Tsallake zuwa abun ciki

Israel

1,007 ayoyi · 20 'yan gida

An kuma san shi da: Jacob

Ayoyin da suka ambaci Israel

Tace bisa littafi
  1. Waɗannan su ne sunayen ’ya’yan Isra’ila maza (Yaƙub da zuriyarsa) waɗanda suka tafi Masar, Ruben ɗan farin Yaƙub.

  2. Waɗannan su ne ’ya’yan Liyatu maza da ta haifa wa Yaƙub a Faddan Aram, ban da ’yarsa Dina. ’Ya’yansa maza da mata duka, mutum talatin da uku ne.

  3. Waɗannan su ne ’ya’yan da Zilfa ta haifa wa Yaƙub, ita ce Laban ya ba wa ’yarsa Liyatu. ’Ya’yan duka, su sha shida ne.

  4. ’Ya’yan Yaƙub maza waɗanda Rahila ta haifa su ne, Yusuf da Benyamin.

  5. Waɗannan su ne ’ya’yan Rahila maza waɗanda ta haifa wa Yaƙub, dukansu mutum goma sha huɗu ne.

  6. Waɗannan su ne ’ya’ya mazan da Bilha ta haifa wa Yaƙub, ita ce Laban ya ba wa ’yarsa Rahila. ’Ya’yan suka su bakwai ne.

  7. Dukan waɗanda suka tafi Masar tare da Yaƙub, waɗanda suke zuriyarsa kai tsaye ban da matan ’ya’yansa maza, su mutum sittin da shida ne.

  8. In aka haɗa da ’ya’yan nan maza guda biyu waɗanda aka haifa wa Yusuf a Masar, membobin iyalin Yaƙub, waɗanda suka tafi Masar, duka su saba’in ne.

  9. sai Yusuf ya kintsa keken yaƙinsa ya haura zuwa Goshen don yă taryi mahaifinsa, Isra’ila. Nan da nan da isowar Yusuf a wurin mahaifinsa, sai ya rungumi mahaifinsa, ya yi kuka na dogon lokaci.

  10. Isra’ila ya ce wa Yusuf, “Yanzu ina a shirye in mutu, da yake na gani da kaina cewa har yanzu kana da rai.”

  11. Sa’an nan Yusuf ya shigar da Yaƙub mahaifinsa, ya gabatar da shi a gaban Fir’auna. Bayan Yaƙub ya albarkaci Fir’auna,

  12. sai Fir’auna ya tambaye shi, “Shekarunka nawa da haihuwa?”

  13. Yaƙub kuwa ya ce wa Fir’auna, “Shekarun hijirata, shekaru ɗari da talatin ne. Shekaruna kaɗan ne cike da wahala, ba za a kuwa daidaita su da shekarun hijirar kakannina ba.”

  14. Sai Yaƙub ya albarkaci Fir’auna, ya yi masa bankwana, sa’an nan ya fita.

  15. To, Isra’ilawa suka zauna a Masar a yankin Goshen. Suka mallaki filaye a can, suka riɓaɓɓanya suka ƙaru ƙwarai.

  16. Yaƙub ya yi zama a Masar shekaru goma sha bakwai, yawan shekarunsa duka sun zama ɗari da arba’in da bakwai.

  17. Sa’ad da lokaci ya gabato da Isra’ila zai mutu, sai ya kira ɗansa Yusuf, ya ce masa, “Ka yi mini wannan alheri, ka sa hannunka ƙarƙashin cinyar ƙafata, ka yi mini alkawari saboda ina roƙonka kaɗa ka bizne ni a Masar,

  18. Yaƙub ya ce, “Ka rantse mini.” Sai Yusuf ya rantse masa, Isra’ila kuwa ya yi godiya ga Allah yayinda ya jingina a kan sandansa.

  19. Sa’ad da aka faɗa wa Yaƙub, “Ɗanka Yusuf ya zo gare ka,” sai Isra’ila ya ƙoƙarta ya tashi ya zauna a kan gado.

  20. Yaƙub ya ce wa Yusuf, “Allah Maɗaukaki ya bayyana gare ni a Luz a ƙasar Kan’ana, a can ya albarkace ni

  21. Sa’ad da Isra’ila ya ga ’ya’yan Yusuf maza, sai ya yi tambaya, “Su wane ne waɗannan?”

  22. Yanzu fa idanun Isra’ila sun fara rasa ƙarfi saboda tsufa, har ba ya iya gani sosai. Saboda haka Yusuf ya kawo ’ya’yansa maza kusa da shi, sai mahaifinsa ya sumbace su ya rungume su.

  23. Isra’ila ya ce wa Yusuf, “Ban yi tsammani zan ga fuskarka kuma ba, yanzu kuwa Allah ya bar ni in ga ’ya’yanka su ma.”

  24. Yusuf ya ɗauke su biyu, Efraim a damansa zuwa hagun Isra’ila, Manasse kuma a hagunsa zuwa hannun daman Isra’ila, ya kuma kawo su kusa da shi.

  25. Amma Isra’ila ya miƙa hannun damansa ya sa shi a kan Efraim, ko da yake shi ne ƙaramin, ta wurin harɗewa hannuwansa, ya sa hannun hagunsa a kan Manasse, ko da yake Manasse ne ɗan farinsa.