Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Levites: Substituted in the place of the firstborn

8 ayoyi · 17 fannoni

Ayoyi game da Substituted in the place of the firstborn

  1. Ka ɗauko mini Lawiyawa a maimakon dukan ’ya’yan fari na Isra’ilawa, haka ma na dabbobi na Lawiyawa, a maimakon ’ya’yan fari na dabbobin Isra’ilawa. Ni ne Ubangiji.”

  2. Haka Musa ya ƙidaya ’ya’yan fari na Isra’ilawa, yadda Ubangiji ya umarce shi.

  3. Jimillar ’ya’yan fari maza daga wata ɗaya da kuma fiye, da aka rubuta bisa ga sunayensu, 22,273 ne.

  4. Sai Ubangiji ya kuma yi magana da Musa ya ce,

  5. “Ka ɗauki Lawiyawa a maimakon dukan ’ya’yan fari na Isra’ila, dabbobin Lawiyawa kuma a maimakon dabbobinsu. Lawiyawa za su zama nawa. Ni ne Ubangiji.

  6. Gama dukansu an ba ni su daga cikin Isra’ilawa a maimakon dukan waɗanda suka fara buɗe mahaifa, wato, dukan ’ya’yan farin Isra’ilawa. Na karɓi Lawiyawa su zama nawa.

  7. Kowane ɗan farin haihuwa, ko mutum, ko dabba a Isra’ila, nawa ne. Sa’ad da na kashe ’ya’yan fari a Masar, na keɓe ’ya’yan fari na Isra’ilawa wa kaina.

  8. Na kuma ɗauki Lawiyawa a maimakon dukan ’ya’yan fari maza a Isra’ila.