Tsallake zuwa abun ciki

circa 800–400 BC

The Hebrew Prophets

God speaks through Isaiah, Jeremiah, and the minor prophets—calling Israel to repentance and foretelling the coming Messiah.

3,706 ayoyi · 14 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Yunana 1:8kusan 862 K.H.

    Saboda haka suka tambaye shi suka ce, “Yanzu, gaya mana, dalilin da ya sa wannan masifa ta zo mana? Mene ne aikinka? Daga ina ka fito? Ina ne ƙasarka? Daga wacce kabila ce ka fito?”

  2. Yunana 1:9kusan 862 K.H.

    Sai ya amsa, “Ni mutumin Ibraniyawa ne, ina kuma bauta wa Ubangiji Allah na sama, wanda ya yi teku da tuddai.”

  3. Yunana 1:10kusan 862 K.H.

    Sai matuƙan jirgin suka tsorata ƙwarai, suka ce masa, “Wane irin mugun abu ne ka aikata haka?” (Sun gane cewa yana gudu ne daga wurin Ubangiji, domin ya riga ya faɗa musu.)

  4. Yunana 1:11kusan 862 K.H.

    Sai tekun ya daɗa rikicewa. Sai suka tambaye shi, “Me za mu yi da kai domin tekun yă daina hauka?”

  5. Yunana 1:12kusan 862 K.H.

    Ya amsa musu ya ce, “Ku ɗauke ni ku jefa a cikin teku, tekun zai kwanta. Na san cewa laifina ne ya jawo wannan babban hadirin da ya auka muku.”

  6. Yunana 1:13kusan 862 K.H.

    Maimakon mutanen su yi haka, sai suka yi ƙoƙari su tura jirgin ruwan zuwa bakin teku. Amma ba su iya ba, saboda iskar ta sa tekun ya yi ta ƙara hauka.

  7. Yunana 1:14kusan 862 K.H.

    Sai suka yi kuka ga Ubangiji suka ce, “Ya Ubangiji, in ka yarda kada ka bar mu mu mutu saboda ran mutumin nan. Kada ka yi mana hukuncin masu kisankai, gama kai ne, ya Ubangiji, ka ga ya gamshe ka.”

  8. Yunana 1:15kusan 862 K.H.

    Sa’an nan suka ɗauki Yunana suka jefar da shi daga jirgin, sai tekun ya kwanta.

  9. Yunana 1:16kusan 862 K.H.

    Ganin haka sai mutanen suka cika da tsoron Ubangiji, suka kuma miƙa wa Ubangiji hadaya, suka yi wa’adi da shi.

  10. Yunana 1:17kusan 862 K.H.

    Amma Ubangiji ya tanada wani babban kifi da zai haɗiye Yunana, Yunana kuwa ya yi yini uku da dare uku a ciki cikin kifin.

  11. Yunana 2:1kusan 862 K.H.

    Daga ciki cikin kifi, Yunana ya yi addu’a ga Ubangiji Allahnsa.

  12. Yunana 2:2kusan 862 K.H.

    Ya ce, “A cikin damuwata na yi kira ga Ubangiji, ya kuwa amsa mini. Daga cikin zurfi kabari na yi kiran neman taimako, ka kuwa saurari kukata.

  13. Yunana 2:3kusan 862 K.H.

    Cikin tashin hankali, ka jefa ni cikin zurfafa, a tsakiyar teku, ka kuma jujjuya ni a cikin ruwa; dukan raƙuman ruwanka da ambaliyarka sun bi ta kaina.

  14. Yunana 2:4kusan 862 K.H.

    Sai na ce, ‘An kore ni daga fuskarka; duk da haka zan sāke duba wajen haikalinka mai tsarki.’

  15. Yunana 2:5kusan 862 K.H.

    Ruwayen da suke kewaye da ni sun yi mini barazana, zurfi kuma ya kewaye ni, ciyayin ruwa suna nannaɗe kewaye da ni.

  16. Yunana 2:6kusan 862 K.H.

    Na nutsa har ƙarƙashin tuddai; a ƙarƙashin duniya, ka rufe ni har abada. Amma ka dawo da raina daga rami, Ya Ubangiji Allahna.

  17. Yunana 2:7kusan 862 K.H.

    “Sa’ad da na ji raina yana rabuwa da ni, na tuna da kai ya Ubangiji, addu’ata kuma ta kai gare ka, a haikalinka mai tsarki.

  18. Yunana 2:8kusan 862 K.H.

    “Waɗanda suka maƙale wa gumaka marasa amfani, sukan ƙyale alherin da zai kasance nasu.

  19. Yunana 2:9kusan 862 K.H.

    Amma ni, da waƙar godiya, zan miƙa tawa hadaya gare ka. Abin da na yi alkawari, shi ne zan yi. Ceto yakan zo ne kawai daga wurin Ubangiji.”

  20. Yunana 2:10kusan 862 K.H.

    Sai Ubangiji ya umarci kifin, kifin kuwa ya amayar da Yunana a gaɓan teku.

  21. Yunana 3:1kusan 862 K.H.

    Sa’an nan sai maganar Ubangiji ta zo wa Yunana sau na biyu.

  22. Yunana 3:2kusan 862 K.H.

    “Tafi babban birnin nan Ninebe, ka yi masa shelar saƙon da na ba ka.”

  23. Yunana 3:3kusan 862 K.H.

    Sai Yunana ya yi biyayya da maganar Ubangiji, ya tafi Ninebe. Ninebe birni ne da yake da muhimmanci, wanda sai an ɗauki kwana uku kafin a iya zaga shi.

  24. Yunana 3:4kusan 862 K.H.

    A rana ta fari, Yunana ya kama tafiya yana ratsa birnin. Sai ya yi shela cewa, “Nan da kwana arba’in za a hallaka Ninebe?”

  25. Yunana 3:5kusan 862 K.H.

    Mutanen Ninebe kuwa suka gaskata Allah. Aka yi shela a yi azumi, sai dukansu daga babba har zuwa ƙaraminsu, suka sa tufafin makoki.