Tsallake zuwa abun ciki

circa 1446–1406 BC

The Wilderness Years

Forty years of wandering in the desert test Israel's faith and prepare a new generation to enter the promised land.

2,247 ayoyi · 2 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Ƙidaya 4:37kusan 1490 K.H.

    Jimillar dukan waɗanda suke na kabilan Kohatawa, waɗanda suka yi hidimar aiki a Tentin Sujada ke nan. Musa da Haruna sun ƙidaya su bisa ga umarnin Ubangiji.

  2. Ƙidaya 4:38kusan 1490 K.H.

    Aka ƙidaya mazan Gershonawa ta kabilansu da kuma iyalansu.

  3. Ƙidaya 4:39kusan 1490 K.H.

    Dukan maza daga shekara talatin zuwa hamsin waɗanda sukan zo hidimar aiki a Tentin Sujada,

  4. Ƙidaya 4:40kusan 1490 K.H.

    da aka ƙidaya kabila-kabila da kuma iyali-iyali, su 2,630 ne.

  5. Ƙidaya 4:41kusan 1490 K.H.

    Jimillar waɗanda suke na kabilar Gershonawa ke nan, waɗanda suka yi hidimar aiki a Tentin Sujada. Musa da Haruna sun ƙidaya su bisa ga umarnin Ubangiji.

  6. Ƙidaya 4:42kusan 1490 K.H.

    Aka ƙidaya mazan Merari ta kabilarsu da kuma iyalansu.

  7. Ƙidaya 4:43kusan 1490 K.H.

    Dukan maza daga shekara talatin zuwa hamsin waɗanda sukan zo hidimar aiki a Tentin Sujada,

  8. Ƙidaya 4:44kusan 1490 K.H.

    da aka ƙidaya kabila-kabila, su 3,200 ne.

  9. Ƙidaya 4:45kusan 1490 K.H.

    Jimillar waɗanda suke na kabilar Merari ke nan. Musa da Haruna suka ƙidaya su bisa ga umarnin Ubangiji.

  10. Ƙidaya 4:46kusan 1490 K.H.

    Saboda haka, Musa, Haruna da shugabannin Isra’ila, suka ƙidaya dukan Lawiyawa kabila-kabila da kuma iyali-iyali.

  11. Ƙidaya 4:47kusan 1490 K.H.

    Dukan maza daga shekara talatin zuwa hamsin waɗanda sukan zo hidimar aiki da kuma ɗaukar Tentin Sujada

  12. Ƙidaya 4:48kusan 1490 K.H.

    jimillarsu ta kai 8,580.

  13. Ƙidaya 4:49kusan 1490 K.H.

    Bisa ga umarnin Ubangiji ta wurin Musa, aka ba kowa aikinsa, aka kuma faɗa musu abin da za su ɗauka. Ta haka aka ƙidaya su, yadda Ubangiji ya umarci Musa.

  14. Ƙidaya 5:1kusan 1490 K.H.

    Ubangiji ya ce wa Musa,

  15. Ƙidaya 5:2kusan 1490 K.H.

    “Ka umarci Isra’ilawa su kori duk wanda yake da ciwon fatan jiki, ko mai ɗiga na kowane iri, ko wanda ya ƙazantu ta wurin taɓa gawa, daga cikin sansani.

  16. Ƙidaya 5:3kusan 1490 K.H.

    Ka kori maza da mata ma; ka kai su bayan sansani domin kada su ƙazantar da sansani inda nake zama a cikinsu.”

  17. Ƙidaya 5:4kusan 1490 K.H.

    Isra’ilawa suka yi haka; suka kore su daga sansanin. Suka aikata yadda dai Ubangiji ya umarci Musa.

  18. Ƙidaya 5:5kusan 1490 K.H.

    Ubangiji ya ce wa Musa,

  19. Ƙidaya 5:6kusan 1490 K.H.

    “Gaya wa Isra’ilawa, ‘Sa’ad da namiji ko mace ya yi wa ɗan’uwansa laifi ta kowace hanya, ta yin haka, ya yi rashin aminci ga Ubangiji, mutumin kuwa ya yi laifi ke nan

  20. Ƙidaya 5:7kusan 1490 K.H.

    kuma dole yă furta zunubin da ya yi. Dole yă yi biya cikakkiyar diyya saboda laifinsa, yă ƙara kashi ɗaya bisa biyar a kai, yă kuma bayar da shi duka ga wanda ya yi wa laifin.

  21. Ƙidaya 5:8kusan 1490 K.H.

    Amma in mutumin da aka yi wa laifin ba shi da ɗan’uwa na kusa da za a biya diyya saboda laifin, sai diyyar tă zama ta Ubangiji, dole kuma a ba wa firist, haɗe da ragon da za a yi kafara da shi.

  22. Ƙidaya 5:9kusan 1490 K.H.

    Dukan tsarkakakkun abubuwan da Isra’ilawa suka kawo wa firist za su zama nasa.

  23. Ƙidaya 5:10kusan 1490 K.H.

    Kowace tsarkakakkiyar kyauta da mutum ya kawo nasa ne, sai dai abin da ya ba wa firist, zai zama na firist.’ ”

  24. Ƙidaya 5:11kusan 1490 K.H.

    Sai Ubangiji ya ce wa Musa,

  25. Ƙidaya 5:12kusan 1490 K.H.

    “Yi magana da Isra’ilawa, ka ce musu, ‘In matar wani ta kauce, ta kuma yi rashin aminci gare shi