Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Gershon

21 ayoyi · 1 fanni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Waɗannan su ne sunayen ’ya’yan Lawi maza bisa ga abin da aka rubuta, Gershon, Kohat da Merari. Lawi ya yi shekara 137.

  2. ’Ya’yan Gershon maza, bisa ga dangi su ne, Libni da Shimeyi.

  3. Ga sunayen ’ya’yan Lawi, Gershon, Kohat da Merari.

  4. Ga sunayen mutanen Gershon, Libni, da Shimeyi

  5. Sunayen mutanen Kohat kuwa su ne, Amram, Izhar, Hebron da Uzziyel.

  6. Dangin Merari su ne. Mali da Mushi. Ga kabilan Lawiyawa bisa ga iyalansu.

  7. A wajen Gershonawa, kabilarsa su ne Libniyawa, da Shimeyiyawa; waɗannan su ne mutanen Gershom.

  8. Jimillar dukan jarirai maza daga wata ɗaya zuwa gaba da haihuwa su kai 7,500.

  9. Kabilar Gershonawa za su yi sansani ta fuskar yamma, a bayan tabanakul.

  10. Eliyasaf ɗan Layel shi ne shugaban iyalan Gershonawa.

  11. A Tentin Sujada, Gershonawa su ne za su lura da mazauni da tabanakul da kuma tentin, abubuwan rufensa, labule a ƙofar Tentin Sujada,

  12. da labulen filin da yake kewaye da tabanakul da kuma bagade, da igiyoyi, da kuma kowane abin da ya danganci aikinsu.

  13. “Ka ƙidaya mutanen Gershon bisa ga iyalansu da kabilarsu.

  14. Ka ƙidaya maza masu shekara talatin zuwa hamsin waɗanda sukan zo hidimar aiki a Tentin Sujada.

  15. “Ga aikin kabilar Gershonawa yayinda suke aiki, suke kuma ɗaukar kaya.

  16. Za su ɗauki labulen tabanakul, Tentin Sujada, kayan da za a rufe shi, da kuma kayan da za a rufe shi daga waje na fatun rufuwa na shanun teku, labulen ƙofar Tentin Sujada,

  17. labulen filin da yake kewaye da tabanakul da bagade, labulen ƙofa, igiyoyi da kuma dukan abubuwan da ake amfani da su wajen hidima. Geshonawa za su yi dukan abin da ya kamata a yi da waɗannan abubuwa.

  18. Dukan hidimominsu, ko na ɗauko, ko kuma na yin wani aiki, za a yi su ne bisa ga umarnin Haruna da ’ya’yansa. Za ka ba su dukan kayan da za su ɗauka a matsayin hakkinsu.

  19. Wannan shi ne hidimar da kabilar Gershonawa za su yi a Tentin Sujada. Ayyukansu za su kasance bisa ga umarnin Itamar ɗan Haruna firist.

  20. ’Ya’yan Lawi maza su ne, Gershom, Kohat da Merari.

  21. Waɗannan su ne sunayen ’ya’yan Gershom. Libni da Shimeyi.