, kurame suna ji, ana tā da matattu, ana kuma yi wa matalauta wa’azin labari mai daɗi.

  2. Mai albarka ne mutumin da bai yi tuntuɓe ba saboda ni.”

  3. Sai Yesu ya fara yin tir da biranen da aka yi yawancin ayyukansa na banmamaki, don ba su tuba ba.

  4. “Kaitonki, Korazin! Kaitonki, Betsaida! Da a ce ayyukan banmamakin da aka yi a cikinki ne aka yi a Taya da Sidon, da tuni sun tuba sanye da rigar makoki da toka.

  5. Amma ina gaya muku, za a fi jin tausayin Taya da Sidon a ranar shari’a, fiye da ku.

  6. Ke kuma Kafarnahum, za a ɗaga ki sama ne? A’a, za ki gangara zuwa zurfafa ne. Da a ce ayyukan banmamakin da aka yi a cikinki ne a aka yi a Sodom, da tana nan har yă zuwa yau.

  7. Amma ina gaya miki, za a fi jin tausayin Sodom fiye da ke a ranar shari’a.”

  8. Amma in ina fitar da aljanu ta wurin Ruhun Allah ne, to, fa, mulkin Allah ya zo muku ke nan.

  9. Bai kuwa yi abubuwan banmamaki da yawa a can ba saboda rashin bangaskiyarsu.

  10. Da mutanen wurin suka gane da Yesu, sai suka kai labari a ko’ina a ƙauyukan da suke kewaye. Mutane suka kawo masa dukan marasa lafiyarsu

  11. suka kuwa roƙe shi yă bar marasa lafiya su taɓa ko da gefen rigarsa kawai, duk waɗanda suka taɓa shi kuwa suka warke.

  12. Yesu ya amsa ya ce, “Mai albarka ne kai Siman ɗan Yunana, gama ba mutum ne ya bayyana maka wannan ba, sai dai Ubana da yake cikin sama.

  13. Ya amsa ya ce, “Saboda kuna da ƙarancin bangaskiya sosai. Gaskiya nake gaya muku, in kuna da bangaskiyar da take ƙanƙanuwa kamar ƙwayar mustad, za ku iya ce wa wannan dutse, ‘Matsa daga nan zuwa can,’ zai kuwa matsa. Babu abin da zai gagare ku.”

  14. Sai ya bar su, ya fita daga birnin ya tafi Betani, inda ya kwana.

  15. Kashegari da sassafe, yayinda yake kan hanyarsa ta komawa cikin birni, sai ya ji yunwa.

  16. Ganin itacen ɓaure kusa da hanya, sai ya je wajensa amma bai sami kome a kansa ba sai ganye. Sai ya ce masa, “Kada ka ƙara yin ’ya’ya!” Nan da nan itacen ya yanƙwane.

  17. Sa’ad da almajiran suka ga haka, sai suka yi mamaki suna tambaya, “Yaya itacen ɓauren ya yanƙwane nan da nan haka?”

  18. Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, in kuna da bangaskiya, ba kuwa da wata shakka ba, ba kawai za ku iya yin abin da aka yi wa itacen ɓauren nan ba, amma za ku ma iya ce wa dutsen nan, ‘Je ka, ka jefa kanka cikin teku,’ sai yă faru.

  19. In kun gaskata, za ku karɓi duk abin da kuka roƙa a cikin addu’a.”

  20. “Ya ceci waɗansu, amma ya kāsa ceton kansa! In shi ne Sarkin Isra’ila! To, yă sauko daga kan gicciyen nan, mu kuwa mu gaskata shi.

  21. Wanne ya fi sauƙi, a ce wa shanyayyen, ‘An gafarta zunubanka,’ ko a ce, ‘Tashi, ɗauki tabarmarka ka yi tafiya’?

  22. Amma don ku san cewa, Ɗan Mutum yana da iko a duniya yă gafarta zunubai.” Sai ya ce wa shanyayyen,

  23. “Ina ce maka, tashi, ɗauki tabarmarka, ka tafi gida.”

  24. Sai ya tashi, ya ɗauki tabarmarsa, ya yi tafiyarsa a gabansu duka. Wannan ya ba wa kowa mamaki, suka kuma ɗaukaka Allah suna cewa, “Ba mu taɓa ganin abu haka ba!”

  25. gama ba su fahimci al’amarin burodin nan ba, don zuciyarsu ta taurare.