Tsallake zuwa abun ciki

circa 1446–1406 BC

The Wilderness Years

Forty years of wandering in the desert test Israel's faith and prepare a new generation to enter the promised land.

2,247 ayoyi · 2 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Ƙidaya 7:30kusan 1490 K.H.

    A ranan ta huɗu, Elizur ɗan Shedeyur, shugaban mutanen Ruben, ya kawo hadayarsa.

  2. Ƙidaya 7:31kusan 1490 K.H.

    Hadayar da ya kawo ita ce, faranti guda ɗaya na azurfa, nauyinsa shekel ɗari ɗaya da talatin, da kuma daro na yayyafawa na azurfa, nauyinsa shekel saba’in, dukan biyu, an auna su bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, kowannensu cike da lallausan gari, haɗe da mai kamar hadaya ta gari;

  3. Ƙidaya 7:32kusan 1490 K.H.

    ya kuma kawo kwanon zinariya ɗaya mai nauyin shekel goma, cike da turaren hayaƙi;

  4. Ƙidaya 7:33kusan 1490 K.H.

    da ƙaramin bijimi guda ɗaya, tunkiya ɗaya, da rago, dukansu bana ɗaya-ɗaya domin hadaya ta ƙonawa;

  5. Ƙidaya 7:34kusan 1490 K.H.

    ya kuma kawo bunsuru ɗaya domin hadaya don zunubi;

  6. Ƙidaya 7:35kusan 1490 K.H.

    da shanu biyu, raguna biyar, bunsurai biyar da kuma ’yan raguna biyar, dukansu bana ɗaya-ɗaya, a miƙa su hadaya ta salama. Wannan ita ce hadayar Elizur ɗan Shedeyur.

  7. Ƙidaya 7:36kusan 1490 K.H.

    A rana ta biyar, Shelumiyel ɗan Zurishaddai, shugaban mutanen Simeyon, ya kawo hadayarsa.

  8. Ƙidaya 7:37kusan 1490 K.H.

    Hadayar da ya kawo ita ce, faranti guda ɗaya na azurfa, nauyinsa shekel ɗari ɗaya da talatin, da kuma daro na yayyafawa na azurfa, nauyinsa shekel saba’in, dukan biyu, an auna su bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, kowannensu cike da lallausan gari, haɗe da mai kamar hadaya ta gari;

  9. Ƙidaya 7:38kusan 1490 K.H.

    ya kuma kawo kwanon zinariya ɗaya mai nauyin shekel goma, cike da turaren hayaƙi;

  10. Ƙidaya 7:39kusan 1490 K.H.

    da ƙaramin bijimi guda ɗaya, tunkiya ɗaya, da rago, dukansu bana ɗaya-ɗaya domin hadaya ta ƙonawa;

  11. Ƙidaya 7:40kusan 1490 K.H.

    ya kuma kawo bunsuru ɗaya domin hadaya don zunubi;

  12. Ƙidaya 7:41kusan 1490 K.H.

    da shanu biyu, raguna biyar, bunsurai biyar da kuma ’yan raguna biyar, dukansu bana ɗaya-ɗaya, a miƙa su hadaya ta salama. Wannan ita ce hadayar Shelumiyel ɗan Zurishaddai.

  13. Ƙidaya 7:42kusan 1490 K.H.

    A rana ta shida, Eliyasaf ɗan Deyuwel, shugaban mutanen Gad, ya kawo hadayarsa.

  14. Ƙidaya 7:43kusan 1490 K.H.

    Hadayar da ya kawo ita ce, faranti guda ɗaya na azurfa, nauyinsa shekel ɗari ɗaya da talatin, da kuma daro na yayyafawa na azurfa, nauyinsa shekel saba’in, dukan biyu, an auna su bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, kowannensu cike da lallausan gari, haɗe da mai kamar hadaya ta gari;

  15. Ƙidaya 7:44kusan 1490 K.H.

    ya kuma kawo kwanon zinariya ɗaya mai nauyin shekel goma, cike da turaren hayaƙi;

  16. Ƙidaya 7:45kusan 1490 K.H.

    da ƙaramin bijimi guda ɗaya, tunkiya ɗaya, da rago, dukansu bana ɗaya-ɗaya domin hadaya ta ƙonawa;

  17. Ƙidaya 7:46kusan 1490 K.H.

    ya kuma kawo bunsuru ɗaya domin hadaya don zunubi;

  18. Ƙidaya 7:47kusan 1490 K.H.

    da shanu biyu, raguna biyar, bunsurai biyar da kuma ’yan raguna biyar, dukansu bana ɗaya-ɗaya, a miƙa su hadaya ta salama. Wannan ita ce hadayar Eliyasaf ɗan Deyuwel.

  19. Ƙidaya 7:48kusan 1490 K.H.

    A rana ta bakwai, Elishama ɗan Ammihud, shugaban mutanen Efraim, ya kawo hadayarsa.

  20. Ƙidaya 7:49kusan 1490 K.H.

    Hadayar da ya kawo ita ce, faranti guda ɗaya na azurfa, nauyinsa shekel ɗari ɗaya da talatin, da kuma daro na yayyafawa na azurfa, nauyinsa shekel saba’in, dukan biyu, an auna su bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, kowannensu cike da lallausan gari, haɗe da mai kamar hadaya ta gari;

  21. Ƙidaya 7:50kusan 1490 K.H.

    kwanon zinariya ɗaya mai nauyin shekel goma, cike da turaren hayaƙi;

  22. Ƙidaya 7:51kusan 1490 K.H.

    da ƙaramin bijimi guda ɗaya, tunkiya ɗaya, da rago, dukansu bana ɗaya-ɗaya domin hadaya ta ƙonawa;

  23. Ƙidaya 7:52kusan 1490 K.H.

    ya kuma kawo bunsuru ɗaya domin hadaya don zunubi;

  24. Ƙidaya 7:53kusan 1490 K.H.

    da shanu biyu, raguna biyar, bunsurai biyar da kuma ’yan raguna biyar, dukansu bana ɗaya-ɗaya, a miƙa su hadaya ta salama. Wannan ita ce hadayar Elishama ɗan Ammihud.

  25. Ƙidaya 7:54kusan 1490 K.H.

    A rana ta takwas, Gamaliyel ɗan Fedazur, shugaban mutanen Manasse, ya kawo hadayarsa.