Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Levites

186 ayoyi · 17 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Dukan ’ya’yan Lawiyawa maza daga wata ɗaya zuwa gaba, jimillarsu ta kai 23,000. Ba a ƙidaya su tare da sauran Isra’ilawa ba, domin ba a ba su gādo tare da su ba.

  2. Kashin da aka ba wa Isra’ilawa, wanda Musa ya ware daga cikin na waɗanda suka tafi yaƙi,

  3. kashin da aka ba wa jama’a kuwa tumaki 337,500 ne,

  4. shanu 36,000,

  5. jakuna 30,500

  6. da mutane 16,000.

  7. Daga rabin kashi na Isra’ilawa, Musa ya ɗauki ɗaya daga cikin hamsin na mutane da na dabbobi, yadda Ubangiji ya umarce shi, ya ba wa Lawiyawan da suke lura da tabanakul na Ubangiji.

  8. Ya yi zancen mahaifinsa da mahaifiyarsa ya ce, ‘Ban kula da su ba.’ Bai gane da ’yan’uwansa ba, ko yă yarda da ’ya’yansa, amma ya kiyaye maganarka ya tsare alkawarinka.

  9. Ya koyar da farillanka ga Yaƙub, dokarka kuma ga Isra’ila. Ya miƙa turare a gabanka da kuma hadaya ta ƙonawa ɗungum a kan bagadenka.

  10. ku kuma da kuke a sauran ƙungiyoyi biyu da kun saba hutu a Asabbaci, duk za ku yi gadin haikali don sarki.

  11. Ku tsaya kewaye da sarki, kowane mutum da makaminsa a hannu. Duk wanda ya kusace ku, ku kashe shi. Ku manne wa sarki duk inda ya tafi.”

  12. Komandodin sojoji suka yi yadda Yehohiyada firist ya umarta. Kowa ya ɗauki mutanensa, waɗanda za su kama aiki Asabbaci da waɗanda za su kama hutun Asabbaci, suka zo wurin Yehohiyada firist.

  13. Sai ya ba komandodin māsu da garkuwoyi da dā suke na Dawuda, waɗanda suke a cikin haikalin Ubangiji.

  14. Matsaran kuma kowa da makaminsa a hannu, suka tsaya kewaye da sarki, kusa da bagade da kuma haikali, daga gefen kudu zuwa gefen arewa na haikalin.

  15. Aka ƙidaya Lawiyawan da suke ’yan shekaru talatin da haihuwa ko fiye, suka kai wajen mutum dubu talatin da takwas.

  16. Dawuda ya ce, “Cikin waɗannan, dubu ashirin da huɗu za su lura da aikin haikalin Ubangiji, dubu shida su zama manyan na ma’aikata da alƙalai.

  17. Dubu huɗu su zama matsaran ƙofofi, dubu huɗu kuma su yabi Ubangiji da kayayyakin bushe-bushe da na kaɗe-kaɗe waɗanda na tanada saboda wannan manufa.”

  18. Firistoci da Lawiyawa daga dukan yankuna ko’ina a Isra’ila suka haɗa kai da shi.

  19. Lawiyawa suka ma bar makiyayansu da mallakarsu, suka zo Yahuda da Urushalima domin Yerobowam da ’ya’yansa maza sun ƙi su a matsayin firistocin Ubangiji.

  20. Yerobowam ya naɗa firistocinsa domin masujadan kan tudu da kuma domin gumakan nan na akuya da maraƙin da ya yi.

  21. Waɗanda suke daga kowane kabilar Isra’ila waɗanda suka sa zuciya a kan neman Ubangiji, Allah na Isra’ila, suka bi Lawiyawa zuwa Urushalima don su miƙa hadayu ga Ubangiji Allah na kakanninsu.

  22. Suka ƙarfafa mulkin Yahuda suka kuma goyi bayan Rehobowam ɗan Solomon shekaru uku, suna tafiya a hanyoyin Dawuda da Solomon a wannan lokaci.

  23. Ba ku ne kuka kori firistocin Ubangiji, ’ya’yan Haruna maza, da Lawiyawa kuka kuma zaɓi firistocinku kamar yadda sauran al’ummai suke yi ba? Duk wanda ya zo ya miƙa ɗan bijimi da raguna bakwai don yă tsarkake kansa, ya zama firist na gumaka ke nan, ba na Allah ba.

  24. “Gare mu kuwa, Ubangiji shi ne Allah, kuma ba mu yashe shi ba. Firistocin da suke bauta wa Ubangiji ’ya’yan Haruna maza ne, Lawiyawa ne kuwa suke taimakonsu.

  25. Kowace safiya da kowace yamma sukan miƙa hadayun ƙonawa da turare mai ƙanshi ga Ubangiji. Sukan shirya burodi a tsarkaken tebur mai tsabta, sukan kuma ƙuna fitilu a alkukai kowace yamma. Muna kiyaye ƙa’idodin Ubangiji Allahnmu. Amma ku kun yashe shi.