Tsallake zuwa abun ciki

Jerusalem

753 verses · 2 known names

An kuma san shi da: Jerusalem's

31.7700, 35.2300 Duba a Google Maps

Ayoyin da suka ambaci Jerusalem

Tace bisa littafi
  1. Ki rera, ya Diyar Sihiyona; ki tā da murya, ya Isra’ila! Ki yi murna ki kuma yi farin ciki da dukan zuciyarki, Ya Diyar Urushalima!

  2. A wannan rana za su cewa Urushalima, “Kada ki ji tsoro, ya Sihiyona; kada ki bar hannuwanki su raunana.

  3. Sa’an nan mala’ikan Ubangiji ya ce, “Ya Ubangiji Maɗaukaki, har yaushe za ka ci gaba da ƙi nuna wa Urushalima da kuma garuruwan Yahuda jinƙai, waɗanda kake fushi da su shekarun nan saba’in?”

  4. Sai mala’ikan da yake magana da ni ya ce, “Ka yi shelar maganan nan, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘Ina kishi domin Urushalima da Sihiyona,

  5. “Saboda haka, ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Zan komo Urushalima da jinƙai, a can ne za a sāke gina gidana. Za a kuma miƙe ma’auni a bisa Urushalima,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki.

  6. “Ci gaba da yin shela, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘Garuruwana za su sāke kwarara da wadata, Ubangiji kuma zai sāke yi wa Sihiyona ta’aziyya, yă kuma zaɓi Urushalima.’ ”

  7. Na tambayi mala’ikan da yake mini magana, na ce, “Mene ne waɗannan?” Ya amsa mini ya ce, “Waɗannan su ne ƙahonin da suka watsar da Yahuda, Isra’ila da kuma Urushalima.”

  8. Sai na yi tambaya, na ce, “Ina za ka?” Ya amsa mini ya ce, “Zan je in auna Urushalima, in ga yadda fāɗinta da tsawonta suke.”

  9. ya ce masa, “Yi gudu, gaya wa saurayin can cewa, ‘Urushalima za tă zama birni marar katanga domin mutane da dabbobi masu yawa ƙwarai za su kasance a cikinta.

  10. Ubangiji zai gāji Yahuda a matsayin rabonsa a cikin ƙasa mai tsarki zai kuma sāke zaɓi Urushalima.

  11. Ubangiji ya ce wa Shaiɗan, “Ubangiji ya tsawata maka, Shaiɗan! Ubangiji wanda ya zaɓi Urushalima, ya tsawata maka! Ashe, mutumin nan ba shi ne sandar da take ƙonewa da aka ciro daga cikin wuta ba?”

  12. Ashe, ba kalmomin da Ubangiji ya faɗi ke nan ta bakin annabawan farko ba sa’ad da Urushalima da garuruwan da suke kewaye da ita suke hutawa, suke cikin wadata, akwai kuma mutane a Negeb da yammancin gindin tuddai?’ ”

  13. Ga abin da Ubangiji ya ce, “Zan koma Sihiyona in zauna a Urushalima. Sa’an nan za a kira Urushalima Birnin Gaskiya, a kuma kira dutsen Ubangiji Maɗaukaki Dutse Mai Tsarki.”

  14. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Tsofaffi maza da mata za su sāke zauna a titunan Urushalima, kowanne da sanda a hannu saboda tsufa.

  15. Zan komo da su su zauna a Urushalima; za su zama mutanena, ni kuwa zan zama amintaccen Allahnsu mai adalci.”

  16. kada ku ji tsoro “saboda a yanzu na yi niyya in sāke yi wa Urushalima da Yahuda abu mai kyau.

  17. Mutane da yawa kuma da al’ummai masu ƙarfi za su zo Urushalima su nemi Ubangiji Maɗaukaki su kuma roƙe shi.”

  18. Ki yi murna ƙwarai, ya Diyar Urushalima! Ki yi sowa, Diyar Urushalima! Duba, ga sarkinki yana zuwa wurinki, mai adalci yana kuma da ceto, mai tawali’u yana kuma hawan jaki, yana a kan ɗan aholaki, a kan ’yar jaka.

  19. Zan ƙwace kekunan yaƙi daga Efraim, da kuma dawakan yaƙi daga Urushalima, za a kuma karya bakan yaƙi. Zai yi shelar salama ga al’ummai. Mulkinsa zai yaɗu daga teku zuwa teku, daga Kogi kuma zuwa ƙarshen duniya.

  20. “Zan sa Urushalima ta zama kwaf mai sa mutanen da suke a dukan kewayenta, jiri. Yaƙi zai kewaye Urushalima har yă shafi Yahuda ma.

  21. A ranan nan, sa’ad da duk al’umman duniya za su tayar mata, zan sa Urushalima ta zama dutsen da ba a iya matsarwa ga dukan al’ummai. Duk waɗanda suka yi ƙoƙari su matsar da shi za su ji ciwo.

  22. Sa’an nan shugabannin Yahuda za su ce a cikin zukatansu, ‘Mutanen Urushalima suna da ƙarfi domin Ubangiji Maɗaukaki shi ne Allahnsu.’

  23. “A ranan nan zan sa shugabannin Yahuda su zama kamar tukunyar wuta a tarin itacen wuta; kamar harshen wuta a dammunan hatsi. Za su ƙone dukan mutanen da suke kewaye da su hagu da dama, amma babu abin da zai taɓa mutanen Urushalima.

  24. “Ubangiji zai ceci wuraren zaman Yahuda da farko, don kada darajar gidan Dawuda da mazaunan Urushalima su fi na Yahuda daraja.

  25. A ranan nan Ubangiji zai kiyaye waɗanda suke zama a Urushalima, domin marasa ƙarfi a cikinsu su zama kamar Dawuda, gidan Dawuda kuma zai zama kamar Allah, kamar mala’ikan Ubangiji da yake tafiya a gabansu.