Tsallake zuwa abun ciki

circa AD 48–96

Letters to the Churches

Paul and other apostles write to strengthen, correct, and encourage the scattered churches across the Roman world.

2,767 ayoyi · 21 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Romawa 7:15kusan 60 M.

    Ban gane abin da nake yi ba. Don abin da nakan so yi, ba shi nakan yi ba, sai dai abin da nake ƙi, shi nake yi.

  2. Romawa 7:16kusan 60 M.

    In kuma na yi abin da ba na son yi, na yarda da cewa dokar aba ce mai kyau.

  3. Romawa 7:17kusan 60 M.

    Kamar dai yadda yake, ba ni kaina nake yinsa ba, sai dai zunubin da yake zaune a cikina ne.

  4. Romawa 7:18kusan 60 M.

    Gama na san cewa babu wani abin kirkin da yake zaune a cikina, wato, a mutuntakata. Gama sha’awar yin abu mai kyau kam ina da ita, sai dai ikon yin ne fa babu.

  5. Romawa 7:19kusan 60 M.

    Gama abin da nake yi ba shi ne abu mai kyau da nake so in yi ba; a’a, mugun da ba na so in yi, shi ne nake ci gaba da yi.

  6. Romawa 7:20kusan 60 M.

    To, in na yi abin da ba na so in yi, ba ni ba ne nake yinsa, sai dai zunubin nan da yake zaune a cikina.

  7. Romawa 7:21kusan 60 M.

    Saboda haka na gane wannan ƙa’ida ce take aiki a cikina. Sa’ad da nake so in yi abu mai kyau, sai in ga cewa mugun nan ne nake yi.

  8. Romawa 7:22kusan 60 M.

    Gama a ciki-cikina ina farin cikin da dokar Allah;

  9. Romawa 7:23kusan 60 M.

    amma ina ganin wata doka tana aiki a gaɓoɓin jikina, tana yaƙi da dokar hankalina, tana kuma sa in zama ɗaurarren dokar zunubin da take aiki a gaɓoɓin jikina.

  10. Romawa 7:24kusan 60 M.

    Kaitona! Wane ne zai cece ni daga wannan jiki mai mutuwa?

  11. Romawa 7:25kusan 60 M.

    Godiya ga Allah ta wurin Yesu Kiristi Ubangijinmu! Saboda haka fa, ni kaina a cikin hankalina, ni bawa ne ga dokar Allah, amma a mutuntaka, ni bawa ne ga dokar zunubi.

  12. Romawa 8:1kusan 60 M.

    Saboda haka, yanzu babu hukunci don waɗanda suke cikin Kiristi Yesu,

  13. Romawa 8:2kusan 60 M.

    gama ta wurin Kiristi Yesu dokar Ruhu mai ba da rai ta ’yantar da ni daga Dokar Musa.

  14. Romawa 8:3kusan 60 M.

    Gama abin da dokar ba tă iya yi saboda kāsawar mutuntaka ba, Allah ya yi shi sa’ad da ya aiko da Ɗansa a kamannin mutum mai zunubi, don yă zama hadaya ta zunubi. Ta haka, ya hukunta zunubi a cikin mutum mai zunubi.

  15. Romawa 8:4kusan 60 M.

    Ya yi haka domin yă cika bukatun adalcin doka a cikinmu, mu da ba ma rayuwa bisa ga mutuntaka, sai dai bisa ga Ruhu.

  16. Romawa 8:5kusan 60 M.

    Waɗanda suke rayuwa bisa ga mutuntaka sun kafa hankulansu a kan sha’awace-shawa’acen jiki; amma waɗanda suke rayuwa bisa ga Ruhu sun kafa hankulansu a kan abubuwan da Ruhu yake so.

  17. Romawa 8:6kusan 60 M.

    Ƙwallafa rai ga al’amuran halin mutuntaka ƙarshensa mutuwa ne, ƙwallafa rai ga al’amuran Ruhu kuwa rai ne da salama;

  18. Romawa 8:7kusan 60 M.

    hankalin mai zunubi na gāba da Allah. Ba ya biyayya da dokar Allah, ba kuwa zai iya yin haka ba.

  19. Romawa 8:8kusan 60 M.

    Waɗanda mutuntaka yake mulkinsu ba za su iya su gamshi Allah ba.

  20. Romawa 8:9kusan 60 M.

    Ku kam, ana mulkinku ba ta wurin mutuntaka ba, sai dai ta wurin Ruhu, in Ruhun Allah yana zaune a cikinku. In kuma wani ba shi da Ruhun Kiristi, shi ba na Kiristi ba ne.

  21. Romawa 8:10kusan 60 M.

    Amma in Kiristi yana a cikinku, jikinku matacce ne saboda zunubi, duk da haka ruhunku yana a raye saboda adalci.

  22. Romawa 8:11kusan 60 M.

    In kuwa Ruhu wannan da ya tā da Yesu daga matattu yana zama a cikinku, shi wanda ya tā da Kiristi daga matattu zai ba da rai ga jikunanku masu mutuwa ta wurin Ruhunsa, wanda yake zama a cikinku.

  23. Romawa 8:12kusan 60 M.

    Saboda haka ’yan’uwa, muna da hakki, amma ba na wanda za mu yi rayuwar mutuntaka da yake so ba.

  24. Romawa 8:13kusan 60 M.

    Gama in kuna rayuwa bisa ga mutuntaka, za ku mutu; amma in ta wurin Ruhu kuka kashe ayyukan jikin nan, za ku rayu.

  25. Romawa 8:14kusan 60 M.

    Domin waɗanda Ruhun Allah yake bi da su ne ’ya’yan Allah.