Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Miracles: Should produce obedience

6 ayoyi · 37 fannoni

Ayoyi game da Should produce obedience

  1. To, sai ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku, kullum ku kuma kiyaye abubuwan da yake bukata, ku kiyaye ƙa’idodinsa, dokokinsa da kuma umarnansu.

  2. Ku tuna a yau, cewa ’ya’yanku ba su ne suka gani suka kuma ɗanɗana horon Ubangiji Allahnku ba; ba su suka gani girmansa, hannunsa mai ƙarfi, hannunsa mai iko;

  3. alamun da ya aikata da abubuwan da ya yi a cikin Masar, ga Fir’auna sarkin Masar da kuma ga dukan ƙasarsa ba;

  4. Sai Musa ya tara dukan Isra’ila, ya ce musu, Idanunku sun ga dukan abin da Ubangiji ya yi a Masar ga Fir’auna, ga kuma dukan shugabanninsa da kuma ga dukan ƙasarsa.

  5. Da idanunku kun ga waɗannan gwaje-gwaje, waɗannan alamu masu banmamaki, da al’ajabai masu girma.

  6. Saboda haka sai ku kiyaye, ku bi sharuɗan wannan alkawari, don ku yi nasara a cikin kome da kuke yi.