Tsallake zuwa abun ciki

Jerusalem

753 verses · 2 known names

An kuma san shi da: Jerusalem's

31.7700, 35.2300 Duba a Google Maps

Ayoyin da suka ambaci Jerusalem

Tace bisa littafi
  1. a shekara ta farko ta mulkinsa, ni, Daniyel na gane daga cikin littattafai, bisa ga maganar Ubangiji da aka faɗa wa annabi Irmiya, cewa zaman Urushalima kango zai kai shekara saba’in.

  2. “Ubangiji, kai mai adalci ne, amma a yau kunya ta rufe mu, mutanen Yahuda da mutanen Urushalima da na dukan Isra’ila, waɗanda suke kusa da kuma nesa, a dukan ƙasashen da ka warwatsa mu saboda rashin amincinmu a gare ka.

  3. Ka cika kalmomin da ka yi a kanmu da kuma a kan masu mulkinmu ta wurin kawo mana babban bala’i. A duniya duka ba a taɓa yin wani abu kamar yadda aka yi wa Urushalima ba.

  4. Ya Ubangiji, ta wurin kiyaye dukan ayyukanka na adalci, ka huce daga fushinka da hukuncinka da ka yi a kan Urushalima, birninka, tudunka mai tsarki. Zunubinmu da laifofin iyayenmu sun mai da Urushalima da kuma mutanenka abin ba’a ga dukan waɗanda suke kewaye da mu.

  5. “Sai ka sani ka kuma fahimci wannan; Tun daga sa’ad da aka kafa doka don a maido a kuma sāke gina Urushalima har sai Shafaffen nan, mai mulki, ya zo, za a yi shekara arba’in da tara, da shekara ɗari huɗu da talatin da huɗu. Za a sāke gina ta a yi mata tituna da mafaka.

  6. Amma dukan waɗanda suka nemi Ubangiji za su tsira. Kamar yadda Ubangiji ya ce, gama a Dutsen Sihiyona da Urushalima akwai ceto, a cikin waɗannan da Ubangiji ya kira.

  7. “A waɗancan kwanaki da kuma a wancan lokaci, sa’ad da zan maido da arzikin Yahuda da Urushalima,

  8. Kun sayar da mutanen Yahuda da na Urushalima ga mutanen Hellenawa, don ku aika da su nesa da ƙasarsu.

  9. Ubangiji zai yi ruri daga Sihiyona tsawa kuma daga Urushalima; duniya da sararin sama za su yi rawan jiki. Amma Ubangiji zai zama mafakar mutanensa, mafaka ga mutanensa Isra’ila.

  10. “Sa’an nan za ku san cewa ni, Ubangiji Allahnku, ina zaune a Sihiyona, dutsena mai tsarki. Urushalima za tă zama mai tsarki; baƙi ba za su ƙara mamaye ta ba.

  11. Za a zauna a Yahuda har abada Urushalima kuma daga tsara zuwa tsara.

  12. Ya ce, “Ubangiji ya yi ruri daga Sihiyona ya kuma yi tsawa daga Urushalima; wuraren kiwo duk sun bushe, dutsen Karmel kuma ya yi yaushi.”

  13. Zan sa wuta a Yahuda da za tă ƙone kagarun Urushalima.”

  14. A ranan nan kin tsaya kawai kina zuba ido yayinda baƙi suke washe dukiyar ɗan’uwanki, baƙi kuma suka shiga ta ƙofofinsa suka jefa ƙuri’a don a rarraba Urushalima, kin tsaya kina kallo kamar ɗaya daga cikin abokan gābansa.

  15. Wannan ƙungiyar Isra’ilawan da aka kwashe zuwa bauta da suke a Kan’ana za su mallaki ƙasar har zuwa Zarefat; waɗannan da aka kwashe zuwa bauta daga Urushalima da suke a Sefarad za su mallaki garuruwan Negeb.

  16. Maganar Ubangiji ta zo wa Mika mutumin Moreshet a zamanin Yotam, da na Ahaz, da kuma na Hezekiya, sarakunan Yahuda, Mika ya ga wahayi a kan Samariya da kuma a kan Urushalima. Ga abin da ya ce.

  17. Duk wannan zai faru saboda laifin Yaƙub, da kuma zunuban gidan Isra’ila ne. Mene ne laifin Yaƙub? Shin, ba Samariya ba ce? Ina ne maɗaukakan wuraren Yahuda? Shin, ba Urushalima ba ce?

  18. Gama raunin Samariya ba mai warkewa ba ne; ya bazu har Yahuda. Ya ma kai bakin ƙofar mutanena, har ma Urushalima da kanta.

  19. Mazaunan Marot sun ƙosa su ga alheri, amma Ubangiji ya sauko da azaba, har zuwa ƙofar Urushalima.

  20. kuka gina Sihiyona ta wurin zub da jini, Urushalima kuma ta wurin mugunta.

  21. Don haka, saboda ku, za a nome Sihiyona kamar gona, Urushalima kuma ta zama tarin juji, tudun haikali kuwa zai zama kurmin ƙayayyuwa.

  22. Al’ummai da yawa za su zo su ce, “Ku zo, bari mu haura zuwa dutsen Ubangiji, zuwa gidan Allah na Yaƙub. Zai koya mana hanyoyinsa, don mu yi tafiya cikin hanyoyinsa.” Doka za tă fita daga Sihiyona, maganar Ubangiji kuma daga Urushalima.

  23. Game da ke, ya hasumiyar tsaron garke, Ya mafaka Diyar Sihiyona, za a maido miki da mulkinki na dā, sarauta kuma za tă zo wa Diyar Urushalima.”

  24. “Zan miƙa hannuna gāba da Yahuda da kuma dukan mazaunan Urushalima. Zan datse raguwar Ba’al daga wannan wuri, da sunayen firistocin gumaka da na marasa sanin Allah,

  25. A wannan lokaci zan bincike Urushalima da fitilu in kuma hukunta waɗanda ba su kula ba, waɗanda suke kamar ruwan inabin da aka bar a ƙasan tukunya, waɗanda suke tsammani, ‘Ubangiji ba zai yi kome ba nagari ko mummuna.’