Tsallake zuwa abun ciki

Israel

1,007 ayoyi · 20 'yan gida

An kuma san shi da: Jacob

Ayoyin da suka ambaci Israel

Tace bisa littafi
  1. Ya albarkace su a wannan rana ya ce, “A cikin sunanku Isra’ila zai sa wannan albarka ‘Bari Allah yă sa ku zama kamar Efraim da Manasse.’ ” Saboda haka ya sa Efraim gaban Manasse.

  2. Sa’an nan Isra’ila ya ce wa Yusuf, “Ina gab da mutuwa, amma Allah zai kasance tare da ku

  3. Sai Yaƙub ya kira ’ya’yansa maza ya ce, “Ku tattaru don in faɗa muku abin da zai faru gare ku, a kwanaki masu zuwa.

  4. “Ku tattaru, ku saurara, ’ya’yan Yaƙub maza; ku saurari mahaifinku, Isra’ila.

  5. La’ananne ne fushinsu, mai tsanani ne ƙwarai, hasalarsu kuwa, muguwa ce ƙwarai! Zan warwatsa su cikin Yaƙub in kuma daidaita su cikin Isra’ila.

  6. “Dan zai tanada adalci wa mutanensa kamar ɗaya cikin kabilan Isra’ila.

  7. Amma bakansa yana nan daram hannuwansa masu ƙarfi ba sa jijjiguwa saboda hannun Maɗaukaki na Yaƙub, saboda Makiyayi, Dutsen Isra’ila,

  8. Dukan waɗannan su ne kabilu goma sha biyu na Isra’ila, kuma abin da mahaifinsu ya faɗa musu ke nan sa’ad da ya albarkace su, yana ba kowane albarkar da ta dace da shi.

  9. Sa’ad da Yaƙub ya gama ba da umarnan ga ’ya’yansa maza, sai ya ɗaga ƙafafunsa zuwa gado, ya ja numfashinsa na ƙarshe, aka kuwa tara shi ga mutanensa.

  10. Sa’an nan Yusuf ya umarci masu maganin da suke yin masa hidima, su shafe mahaifinsa Isra’ila da maganin hana ruɓa. Saboda haka masu maganin suka shafe shi da maganin hana ruɓa.

  11. Sai Yusuf ya ce wa ’yan’uwansa, “Ina gab da mutuwa. Amma tabbatacce Allah zai taimake ku, yă fid da ku daga wannan ƙasa zuwa ƙasar da ya alkawarta da rantsuwa wa Ibrahim, Ishaku da kuma Yaƙub.”

  12. Yusuf kuwa ya sa ’ya’yan Isra’ila maza suka yi rantsuwa, ya kuma ce, “Tabbatacce Allah zai taimake ku, ku kuma dole ku ɗauki ƙasusuwana, ku haura da su daga wannan wuri.”

  13. Waɗannan su ne sunayen ’ya’yan Isra’ila maza, waɗanda suka tafi Masar tare da Yaƙub; kowanne da iyalinsa.

  14. Zuriyar Yaƙub duka sun kai mutum saba’in. Yusuf ya riga ya kasance a Masar.

  15. amma Isra’ilawa sun riɓaɓɓanya, suka kuma yi ta haihuwa sosai, suka yi yawan sosai, har ƙasar ta cika da su.

  16. Ya ce wa mutanensa, “Duba Isra’ilawa sun yi yawa, sun fi ƙarfinmu.

  17. Amma duk da wannan ƙarin wulaƙancin da ake yi musu, su kuwa sai daɗa riɓaɓɓanya suke ta yi. Sai tsoron Isra’ilawa ya ƙaru a zuciyar Masarawa,

  18. ganin haka sai Masarawa suka ƙara musu wahala.

  19. Ana nan dai, a kwana a tashi, sai sarkin Masar ya mutu. Isra’ilawa suka yi kuka mai zafi saboda bautarsu mai wuya, sai kukar neman taimakonsu saboda bauta, ya kai wurin Allah.

  20. Allah kuwa ya ji kukansu sai ya tuna da alkawarinsa da Ibrahim da Ishaku da Yaƙub.

  21. Sai Allah ya dubi Isra’ilawa, ya kuma damu da su.

  22. Sai Allah ya ce, “Ni ne Allah na kakanninka, Allah na Ibrahim, Allah na Ishaku da kuma Allah na Yaƙub.” Da jin wannan, sai Musa ya ɓoye fuskarsa, domin ya ji tsoro yă dubi Allah.

  23. Yanzu kukan Isra’ilawa ya kai gare ni, na kuma ga yadda Masarawa suke wulaƙanta su

  24. To, fa, sai ka tafi. Ina aikan ka wurin Fir’auna don ka fitar da mutanena Isra’ilawa daga Masar.”

  25. Amma Musa ya ce wa Allah, “Wane ni in tafi wurin Fir’auna, in kuma fitar da Isra’ilawa daga Masar?”