Tsallake zuwa abun ciki

circa 1446–1406 BC

The Wilderness Years

Forty years of wandering in the desert test Israel's faith and prepare a new generation to enter the promised land.

2,247 ayoyi · 2 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Ƙidaya 5:13kusan 1490 K.H.

    ta wurin kwana da wani dabam, wannan kuwa ya kasance a ɓoye ga mijinta, rashin tsarkinta kuwa bai tonu ba (da yake babu shaida, ba a kuma kama ta tana yi ba),

  2. Ƙidaya 5:14kusan 1490 K.H.

    in kuma kishi ya sha kan mijinta kuma tana da ƙazanta, ko kuwa idan yana kishi yana kuma zatonta ko ma ba ta da ƙazanta

  3. Ƙidaya 5:15kusan 1490 K.H.

    mijin zai kai matansa a gaban firist, yă kuma kawo hadayar abubuwan da ake bukata; abubuwa kamar, garin sha’ir garwa ɗaya, amma kada yă zuba mai a kan garin sha’ir, kada kuma yă sa turaren wuta a kansa, domin hadaya ce ta miji mai tuhumar matarsa da aka kawo domin gaskiya tă fito fili.

  4. Ƙidaya 5:16kusan 1490 K.H.

    “ ‘Firist zai kawo ta, yă sa tă tsaya a gaban Ubangiji.

  5. Ƙidaya 5:17kusan 1490 K.H.

    Sa’an nan zai ɗebi ruwa mai tsarki a tulun laka, yă zuba ƙurar da ya ɗebo daga daɓen tabanakul a cikin ruwan.

  6. Ƙidaya 5:18kusan 1490 K.H.

    Bayan da firist ya sa matan ta tsaya a gaban Ubangiji, sai yă kunce gashin kanta, yă kuma sa hadaya ta gari don tunawa a hannuwanta, hadayar gari ce ta kishi, yayinda shi kansa zai riƙe ruwa mai ɗaci, mai jawo la’ana.

  7. Ƙidaya 5:19kusan 1490 K.H.

    Sa’an nan firist zai sa tă yi rantsuwa, yă kuma ce mata, “In ba wani mutumin da ya kwana da ke kuma ba ki kauce kin ƙazantar da kanki yayinda kike auren mijinki ba, kada wannan ruwa mai ɗaci, mai jawo la’ana, yă cuce ki.

  8. Ƙidaya 5:20kusan 1490 K.H.

    Amma in kin kauce yayinda kike auren mijinki, kika kuma ƙazantar da kanki ta wurin kwana da wani dabam da ba mijinki ba,”

  9. Ƙidaya 5:21kusan 1490 K.H.

    (a nan firist zai sa macen a ƙarƙashin la’anar rantsuwa cewa) “bari Ubangiji yă sa mutanenki su la’ance ki, su kuma yi Allah wadai da ke, sa’ad da Ubangiji ya sa cinyarki ta shanye, cikinki kuma ya kumbura.

  10. Ƙidaya 5:22kusan 1490 K.H.

    Bari wannan ruwa mai jawo la’ana, yă shiga jikinki saboda cikinki yă kumbura, cinyarki kuma yă shanye.” “ ‘Sai macen tă ce, “Amin. Bari yă zama haka.”

  11. Ƙidaya 5:23kusan 1490 K.H.

    “ ‘Firist zai rubuta waɗannan la’anoni a littafi, sa’an nan yă wanke su cikin ruwa mai ɗaci.

  12. Ƙidaya 5:24kusan 1490 K.H.

    Sai yă sa macen tă sha ruwa mai ɗaci, mai jawo la’ana, wannan ruwa kuwa zai shiga cikinta yă kawo mata wahala mai zafi.

  13. Ƙidaya 5:25kusan 1490 K.H.

    Firist zai karɓi hadaya ta gari don kishi daga hannuwanta, yă kaɗa shi a gaban Ubangiji sa’an nan yă kawo a bagade.

  14. Ƙidaya 5:26kusan 1490 K.H.

    Sa’an nan firist zai ɗiba hatsi na hadaya cike da hannunsa don hadayar tunawa, yă kuma ƙone a bagade; bayan haka sai yă sa macen tă sha ruwan.

  15. Ƙidaya 5:27kusan 1490 K.H.

    In ta ƙazantar da kanta ta kuma ci amanar mijinta, to, yayinda aka sa tă sha ruwa mai jawo la’ana, ruwan zai shiga cikinta, yă jawo mata wahala mai zafi; cikinta zai kumbura, cinyarta kuma yă shanye, tă kuwa zama la’ananniya a cikin mutanenta.

  16. Ƙidaya 5:28kusan 1490 K.H.

    Amma fa, in macen ba tă ƙazantar da kanta ba, ba tă kuma da ƙazanta, za a kuɓutar da ita daga laifin, za tă kuma iya haihuwa.

  17. Ƙidaya 5:29kusan 1490 K.H.

    “ ‘Wannan dai, ita ce dokar kishi sa’ad da mace ta kauce, ta kuma ƙazantar da kanta yayinda take aure da mijinta,

  18. Ƙidaya 5:30kusan 1490 K.H.

    ko kuma sa’ad da mijin yana kishi domin yana shakkar matarsa. Firist zai sa tă tsaya a gaban Ubangiji, yă kuma yi amfani da wannan doka gaba ɗaya a kanta.

  19. Ƙidaya 5:31kusan 1490 K.H.

    Mijin zai zama marar laifi daga kowane laifi, amma matar za tă ɗauki muguntarta, idan ta yi laifin.’ ”

  20. Ƙidaya 6:1kusan 1490 K.H.

    Ubangiji ya ce wa Musa,

  21. Ƙidaya 6:2kusan 1490 K.H.

    “Yi magana da Isra’ilawa, ka ce musu, ‘In mace, ko namiji yana so yă yi alkawari na musamman, alkawarin zaman keɓaɓɓe ga Ubangiji, a matsayin Banazare,

  22. Ƙidaya 6:3kusan 1490 K.H.

    dole yă keɓe kansa daga ruwan inabi, ko daga waɗansu abubuwa sha masu sa maye, kada kuma yă sha ruwan tsamin da aka yi daga ruwan inabi, ko daga waɗansu abubuwa sha masu sa maye. Ba zai sha ruwan ’ya’yan inabi, ko yă ci ’ya’yan inabi ɗanye ko busasshe ba.

  23. Ƙidaya 6:4kusan 1490 K.H.

    Muddin yana Banazare, ba zai ci wani abin da ya fito daga ’ya’yan inabi ba, ko ƙwayar inabi, ko ɓawonsa ma.

  24. Ƙidaya 6:5kusan 1490 K.H.

    “ ‘A dukan lokacin da yake a kan alkawarin keɓewarsa, reza ba zai taɓa kansa. Dole yă kasance da tsarki har ƙarshen keɓewarsa ga Ubangiji; tilas yă bar gashin kansa yă yi tsawo.

  25. Ƙidaya 6:6kusan 1490 K.H.

    A dukan kwanakin keɓewarsa ga Ubangiji, Banazarin ba zai yi kusa da gawa ba.