Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Levites

186 ayoyi · 17 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Zuriyar ma’aikatan haikali da ta bayin Solomon su 392.

  2. Waɗansu sun hauro daga garuruwan Tel-Mela, Tel-Harsha, Kerub, Addon da Immer, amma ba su iya nuna cewa iyalansu su zuriyar Isra’ila ce ba,

  3. zuriyar Delahiya, Tobiya, da Nekoda 642.

  4. Na wajen firistoci kuwa su ne, Zuriyar Hobahiya, da ta Hakkoz, da ta Barzillai (wani mutumin da ya auri ’yar Barzillai mutumin Gileyad, aka kuma kira shi da wannan suna).

  5. Waɗannan ne aka nemi sunayensu a cikin tarihin asalin iyalai, amma ba a same su a ciki ba, saboda haka aka hana su shiga cikin firistoci, sun zama kamar marasa tsarki.

  6. Sai gwamna ya umarce su kada su ci wani abinci mafi tsarki, sai akwai firist da zai nemi nufin Ubangiji ta wurin Urim da Tummim.

  7. Yawan jama’ar duka ya kai mutum 42,360,

  8. ban da bayinsu maza da mata 7,337. Suna kuma da mawaƙa maza da mata 245.

  9. Akwai dawakai 736, alfadarai 245

  10. raƙuma 435, da kuma jakuna 6,720.

  11. Waɗansu shugabannin iyalai suka ba da kyautai domin taimakon aiki. Gwamna ya ba da darik 1,000 na zinariya, kwanoni 50, da riguna 530 don firistoci.

  12. Waɗansu shugabannin iyalai sun ba da darik 20,000 na zinariya da mina 2,200 na azurfa don aiki.

  13. Jimillar da sauran mutane suka bayar ta kai darik 20,000 na zinariya, minas 2,000 na azurfa, da riguna sittin da bakwai don firistoci.

  14. Firistoci, da Lawiyawa, da matsaran ƙofofi, da mawaƙa, da ma’aikatan haikali tare da waɗansu mutane da kuma sauran mutanen Isra’ila, suka zauna a garuruwansu. Da wata na bakwai ya zo, Isra’ilawa kuwa sun riga sun zauna a garuruwansu,

  15. Lawiyawan kuwa su ne, Yeshuwa ɗan Azaniya, da Binnuyi ɗan Henadad, da Kadmiyel,

  16. ’yan’uwansu kuwa su ne, Shebaniya, da Hodiya, da Kelita, da Felahiya, da Hanan,

  17. da Mika, da Rehob, da Hashabiya,

  18. da Zakkur, da Sherebiya, da Shebaniya,

  19. da Hodiya, da Bani da kuma Beninu.

  20. Shugabannin mutane su ne, Farosh, da Fahat-Mowab, da Elam, da Zattu, da Bani,

  21. da Bunni, da Azgad, da Bebai,

  22. da Adoniya, da Bigwai, da Adin,

  23. da Ater, da Hezekiya, da Azzur,

  24. da Hodiya, da Hashum, da Bezai,

  25. da Harif, da Anatot, da Nebai,