Tsallake zuwa abun ciki

circa 1446–1406 BC

The Wilderness Years

Forty years of wandering in the desert test Israel's faith and prepare a new generation to enter the promised land.

2,247 ayoyi · 2 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Ƙidaya 2:22kusan 1490 K.H.

    Na biye da su su ne mutanen Benyamin. Shugaban mutanensu kuwa Abidan ɗan Gideyoni.

  2. Ƙidaya 2:23kusan 1490 K.H.

    Yawan mutanen sashensa 35,400 ne.

  3. Ƙidaya 2:24kusan 1490 K.H.

    Dukan mazan da aka ba su aiki a sansanin Efraim, bisa ga sashensu su kai 108,100 ne. Su ne za su zama na uku sa’ad da za a tashi.

  4. Ƙidaya 2:25kusan 1490 K.H.

    A arewa za a sami sashen sansanin Dan, a ƙarƙashin ƙa’idarsu. Shugabansu shi ne Ahiyezer ɗan Ammishaddai.

  5. Ƙidaya 2:26kusan 1490 K.H.

    Yawan mutanen sashensa 62,700 ne.

  6. Ƙidaya 2:27kusan 1490 K.H.

    Kabilar Asher ce za tă zama ta biye. Shugabansu shi ne Fagiyel ɗan Okran.

  7. Ƙidaya 2:28kusan 1490 K.H.

    Yawan mutanen sashensa 41,500 ne.

  8. Ƙidaya 2:29kusan 1490 K.H.

    Kabilar Naftali za su zama na biye da su. Shugaban mutanen kuwa shi ne Ahira ɗan Enan.

  9. Ƙidaya 2:30kusan 1490 K.H.

    Yawan mutanen sashensa 53,400 ne

  10. Ƙidaya 2:31kusan 1490 K.H.

    Dukan mazan da aka ba su aiki a sansanin Efraim, bisa ga sashensu su kai 157,600. Su ne za su zama na ƙarshe, ƙarƙashin ƙa’idarsu.

  11. Ƙidaya 2:32kusan 1490 K.H.

    Waɗannan su ne Isra’ilawan da aka a ƙidaya bisa ga iyalansu. Dukansu da suke a sansani, mutane 603,550 ne.

  12. Ƙidaya 2:33kusan 1490 K.H.

    Ba a dai ƙidaya Lawiyawa tare da sauran Isra’ilawa ba yadda Ubangiji ya umarci Musa.

  13. Ƙidaya 2:34kusan 1490 K.H.

    Saboda haka Isra’ilawa suka yi duk ko mene ne da Ubangiji ya umarci Musa. Ta haka ne suka yi sansani a ƙarƙashin ƙa’idarsu kowanne tare da kabilarsa da danginsa.

  14. Ƙidaya 3:1kusan 1490 K.H.

    Waɗannan su ne zuriyar Haruna da Musa a lokacin da Ubangiji ya yi magana da Musa a kan Dutsen Sinai.

  15. Ƙidaya 3:2kusan 1490 K.H.

    Sunayen ’ya’yan Haruna su ne, Nadab ɗan fari, da Abihu, da Eleyazar da Itamar.

  16. Ƙidaya 3:3kusan 1490 K.H.

    Waɗannan su ne sunayen ’ya’yan Haruna, shafaffun firistocin da aka naɗa domin su yi aiki firist.

  17. Ƙidaya 3:4kusan 1490 K.H.

    Amma Nadab da Abihu suka fāɗi suka mutu a gaban Ubangiji a Hamadar Sinai a sa’ad da suka ƙona turare da haramtacciyar wuta a gabansa. Ba su kuwa da ’ya’ya; saboda haka Eleyazar da Itamar kaɗai suka yi aiki firist a zamanin mahaifinsu Haruna.

  18. Ƙidaya 3:5kusan 1490 K.H.

    Ubangiji ya ce wa Musa,

  19. Ƙidaya 3:6kusan 1490 K.H.

    “Ka kawo mutanen Lawi, ka kuma gabatar da su ga Haruna firist, don su taya shi aiki.

  20. Ƙidaya 3:7kusan 1490 K.H.

    Za su yi wa Haruna da dukan al’umma aikace-aikace a Tentin Sujada, ta wurin yin aikin tabanakul.

  21. Ƙidaya 3:8kusan 1490 K.H.

    Za su lura da dukan kayayyakin Tentin Sujada, suna cika hakkin Isra’ilawa ta wurin yin aiki a tabanakul.

  22. Ƙidaya 3:9kusan 1490 K.H.

    Ka ba da Lawiyawa ga Haruna da ’ya’yansa; su ne za su zama Isra’ilawan da za a ba da su ɗungum gare shi.

  23. Ƙidaya 3:10kusan 1490 K.H.

    Ka naɗa Haruna da ’ya’yansa su yi aiki firistoci; duk wanda ya yi shisshigi a wuri mai tsarki kuwa dole a kashe shi.”

  24. Ƙidaya 3:11kusan 1490 K.H.

    Ubangiji ya kuma ce wa Musa,

  25. Ƙidaya 3:12kusan 1490 K.H.

    “Ga shi na ɗauki Lawiyawa daga cikin Isra’ilawa a maimakon ɗan fari na kowace mace a Isra’ila. Lawiyawa nawa ne,