- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 1446–1406 BC
The Wilderness Years
Forty years of wandering in the desert test Israel's faith and prepare a new generation to enter the promised land.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Maimaitawar Shari’a 31:2kusan 1451 K.H.
“Yanzu shekaruna ɗari da ashirin ne, ba na iya kaiwa da komowa. Ubangiji ya ce mini, ‘Ba za ka haye Urdun ba.’
- Maimaitawar Shari’a 31:3kusan 1451 K.H.
Ubangiji Allahnku kansa zai haye a gabanku. Zai hallaka waɗannan al’ummai da suke gabanku, za ku kuwa mallaki ƙasarsu. Yoshuwa shi ma zai haye a gabanku, yadda Ubangiji ya faɗa.
- Maimaitawar Shari’a 31:4kusan 1451 K.H.
Ubangiji zai yi da su, yadda ya yi da Sihon da Og, sarakunan Amoriyawa, waɗanda ya hallaka tare da ƙasarsu.
- Maimaitawar Shari’a 31:5kusan 1451 K.H.
Ubangiji zai bashe su gare ku, dole kuma ku yi musu dukan abin da na umarce ku.
- Maimaitawar Shari’a 31:6kusan 1451 K.H.
Ku ƙarfafa, ku yi ƙarfin hali. Kada ku ji tsoro, ko ku firgita saboda su, gama Ubangiji Allahnku yana tafe tare da ku, ba zai taɓa barinku ko yă yashe ku ba.”
- Maimaitawar Shari’a 31:7kusan 1451 K.H.
Sai Musa ya kira Yoshuwa, ya ce masa a gaban dukan Isra’ila, “Ka ƙarfafa, ka kuma yi ƙarfin hali, gama dole ka tafi tare da mutanen nan zuwa cikin ƙasar da Ubangiji ya rantse cewa za ba wa kakanninku, dole kuma ka raba ta gare su ta zama gādonsu.
- Maimaitawar Shari’a 31:8kusan 1451 K.H.
Ubangiji kansa yana tafe a gabanka, zai kuma kasance tare da kai, ba zai taɓa barinka ko yă yashe ka ba. Kada ka ji tsoro; kada kuma ka karai.”
- Maimaitawar Shari’a 31:9kusan 1451 K.H.
Sai Musa ya rubuta wannan doka ya kuma ba da ita ga firistoci, ’ya’yan Lawi maza, waɗanda sukan ɗauka akwatin alkawarin Ubangiji, da kuma dukan dattawan Isra’ila.
- Maimaitawar Shari’a 31:10kusan 1451 K.H.
Sa’an nan Musa ya umarce su ya ce, “A ƙarshen kowace shekara bakwai, a shekara ta yafe basusuwa, a lokacin Bikin Tabanakul,
- Maimaitawar Shari’a 31:11kusan 1451 K.H.
sa’ad da dukan Isra’ila suka zo, don su bayyana a gaban Ubangiji Allahnku, a wurin da zai zaɓa, za ku karanta wannan doka a gabansu, a kunnuwansu.
- Maimaitawar Shari’a 31:12kusan 1451 K.H.
Ku tattara mutane, maza, mata da kuma yara, da baƙin da suke zama a cikin garuruwanku, saboda su saurara, su kuma koyi tsoron Ubangiji Allahnku, su lura, su bi dukan kalmomin wannan doka.
- Maimaitawar Shari’a 31:13kusan 1451 K.H.
’Ya’yansu, waɗanda ba su san wannan doka ba, dole su ji ta, su kuma koyi tsoron Ubangiji Allahnku muddin ranku a ƙasar da kuke haye Urdun ku ci gādonta.”
- Maimaitawar Shari’a 31:14kusan 1451 K.H.
Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Yanzu ranar mutuwarka ta yi kusa. Ka kira Yoshuwa, ku shigo Tentin Sujada, inda zan ba shi ragamar aiki.” Saboda haka Musa da Yoshuwa suka zo, suka kuma shiga Tentin Sujada.
- Maimaitawar Shari’a 31:15kusan 1451 K.H.
Ubangiji kuwa ya bayyana a Tentin Sujada a cikin ginshiƙin girgije, sai girgijen ya tsaya a ƙofar Tentin Sujada.
- Maimaitawar Shari’a 31:16kusan 1451 K.H.
Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Za ka huta tare da kakanninka, waɗannan mutane kuwa ba da daɗewa ba za su yi karuwanci ga baƙin alloli na ƙasar da za su shiga. Za su yashe ni su kuma karya alkawarin da na yi da su.
- Maimaitawar Shari’a 31:17kusan 1451 K.H.
A wannan rana zan yi fushi da su, in kuma yashe su; zan ɓoye fuskata daga gare su, za a kuwa hallaka su. Masifu masu yawa da wahaloli masu yawa za su auka musu, a wannan rana kuwa za su ce, ‘Masifun nan sun same mu domin Allahnmu ba ya tare da mu’
- Maimaitawar Shari’a 31:18kusan 1451 K.H.
Tabbatacce kuwa, zan ɓoye musu fuskata saboda muguntar da suka aikata, suka kuma bi gumaka.
- Maimaitawar Shari’a 31:19kusan 1451 K.H.
“To, sai ka rubuta wannan waƙa domin kanka, ka koya wa Isra’ilawa, ka kuma sa su rera ta, don tă zama shaida a kansu.
- Maimaitawar Shari’a 31:20kusan 1451 K.H.
Sa’ad da na kawo su cikin ƙasa mai zub da madara da zuma, ƙasar da na yi alkawari da rantsuwa ga kakanninsu, sa’ad da kuma suka ci suka ƙoshi, suka kuma yi ƙiba, za su juya ga waɗansu alloli su bauta musu, su ƙi ni, su kuma karya alkawarina.
- Maimaitawar Shari’a 31:21kusan 1451 K.H.
Sa’ad da kuma masifu masu yawa da wahaloli masu yawa suka auko musu, wannan waƙa za tă zama shaida a kansu, domin zuriyarsu ba za tă manta da ita ba. Na san abin da za su iya yi, kafin ma in kawo su cikin ƙasar da na yi musu alkawari da rantsuwa.”
- Maimaitawar Shari’a 31:22kusan 1451 K.H.
Sai Musa ya rubuta wannan waƙa a wannan rana, ya kuma koya wa Isra’ilawa.
- Maimaitawar Shari’a 31:23kusan 1451 K.H.
Ubangiji ya ba wa Yoshuwa ɗan Nun wannan umarni, “Ka ƙarfafa, ka kuma yi ƙarfin hali, gama za ka kawo Isra’ilawa cikin ƙasar da na yi musu alkawari da rantsuwa, ni kaina kuwa zan kasance tare da kai.”
- Maimaitawar Shari’a 31:24kusan 1451 K.H.
Bayan Musa ya gama rubuta kalmomin dokan nan a littafi daga farko zuwa ƙarshe,
- Maimaitawar Shari’a 31:25kusan 1451 K.H.
sai ya ba wa Lawiyawa, waɗanda suke ɗaukar akwatin alkawarin Ubangiji wannan umarni,
- Maimaitawar Shari’a 31:26kusan 1451 K.H.
“Ku ɗauki wannan Littafin Doka ku sa shi kusa da akwatin alkawarin Ubangiji Allahnku. A can zai kasance a matsayin shaida a kanku.