Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Levites

186 ayoyi · 17 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Na sa su je wurin Iddo wanda yake shugaba a Kasifiya. Aka gaya musu abin da za su gaya wa Iddo da ’yan’uwansa masu aiki a haikali a Kasifiya don su aiko mana waɗanda za su yi mana hidima a haikalin Allahnmu.

  2. Da yake Allah yana tare da mu, sai suka aiko mana da Sherebiya, wanda ya iya aiki, shi daga zuriyar Mali ɗan Lawi ne, ɗan Isra’ila. Sai ya zo tare da ’ya’yansa da kuma ’yan’uwansa. Dukansu dai mutum 18 ne.

  3. Suka kuma aika da Hashabiya tare da Yeshahiya daga zuriyar Merari, da ’yan’uwansu da kuma ’ya’yansu, su kuma mutum 20 ne.

  4. Sun kuma kawo masu aiki a haikali mutum 220, ƙungiyar da Dawuda da abokan aikinsa suka keɓe don su taimaki Lawiyawa aiki. Duk aka rubuta waɗannan da sunayensu.

  5. Bayan an yi waɗannan abubuwa duka, sai shugabanni suka zo wurina suka ce, “Mutanen Isra’ila, har da firistoci da Lawiyawa ba su keɓe kansu daga maƙwabtansu ba, ba su kuma keɓe kansu daga irin rayuwar ƙazantar mutanen ƙasar ba, wato, rayuwar irinta Kan’aniyawa, da Hittiyawa, da Ferizziyawa, da Yebusiyawa, da Ammonawa, da Mowabawa, da Masarawa da Amoriyawa.

  6. Sun auro wa kansu da ’ya’yansu ’yan mata mutanen nan, ta haka aka kwaɓa zuriyar da aka tsarkake da ta mutanen nan da suke tare da su. Shugabanni da manyan ma’aikata su ne a gaba-gaba a aikata wannan abin kunya.”

  7. Cikin Lawiyawa, akwai Yozabad, Shimeyi, Kelaya (wato, Kelita), Fetahahiya, Yahuda, Eliyezer.

  8. Daga mawaƙa, akwai Eliyashib. Daga masu tsaron ƙofofin haikali, akwai Shallum, Telem da Uri.

  9. Ga zuriyar Lawiyawa. Zuriyar Yeshuwa da Kadmiyel (ta wurin Hodeba) 74.

  10. Mawaƙa. Zuriyar Asaf mutum 148.

  11. Ga zuriyar Matsaran Ƙofofi. Zuriyar Shallum, Ater, Talmon, Akkub, Hatita da Shobai 138.

  12. Ma’aikatan haikali. Zuriyar Ziha, Hasufa, Tabbawot,

  13. da ta Keros, da ta Siya, da ta Fadon,

  14. da ta Lebana, da ta Hagaba, da ta Shalmai,

  15. da ta Hanan, da ta Giddel, da ta Gahar,

  16. da ta Reyahiya, da ta Rezin, da ta Nekoda,

  17. da ta Gazzam, da ta Uzza, da ta Faseya,

  18. da ta Besai, da ta Meyunawa, da ta Nefussiyawa,

  19. da ta Bakbuk, da ta Hakufa, da ta Harhur,

  20. da ta Bazlit, da ta Mehida, da ta Harsha,

  21. da ta Barkos, da ta Sisera, da ta Tema,

  22. da ta Neziya, da kuma ta Hatifa.

  23. Ga zuriyar bayin Solomon. Zuriyar Sotai, da ta Soferet, da ta Ferida,

  24. da ta Ya’ala, da ta Darkon, da ta Giddel,

  25. Shefatiya, Hattil, Fokeret-Hazzebayim, da Amon.