- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 1446–1406 BC
The Wilderness Years
Forty years of wandering in the desert test Israel's faith and prepare a new generation to enter the promised land.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Ƙidaya 1:51kusan 1490 K.H.
Duk sa’ad da za a gusar da tabanakul, Lawiyawa ne za su saukar da shi; kuma duk sa’ad da za a kafa shi, Lawiyawa ne za su yi haka. Duk wani dabam da ya je kusa da shi za a kashe shi.
- Ƙidaya 1:52kusan 1490 K.H.
Sauran Isra’ilawa za su zauna ƙungiya-ƙungiya, kowane mutum a ƙungiyarsa daidai bisa ga ƙa’idarsa.
- Ƙidaya 1:53kusan 1490 K.H.
Amma Lawiyawa za su kafa sansaninsu kewaye da tabanakul na Shaida. Don kada fushi yă fāɗo a kan al’ummar Isra’ilawa. Hakkin Lawiyawa ne su kula da tabanakul na Shaida.”
- Ƙidaya 1:54kusan 1490 K.H.
Isra’ilawa suka yi duk waɗannan kamar dai yadda Ubangiji ya umarci Musa.
- Ƙidaya 2:1kusan 1490 K.H.
Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna,
- Ƙidaya 2:2kusan 1490 K.H.
“Duk sa’ad da Isra’ilawa suka yi sansani, kowane mutum zai sauka a inda tutar ƙungiyar kabilarsa take. Sansanin zai kasance a kewaye da Tentin Sujada.”
- Ƙidaya 2:3kusan 1490 K.H.
Kabilar Yahuda za su yi sansani bisa ga ƙa’idarsu a gabas, wajen fitowar rana. Shugaban mutanen Yahuda kuwa shi ne Nashon ɗan Amminadab.
- Ƙidaya 2:4kusan 1490 K.H.
Yawan mutanen sashensa 74,600 ne.
- Ƙidaya 2:5kusan 1490 K.H.
Kabilar Issakar za su yi sansani biye da su. Shugabansu shi ne Netanel ɗan Zuwar.
- Ƙidaya 2:6kusan 1490 K.H.
Yawan mutanen sashensa 54,400 ne.
- Ƙidaya 2:7kusan 1490 K.H.
Kabilar Zebulun za su yi sansani biye da su. Shugabansu shi ne Eliyab ɗan Helon.
- Ƙidaya 2:8kusan 1490 K.H.
Yawan mutanen sashensa 57,400 ne.
- Ƙidaya 2:9kusan 1490 K.H.
Dukan mazan da aka ba su aiki a sansanin Yahuda bisa ga sashensu sun kai 186,400. Su ne za su ja gaba.
- Ƙidaya 2:10kusan 1490 K.H.
A kudu, a nan ne sashe sansanin mutanen Ruben a ƙarƙashin ƙa’idarsu, za su yi sansani. Shugaban mutanen Ruben shi ne Elizur ɗan Shedeyur.
- Ƙidaya 2:11kusan 1490 K.H.
Yawan mutanen sashensa 46,500 ne.
- Ƙidaya 2:12kusan 1490 K.H.
Kabilar Simeyon za su yi sansani biye da su. Shugaban mutanensa shi ne Shelumiyel ɗan Zurishaddai.
- Ƙidaya 2:13kusan 1490 K.H.
Yawan mutanen sashensa 59,300 ne.
- Ƙidaya 2:14kusan 1490 K.H.
Kabilar Gad za su zama na biye. Shugaban mutanensa shi ne Eliyasaf ɗan Reyuwel.
- Ƙidaya 2:15kusan 1490 K.H.
Yawan mutanen sashensa 45,650 ne.
- Ƙidaya 2:16kusan 1490 K.H.
Dukan mazan da aka ba su aiki a sansanin Ruben, bisa ga sashensu sun kai 151,450. Su ne za su zama na biyu in za a tashi.
- Ƙidaya 2:17kusan 1490 K.H.
Sa’an nan Lawiyawa ɗauke da Tentin Sujada za su kasance a tsakiyar sansani sa’ad da aka tashi tafiya. Za su kama hanya kamar yadda aka dokace su su zauna a sansani, kowa a wurinsa a ƙarƙashin ƙa’idarsu.
- Ƙidaya 2:18kusan 1490 K.H.
Ta wajen yamma kuma sashen Efraim za su yi sansani a ƙarƙashin ƙa’idarsu. Shugaban mutanensa, shi ne Elishama ɗan Ammihud.
- Ƙidaya 2:19kusan 1490 K.H.
Yawan mutanen sashensa 40,500 ne.
- Ƙidaya 2:20kusan 1490 K.H.
Kabilar Manasse ce za tă zama ta biye. Shugabansu shi ne Gamaliyel ɗan Fedazur.
- Ƙidaya 2:21kusan 1490 K.H.
Yawan mutanen sashensa 32,200 ne.