Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Miracles: Design of miracles

196 ayoyi · 37 fannoni

Ayoyi game da Design of miracles

Tace bisa littafi
  1. Amma na san cewa sarkin Masar ba zai yarda ku tafi ba, sai hannu mai ƙarfi ya tilasta shi.

  2. Saboda haka zan miƙa hannuna in bugi Masarawa da duk al’ajaban da zan aikata a cikinsu. Bayan haka zai bar ku, ku tafi.

  3. Sai Ubangiji ya ce, “Mene ne wannan a hannunka?” Musa ya amsa ya ce, “Sanda.”

  4. Sai Ubangiji ya ce, “Jefa shi ƙasa.” Musa ya jefa shi ƙasa, sai sandan ya zama maciji, Musa kuwa ya gudu daga gare shi.

  5. Sai Ubangiji ya ce masa, “Sa hannunka ka ɗauke shi ta wutsiya.” Sai Musa ya miƙa hannu, ya kama macijin, macijin kuwa ya dawo sanda a hannunsa.

  6. Ubangiji ya ce, “Wannan zai sa su ba da gaskiya cewa Ubangiji, Allah na kakanninsu, Allah na Ibrahim, Allah na Ishaku, da kuma Allah da Yaƙub, ya bayyana gare ka.”

  7. Sa’an nan Ubangiji ya ce, “Sa hannunka cikin rigarka.” Sai Musa ya sa hannunsa cikin rigarsa, sa’ad da ya fitar da shi, sai hannun ya a kuturce fari fat, kamar ƙanƙara.

  8. Sai Ubangiji ya ce, “Yanzu, mayar da hannunka a rigarka.” Sai Musa ya sa hannunsa cikin rigarsa, da ya fitar da shi, sai hannun ya koma kamar sauran jikinsa.

  9. Sa’an nan Ubangiji ya ce, “In ba su gaskata ba, ko kuma ba su kula da mu’ujiza ta fari ba, wataƙila su gaskata da ta biyun.

  10. Amma in ba su gaskata mu’ujizan nan biyu ba, ko kuwa ba su saurare ka ba, sai ka ɗibo ruwa daga Nilu, ka zuba a busasshiyar ƙasa. Ruwan da ka ɗebo daga kogin zai zama jini a ƙasar.”

  11. Masarawa kuwa za su san cewa ni ne Ubangiji sa’ad da na miƙa hannuna a kan Masar, na kuma fitar da Isra’ilawa daga gare ta.”

  12. Ga abin da Ubangiji ya ce, da wannan za ka san cewa ni ne Ubangiji. Da sandan da yake hannuna zan bugi ruwan Nilu, zai kuma zama jini.

  13. Fir’auna ya kira Musa da Haruna ya ce, “Yi addu’a ga Ubangiji yă ɗauke kwaɗi daga gare ni da mutanena, zan kuwa bar mutanenku su tafi su yi hadaya ga Ubangiji.”

  14. Musa ya ce wa Fir’auna, “Na ba ka dama ka ba da lokacin da zan yi addu’a dominka da kuma bayinka da mutanenka, gidajenku kuwa za su rabu da kwaɗi, amma ban da waɗanda suke cikin Nilu.”

  15. Fir’auna ya ce, “Gobe.” Musa ya amsa, “Za a yi kamar yadda ka faɗa, domin ka sani babu wani kamar Ubangiji, Allahnmu.

  16. “ ‘Amma zan keɓe yankin Goshen, inda mutanena suke don kada ƙudaje su taɓa wurin, domin ka sani cewa Ni, Ubangiji, ina cikin wannan ƙasa.

  17. ko kuwa a wannan lokaci zan aika da cikakkiyar annoba mai ƙarfi a kanka da a kan fadawanka da mutanenka, domin ka san cewa ba kama da ni a dukan duniya.

  18. Gama da ni kaina na miƙa hannuna na buge ka da jama’arka da annoba, ai, da an hallaka ku a duniya ƙaƙaf.

  19. Amma na bar ka ka rayu domin in nuna maka ikona, domin kuma sunana yă zama abin darajantawa a dukan duniya.

  20. Musa ya amsa, “To, da kyau, da zarar na fita daga birnin, zan yi addu’a ga Ubangiji, tsawar za tă tsaya, ƙanƙarar kuma za tă daina, don ku sani cewa duniya ta Ubangiji ce.

  21. Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Je wurin Fir’auna, gama na riga na taurare zuciyarsa da kuma zukatan fadawansa domin in aikata waɗannan mu’ujizai nawa a tsakiyarsu,

  22. don kuma ku gaya wa ’ya’yanku da jikokinku yadda na tsananta wa Masarawa, da kuma yadda na aikata mu’ujizai a cikinsu, don ku sani ni ne Ubangiji.”

  23. Fir’auna ya kira Musa da Haruna da gaggawa ya ce, “Na yi wa Ubangiji Allahnku zunubi, na kuma yi muku.

  24. Yanzu ku gafarta mini zunubina a wannan karo, ku kuma yi addu’a ga Ubangiji Allahnku yă ɗauke wannan muguwar annoba daga gare ni.”

  25. To, fa, sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Zan ƙara kawo annoba guda a kan Fir’auna da kan Masar. Bayan haka, zai bar ku, ku fita daga nan. Sa’ad da ya yi haka kuwa, zai kore ku gaba ɗaya.