- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa AD 30–62
The Early Church
Pentecost ignites a movement; Peter, Paul, and countless others carry the gospel from Jerusalem to the ends of the earth.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Ayyukan Manzanni 7:58kusan 33 M.
Suka ja shi zuwa bayan birnin suka kuma yi ta jifansa da duwatsu. Ana cikin haka, shaidun suka ajiye tufafinsu a wurin wani saurayi mai suna Shawulu.
- Ayyukan Manzanni 7:59kusan 33 M.
Yayinda suke cikin jifansa, sai Istifanus ya yi addu’a ya ce, “Ubangiji Yesu, ka karɓi ruhuna.”
- Ayyukan Manzanni 7:60kusan 33 M.
Sa’an nan ya durƙusa ya ɗaga murya ya ce, “Ubangiji, kada ka riƙe wannan zunubi a kansu.” Da ya faɗi haka, sai ya yi barci.
- Ayyukan Manzanni 8:1kusan 34 M.
Shawulu kuwa yana can, yana tabbatar da mutuwarsa. A wannan rana wani babban tsanani ya auka wa ikkilisiyar da take a Urushalima, sai duka suka warwatsu ko’ina a Yahudiya da Samariya, manzanni kaɗai ne suka rage.
- Ayyukan Manzanni 8:2kusan 34 M.
Mutane masu tsoron Allah suka binne Istifanus suka kuma yi makoki ƙwarai dominsa.
- Ayyukan Manzanni 8:3kusan 34 M.
Amma Shawulu ya fara hallaka ikkilisiya. Yana shiga gida-gida, yana jan maza da mata yana jefa su cikin kurkuku.
- Ayyukan Manzanni 8:4kusan 34 M.
Waɗanda aka wartsar suka yi ta wa’azin maganar a duk inda suka tafi.
- Ayyukan Manzanni 8:5kusan 34 M.
Filibus ya gangara zuwa wani birni a Samariya ya kuma yi shelar Kiristi a can.
- Ayyukan Manzanni 8:6kusan 34 M.
Sa’ad da taron mutane suka ji Filibus suka kuma ga abubuwan banmamakin da ya yi, sai duk suka mai da hankali sosai ga abin da ya faɗa.
- Ayyukan Manzanni 8:7kusan 34 M.
Mugayen ruhohi suka fiffito suna kururuwa daga cikin mutane da yawa, shanyayyu da guragu masu yawa suka sami warkarwa.
- Ayyukan Manzanni 8:8kusan 34 M.
Saboda haka aka yi farin ciki ƙwarai a birnin.
- Ayyukan Manzanni 8:9kusan 34 M.
To, akwai wani mutum mai suna Siman wanda ya kwana biyu yana yin sihiri a birnin har ya ba wa duk mutanen Samariya mamaki. Ya kuma yi taƙama cewa shi wani mai girma ne,
- Ayyukan Manzanni 8:10kusan 34 M.
dukan mutane kuwa, manyan da ƙanana, suka mai da hankali gare shi suka kuma ce, “Mutumin nan shi ne ikon Allah da aka sani a matsayin Iko Mai Girma”
- Ayyukan Manzanni 8:11kusan 34 M.
Suka bi shi domin ya daɗe yana ba su mamaki da sihirinsa.
- Ayyukan Manzanni 8:12kusan 34 M.
Amma da suka gaskata da Filibus sa’ad da yake wa’azin labari mai daɗi na mulkin Allah da kuma sunan Yesu Kiristi, sai aka yi musu baftisma, maza da mata.
- Ayyukan Manzanni 8:13kusan 34 M.
Siman kansa ya gaskata aka kuma yi masa baftisma. Ya kuma bi Filibus ko’ina, yana mamakin manyan alamu da ayyukan banmamakin da ya gani.
- Ayyukan Manzanni 8:14kusan 34 M.
Sa’ad da manzannin da suke a Urushalima suka ji cewa Samariya ta karɓi maganar Allah, sai suka aika musu da Bitrus da Yohanna.
- Ayyukan Manzanni 8:15kusan 34 M.
Da suka iso, sai suka yi musu addu’a domin su karɓi Ruhu Mai Tsarki,
- Ayyukan Manzanni 8:16kusan 34 M.
domin Ruhu Mai Tsarki bai riga ya sauka wa waninsu ba tukuna, an dai yi musu baftisma ne kawai a cikin sunan Ubangiji Yesu.
- Ayyukan Manzanni 8:17kusan 34 M.
Sa’an nan Bitrus da Yohanna suka ɗibiya hannuwansu a kansu, suka kuwa karɓi Ruhu Mai Tsarki.
- Ayyukan Manzanni 8:18kusan 34 M.
Sa’ad da Siman ya ga cewa ana ba da Ruhu ta wurin ɗibiya hannuwan manzannin, sai ya miƙa musu kuɗi,
- Ayyukan Manzanni 8:19kusan 34 M.
ya ce, “Ni ma ku ba ni wannan iyawa don kowa na ɗibiya wa hannuwana yă karɓi Ruhu Mai Tsarki.”
- Ayyukan Manzanni 8:20kusan 34 M.
Bitrus ya amsa ya ce, “Bari kuɗinka ya hallaka tare da kai, domin ka yi tsammani za ka iya saya kyautar Allah da kuɗi!
- Ayyukan Manzanni 8:21kusan 34 M.
Ba ruwanka da wannan hidimar, domin zuciyarka ba daidai take a gaban Allah ba.
- Ayyukan Manzanni 8:22kusan 34 M.
Ka tuba daga wannan mugunta ka kuma yi addu’a ga Ubangiji. Wataƙila zai gafarta maka don irin tunanin da yake a zuciyarka.