Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Levites: Place of, in camp and march

17 ayoyi · 17 fannoni

Ayoyi game da Place of, in camp and march

  1. A maimakon haka sai ka naɗa Lawiyawa su lura da tabanakul Shaida, wato, kan dukan kayayyaki da kuma kome da yake na wuri mai tsarki. Za su ɗauko tabanakul da dukan kayayyakinsa; za su lura da shi, su kasance kewaye da shi.

  2. Duk sa’ad da za a gusar da tabanakul, Lawiyawa ne za su saukar da shi; kuma duk sa’ad da za a kafa shi, Lawiyawa ne za su yi haka. Duk wani dabam da ya je kusa da shi za a kashe shi.

  3. Sauran Isra’ilawa za su zauna ƙungiya-ƙungiya, kowane mutum a ƙungiyarsa daidai bisa ga ƙa’idarsa.

  4. Amma Lawiyawa za su kafa sansaninsu kewaye da tabanakul na Shaida. Don kada fushi yă fāɗo a kan al’ummar Isra’ilawa. Hakkin Lawiyawa ne su kula da tabanakul na Shaida.”

  5. Kabilar Gershonawa za su yi sansani ta fuskar yamma, a bayan tabanakul.

  6. Eliyasaf ɗan Layel shi ne shugaban iyalan Gershonawa.

  7. A Tentin Sujada, Gershonawa su ne za su lura da mazauni da tabanakul da kuma tentin, abubuwan rufensa, labule a ƙofar Tentin Sujada,

  8. da labulen filin da yake kewaye da tabanakul da kuma bagade, da igiyoyi, da kuma kowane abin da ya danganci aikinsu.

  9. Kabilar Kohat su ne, Amramawa da Izharawa da Hebronawa da Uzziyelawa; waɗannan su ne kabilar Kohatawa.

  10. Jimillar dukan jarirai maza daga wata ɗaya ko fiye, 8,600 ne. Kohatawa ne suke lura da wuri mai tsarki.

  11. Kohatawa za su yi sansani a kudu da tabanakul.

  12. Shugaban kabilar Kohatawa shi ne Elizafan ɗan Uzziyel.

  13. Su ne da hakkin kula da akwatin alkawari, tebur, wurin ajiye fitila, bagade, kayayyakin wuri mai tsarki da ake amfani da su a sujada, labule, da kuma kome da ya danganci aikinsu.

  14. Babban shugaban Lawiyawa shi ne Eleyazar ɗan Haruna, firist. An naɗa shi a kan waɗanda suke kula da wuri mai tsarki.

  15. Kabilar Merari su ne Maliyawa da Mushiyawa; waɗannan su ne kabilar Merari.

  16. Jimillar dukan jarirai maza daga wata ɗaya ko fiye, 6,200 ne.

  17. Shugaban iyalan Merari shi ne Zuriyel ɗan Abihayil. Za su yi sansani arewa da tabanakul.