Skip to content

Merari

38 ayoyi · 7 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci Merari

Tace bisa littafi
  1. ’Ya’yan Lawi maza su ne, Gershon, Kohat da Merari.

  2. Waɗannan su ne sunayen ’ya’yan Lawi maza bisa ga abin da aka rubuta, Gershon, Kohat da Merari. Lawi ya yi shekara 137.

  3. ’Ya’yan Merari maza, su ne, Mali da Mushi. Waɗannan su ne dangin Lawi bisa ga abin da aka rubuta.

  4. Ga sunayen ’ya’yan Lawi, Gershon, Kohat da Merari.

  5. Dangin Merari su ne. Mali da Mushi. Ga kabilan Lawiyawa bisa ga iyalansu.

  6. Kabilar Merari su ne Maliyawa da Mushiyawa; waɗannan su ne kabilar Merari.

  7. Shugaban iyalan Merari shi ne Zuriyel ɗan Abihayil. Za su yi sansani arewa da tabanakul.

  8. Kabilar Merari ne aka sa su lura da katakan tabanakul, sandunanta, dogayen sandunanta, tarukanta, dukan kayan aiki da kowane abin da ya danganci aikinsu,

  9. “Ka ƙidaya kabilar Merari bisa ga kabilarsu da iyalansu.

  10. Wannan ce hidimar da mutanen Merari za su yi a aikin Tentin Sujada, a ƙarƙashin jagorancin Itamar ɗan Haruna, firist.”

  11. Aka ƙidaya mazan Merari ta kabilarsu da kuma iyalansu.

  12. Jimillar waɗanda suke na kabilar Merari ke nan. Musa da Haruna suka ƙidaya su bisa ga umarnin Ubangiji.

  13. ya kuma ya ba wa kabilar Merari kekunan yaƙi huɗu da shanu takwas bisa ga aikinsu. Aka ba da su duka a ƙarƙashin ikon Itamar ɗan Haruna, firist.

  14. Sa’an nan aka saukar da tabanakul ƙasa, Gershonawa da mutanen Merari da suke ɗauke da shi suka kama hanya.

  15. Waɗannan su ne Lawiyawa da a ƙidaya bisa ga kabilansu, daga Gershom, kabilar Gershonawa; daga Kohat, kabilar Kohatawa; daga Merari, kabilar Merari.

  16. Aka ba wa zuriyar Merari bisa ga iyalansu, garuruwa goma sha biyu daga kabilan Ruben, Gad da Zebulun.

  17. Aka ba wa iyalan Merari (sauran Lawiyawa) garuruwa, daga kabilar Zebulun, wato, Yokneyam, Karta,

  18. Duka-duka garuruwan da aka ba iyalan mutanen Merari, waɗanda su ne sauran Lawiyawa, garuruwa goma sha biyu ne.

  19. ’Ya’yan Lawi maza su ne, Gershon, Kohat da Merari.

  20. ’Ya’yan Lawi maza su ne, Gershom, Kohat da Merari.

  21. ’Ya’yan Merari maza su ne, Mali da Mushi. Waɗannan suke gidajen Lawiyawan da aka jera bisa ga kakanninsu.

  22. Zuriyar Merari su ne, Mali, Libni, Shimeyi, Uzza,

  23. da kuma daga ’yan’uwansu, mutanen Merari, a hannun hagunsa. Etan ɗan Kishi, ɗan Abdi, ɗan Malluk,

  24. ɗan Mali, ɗan Mushi, ɗan Merari, ɗan Lawi.

  25. Aka ba zuriyar Merari, gida-gida, rabon garuruwa goma sha biyu daga kabilan Ruben, Gad da Zebulun.