Tsallake zuwa abun ciki

circa 1446–1406 BC

The Wilderness Years

Forty years of wandering in the desert test Israel's faith and prepare a new generation to enter the promised land.

2,247 ayoyi · 2 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Ƙidaya 6:7kusan 1490 K.H.

    Ko da ma gawar ta mahaifinsa ce, ko ta mahaifiyarsa, ko ta ɗan mahaifiyarsa, ko kuma ta ’yar’uwarsa ce, ba zai ƙazantar da kansa saboda su ba, domin alamar keɓewarsa ga Allah tana kansa.

  2. Ƙidaya 6:8kusan 1490 K.H.

    A dukan kwanakin keɓewarsa, an tsarkake shi ga Ubangiji.

  3. Ƙidaya 6:9kusan 1490 K.H.

    “ ‘In farat ɗaya wani ya mutu kusa da shi, to, keɓewarsa ta ƙazantu, dole yă aske kansa a ranar tsarkakewarsa, a rana ta bakwai.

  4. Ƙidaya 6:10kusan 1490 K.H.

    Sa’an nan a rana ta takwas, tilas yă kawo wa firist ’yan kurciyoyi biyu, ko kuma ’yan tattabarai biyu a bakin ƙofar Tentin Sujada.

  5. Ƙidaya 6:11kusan 1490 K.H.

    Firist kuwa zai miƙa ɗaya don hadaya ta zunubi, ɗayan kuma don hadaya ta ƙonawa, yă yi kafara dominsa, gama ya yi zunubi ta dalilin gawar. A wannan rana zai sāke keɓe kansa.

  6. Ƙidaya 6:12kusan 1490 K.H.

    Dole yă keɓe kansa ga Ubangiji, har kwanakin keɓewarsa, kuma dole yă kawo ɗan rago bana ɗaya a matsayin hadayar laifi. Kwanakin baya ba sa cikin lissafi, domin ya ƙazantu a lokacin keɓewarsa.

  7. Ƙidaya 6:13kusan 1490 K.H.

    “ ‘To, ga doka saboda Banazare sa’ad da kwanakin keɓewarsa suka gama. Za a kawo shi a bakin ƙofar Tentin Sujada.

  8. Ƙidaya 6:14kusan 1490 K.H.

    A can zai miƙa hadayunsa ga Ubangiji. Hadayun kuwa su ne, ɗan rago, bana ɗaya marar lahani don hadaya ta ƙonawa, ’yar tunkiya, bana ɗaya marar lahani na hadaya don zunubi, rago marar lahani don hadaya ta salama,

  9. Ƙidaya 6:15kusan 1490 K.H.

    tare da hadayu na hatsi da hadayu na sha, da kuma kwando burodi marar yisti, ƙosai da aka yi da lallausan gari kwaɓaɓɓe da mai, da kuma wainan da aka barbaɗa da mai.

  10. Ƙidaya 6:16kusan 1490 K.H.

    “ ‘Firist zai kawo su a gaban Ubangiji, yă miƙa hadaya don zunubi da hadaya ta ƙonawa.

  11. Ƙidaya 6:17kusan 1490 K.H.

    Zai miƙa kwandon burodi marar yisti, yă kuma miƙa ɗan ragon hadaya ta salama tare da hadaya ta gari, da hadaya ta sha ga Ubangiji.

  12. Ƙidaya 6:18kusan 1490 K.H.

    “ ‘Sa’an nan a ƙofar Tentin Sujada, dole Banazaren yă aske gashin da ya alamta keɓewarsa, yă kwashe gashin, yă zuba a cikin wutar da take ƙarƙashin hadaya ta salama.

  13. Ƙidaya 6:19kusan 1490 K.H.

    “ ‘Bayan Banazaren ya aske gashinsa da ya alamta keɓewa, firist zai ɗauki dafaffiyar kafaɗar rago, da ƙosai da kuma waina daga cikin kwando waɗanda duka biyu marar yisti ne, yă sa su a tafin hannun keɓaɓɓen.

  14. Ƙidaya 6:20kusan 1490 K.H.

    Firist zai kaɗa su a gaban Ubangiji, hadaya ce ta kaɗawa; mai tsarki ne kuma, zai zama na firist, tare da ƙirjin da aka kaɗa da kuma cinyar da aka kawo. Bayan haka, Banazaren zai iya shan ruwan inabi.

  15. Ƙidaya 6:21kusan 1490 K.H.

    “ ‘Wannan ita ce dokar Banazare wanda ya yi alkawari ga Ubangiji bisa ga keɓewarsa, tare da duk abin da zai iya bayarwa. Tilas yă cika alkawarin da ya yi bisa ga dokar zaman Banazare.’ ”

  16. Ƙidaya 6:22kusan 1490 K.H.

    Ubangiji ya ce wa Musa,

  17. Ƙidaya 6:23kusan 1490 K.H.

    “Gaya wa Haruna da ’ya’yansa, ‘Ga yadda za ku albarkaci Isra’ilawa. Za ku ce musu,

  18. Ƙidaya 6:24kusan 1490 K.H.

    “ ‘ “Ubangiji yă albarkace ku, yă kuma kiyaye ku;

  19. Ƙidaya 6:25kusan 1490 K.H.

    Ubangiji yă sa fuskarsa ta haskaka a kanku, yă kuma yi muku alheri;

  20. Ƙidaya 6:26kusan 1490 K.H.

    Ubangiji yă dube ku da idon rahama, yă kuma ba ku salama.” ’

  21. Ƙidaya 6:27kusan 1490 K.H.

    “Da haka za su sa sunana a kan Isra’ilawa, ni kuma zan albarkace su.”

  22. Ƙidaya 7:1kusan 1490 K.H.

    Sa’ad da Musa ya gama kafa tabanakul, sai ya shafe shi da mai, ya tsarkake shi tare da dukan kayayyakinsa, ya kuma shafe bagaden da mai, ya tsarkake shi da dukan kayayyakinsa.

  23. Ƙidaya 7:2kusan 1490 K.H.

    Sa’an nan shugabannin Isra’ila, wato, shugabannin iyalai waɗanda suke shugabancin kabilan da aka ƙidaya, suka miƙa hadayu.

  24. Ƙidaya 7:3kusan 1490 K.H.

    Suka kawo kyautansu a gaban Ubangiji. Kyautayin kuwa su ne, kekunan yaƙi shida da aka rufe, da shanu goma sha biyu, saniya guda daga kowane shugaba, da kuma keken yaƙi guda daga shugabanni biyu. Suka miƙa waɗannan a gaban tabanakul.

  25. Ƙidaya 7:4kusan 1490 K.H.

    Ubangiji ya ce wa Musa,