Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Miracles: Curses a fig tree

14 ayoyi · 37 fannoni

Ayoyi game da Curses a fig tree

  1. Sai ya bar su, ya fita daga birnin ya tafi Betani, inda ya kwana.

  2. Kashegari da sassafe, yayinda yake kan hanyarsa ta komawa cikin birni, sai ya ji yunwa.

  3. Ganin itacen ɓaure kusa da hanya, sai ya je wajensa amma bai sami kome a kansa ba sai ganye. Sai ya ce masa, “Kada ka ƙara yin ’ya’ya!” Nan da nan itacen ya yanƙwane.

  4. Sa’ad da almajiran suka ga haka, sai suka yi mamaki suna tambaya, “Yaya itacen ɓauren ya yanƙwane nan da nan haka?”

  5. Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, in kuna da bangaskiya, ba kuwa da wata shakka ba, ba kawai za ku iya yin abin da aka yi wa itacen ɓauren nan ba, amma za ku ma iya ce wa dutsen nan, ‘Je ka, ka jefa kanka cikin teku,’ sai yă faru.

  6. In kun gaskata, za ku karɓi duk abin da kuka roƙa a cikin addu’a.”

  7. Kashegari, da suke barin Betani, Yesu kuwa ya ji yunwa.

  8. Da ya hangi wani itacen ɓaure mai ganye, sai ya je domin yă ga ko yana da ’ya’ya. Amma da ya kai can, bai tarar da kome ba sai ganye, domin ba lokacin ’ya’yan ɓaure ba ne.

  9. Sai ya ce wa itacen, “Kada kowa yă ƙara cin ’ya’yanka.” Almajiransa kuwa suka ji ya faɗi haka.

  10. Da safe, da suke wucewa, sai suka ga itacen ɓauren nan ya yanƙwane tun daga saiwarsa.

  11. Bitrus ya tuna, sai ya ce wa Yesu, “Rabbi, duba! Itacen ɓauren nan da ka la’anta, ya yanƙwane!”

  12. Yesu ya amsa ya ce, “Ku gaskata da Allah.

  13. Gaskiya nake gaya muku, in wani ya ce wa dutsen nan, ‘Je ka, ka fāɗa cikin teku,’ bai kuwa yi shakka a zuciyarsa ba, amma ya gaskata cewa, abin da ya faɗa zai faru, haka kuwa za a yi masa.

  14. Saboda haka, ina faɗa muku, duk abin da kuka roƙa cikin addu’a, ku gaskata kun riga kun karɓa, zai kuwa zama naku.