- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 1446–1406 BC
The Wilderness Years
Forty years of wandering in the desert test Israel's faith and prepare a new generation to enter the promised land.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Ƙidaya 3:13kusan 1490 K.H.
gama duk ’ya’yan fari nawa ne. Lokacin da karkashe duk ’ya’yan fari a Masar, na keɓe wa kaina kowane ɗan fari a Isra’ila, ko mutum, ko dabba. Za su zama nawa. Ni ne Ubangiji.”
- Ƙidaya 3:14kusan 1490 K.H.
Ubangiji ya yi magana da Musa a Hamadar Sinai ya ce,
- Ƙidaya 3:15kusan 1490 K.H.
“Ka ƙidaya Lawiyawa bisa ga iyalansu da kabilarsu. Ka ƙidaya kowane ɗan jinjiri mai wata ɗaya ko fiye.”
- Ƙidaya 3:16kusan 1490 K.H.
Saboda haka Musa ya ƙidaya su duka, kamar yadda maganar Ubangiji ta umarta.
- Ƙidaya 3:17kusan 1490 K.H.
Ga sunayen ’ya’yan Lawi, Gershon, Kohat da Merari.
- Ƙidaya 3:18kusan 1490 K.H.
Ga sunayen mutanen Gershon, Libni, da Shimeyi
- Ƙidaya 3:19kusan 1490 K.H.
Sunayen mutanen Kohat kuwa su ne, Amram, Izhar, Hebron da Uzziyel.
- Ƙidaya 3:20kusan 1490 K.H.
Dangin Merari su ne. Mali da Mushi. Ga kabilan Lawiyawa bisa ga iyalansu.
- Ƙidaya 3:21kusan 1490 K.H.
A wajen Gershonawa, kabilarsa su ne Libniyawa, da Shimeyiyawa; waɗannan su ne mutanen Gershom.
- Ƙidaya 3:22kusan 1490 K.H.
Jimillar dukan jarirai maza daga wata ɗaya zuwa gaba da haihuwa su kai 7,500.
- Ƙidaya 3:23kusan 1490 K.H.
Kabilar Gershonawa za su yi sansani ta fuskar yamma, a bayan tabanakul.
- Ƙidaya 3:24kusan 1490 K.H.
Eliyasaf ɗan Layel shi ne shugaban iyalan Gershonawa.
- Ƙidaya 3:25kusan 1490 K.H.
A Tentin Sujada, Gershonawa su ne za su lura da mazauni da tabanakul da kuma tentin, abubuwan rufensa, labule a ƙofar Tentin Sujada,
- Ƙidaya 3:26kusan 1490 K.H.
da labulen filin da yake kewaye da tabanakul da kuma bagade, da igiyoyi, da kuma kowane abin da ya danganci aikinsu.
- Ƙidaya 3:27kusan 1490 K.H.
Kabilar Kohat su ne, Amramawa da Izharawa da Hebronawa da Uzziyelawa; waɗannan su ne kabilar Kohatawa.
- Ƙidaya 3:28kusan 1490 K.H.
Jimillar dukan jarirai maza daga wata ɗaya ko fiye, 8,600 ne. Kohatawa ne suke lura da wuri mai tsarki.
- Ƙidaya 3:29kusan 1490 K.H.
Kohatawa za su yi sansani a kudu da tabanakul.
- Ƙidaya 3:30kusan 1490 K.H.
Shugaban kabilar Kohatawa shi ne Elizafan ɗan Uzziyel.
- Ƙidaya 3:31kusan 1490 K.H.
Su ne da hakkin kula da akwatin alkawari, tebur, wurin ajiye fitila, bagade, kayayyakin wuri mai tsarki da ake amfani da su a sujada, labule, da kuma kome da ya danganci aikinsu.
- Ƙidaya 3:32kusan 1490 K.H.
Babban shugaban Lawiyawa shi ne Eleyazar ɗan Haruna, firist. An naɗa shi a kan waɗanda suke kula da wuri mai tsarki.
- Ƙidaya 3:33kusan 1490 K.H.
Kabilar Merari su ne Maliyawa da Mushiyawa; waɗannan su ne kabilar Merari.
- Ƙidaya 3:34kusan 1490 K.H.
Jimillar dukan jarirai maza daga wata ɗaya ko fiye, 6,200 ne.
- Ƙidaya 3:35kusan 1490 K.H.
Shugaban iyalan Merari shi ne Zuriyel ɗan Abihayil. Za su yi sansani arewa da tabanakul.
- Ƙidaya 3:36kusan 1490 K.H.
Kabilar Merari ne aka sa su lura da katakan tabanakul, sandunanta, dogayen sandunanta, tarukanta, dukan kayan aiki da kowane abin da ya danganci aikinsu,
- Ƙidaya 3:37kusan 1490 K.H.
da ginshiƙai kewaye da filin tare da rammuka da turaku da igiyoyinsu.