- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 1446–1406 BC
The Wilderness Years
Forty years of wandering in the desert test Israel's faith and prepare a new generation to enter the promised land.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Ƙidaya 3:38kusan 1490 K.H.
Musa da Haruna da ’ya’yansu za su yi sansani gabas da tabanakul, wajen fitowar rana; a gaban Tentin Sujada. Su ne da hakkin lura da wuri mai tsarki a madadin Isra’ilawa. Duk wani wanda ba ya wannan aiki, ya kuma kusaci wuri mai tsarki, za a kashe shi.
- Ƙidaya 3:39kusan 1490 K.H.
Jimillar Lawiyawan da Musa da Haruna suka ƙidaya bisa ga umarnin Ubangiji bisa ga danginsu, haɗe da kowane jariri daga wata ɗaya ko fiye, 22,000 ne.
- Ƙidaya 3:40kusan 1490 K.H.
Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Ƙidaya dukan ’ya’yan fari na Isra’ilawa maza daga wata ɗaya da kuma fiye ka kuma rubuta sunayensu.
- Ƙidaya 3:41kusan 1490 K.H.
Ka ɗauko mini Lawiyawa a maimakon dukan ’ya’yan fari na Isra’ilawa, haka ma na dabbobi na Lawiyawa, a maimakon ’ya’yan fari na dabbobin Isra’ilawa. Ni ne Ubangiji.”
- Ƙidaya 3:42kusan 1490 K.H.
Haka Musa ya ƙidaya ’ya’yan fari na Isra’ilawa, yadda Ubangiji ya umarce shi.
- Ƙidaya 3:43kusan 1490 K.H.
Jimillar ’ya’yan fari maza daga wata ɗaya da kuma fiye, da aka rubuta bisa ga sunayensu, 22,273 ne.
- Ƙidaya 3:44kusan 1490 K.H.
Sai Ubangiji ya kuma yi magana da Musa ya ce,
- Ƙidaya 3:45kusan 1490 K.H.
“Ka ɗauki Lawiyawa a maimakon dukan ’ya’yan fari na Isra’ila, dabbobin Lawiyawa kuma a maimakon dabbobinsu. Lawiyawa za su zama nawa. Ni ne Ubangiji.
- Ƙidaya 3:46kusan 1490 K.H.
Don a fanshi ’ya’yan fari 273 na Isra’ilawa da suka fi Lawiyawa yawa,
- Ƙidaya 3:47kusan 1490 K.H.
ka karɓi shekel biyar domin kowannensu, bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, wanda yake da nauyin gera ashirin.
- Ƙidaya 3:48kusan 1490 K.H.
Ka ba wa Haruna da ’ya’yansa kuɗin fansar da ya haura kai na ’ya’yan farin Isra’ilawa.”
- Ƙidaya 3:49kusan 1490 K.H.
Haka, Musa ya karɓi kuɗin fansar waɗanda suka haura yawan Lawiyawa.
- Ƙidaya 3:50kusan 1490 K.H.
Daga ’ya’yan fari na Isra’ilawa, ya karɓi azurfa masu nauyin shekel 1,365, bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri.
- Ƙidaya 3:51kusan 1490 K.H.
Sa’an nan Musa ya ba da kuɗin fansar ga Haruna da ’ya’yansa, yadda maganar Ubangiji ta umarce shi.
- Ƙidaya 4:1kusan 1490 K.H.
Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna,
- Ƙidaya 4:2kusan 1490 K.H.
“Ku yi ƙidaya Kohatawa daga Lawiyawa, bisa ga kabilarsu da iyalansu.
- Ƙidaya 4:3kusan 1490 K.H.
Ku ƙidaya dukan maza daga shekara talatin zuwa hamsin da suka zo domin aiki a Tentin Sujada.
- Ƙidaya 4:4kusan 1490 K.H.
“Ga aikin Kohatawa a Tentin Sujada, kulawa da kayayyaki mafi tsarki.
- Ƙidaya 4:5kusan 1490 K.H.
Lokacin da za a tashi daga sansani, Haruna da ’ya’yansa za su shiga ciki su kunce labulen kāriya, su rufe Akwatin Alkawari da shi.
- Ƙidaya 4:6kusan 1490 K.H.
Sa’an nan su rufe shi da fatun shanun teku, su shimfiɗa zane mai ruwan shuɗi a bisansa, su sa masa sandunansa.
- Ƙidaya 4:7kusan 1490 K.H.
“A bisa teburin Burodin Ajiyewa, za su shimfiɗa zane mai ruwan shuɗi, a kansa kuma su sa farantai, kwanoni da manyan kwanoni, da tuluna don hadayun sha; da burodin da zai ci gaba da kasancewa a kansa.
- Ƙidaya 4:8kusan 1490 K.H.
A bisa waɗannan za su shimfiɗa jan zane, su rufe su da fatun shanun teku, su kuma zura masa sandunansa.
- Ƙidaya 4:9kusan 1490 K.H.
“Za su ɗauki zane mai ruwan shuɗi su rufe wurin ajiye fitilan da yake don fitilu, tare da fitilunsa, lagwaninsa da farantansa, da dukan tulunansa don man amfaninsu.
- Ƙidaya 4:10kusan 1490 K.H.
Sa’an nan su naɗe shi da kuma dukan kayayyakinsa a cikin fatar shanun teku, su sa shi a kan sandan ɗaukarsa.
- Ƙidaya 4:11kusan 1490 K.H.
“A kan bagaden zinariya, za su shimfiɗa zane mai ruwan shuɗi, su kuma rufe shi da fatar shanun teku, sai a zura masa sandunansa.