Tsallake zuwa abun ciki

Israel

1,007 ayoyi · 20 'yan gida

An kuma san shi da: Jacob

Ayoyin da suka ambaci Israel

Tace bisa littafi
  1. To, a lokacin, sai shugabannin iyalan Lawiyawa suka je wurin Eleyazar firist, Yoshuwa ɗan Nun da kuma shugabannin sauran iyalan kabilu na Isra’ila a

  2. Saboda haka kamar yadda Ubangiji ya umarta, sai Isra’ilawa suka ba wa Lawiyawa waɗannan garuruwa da wuraren kiwo daga cikin gādonsu.

  3. Haka Isra’ilawa suka ba wa Lawiyawa waɗannan garuruwa da wuraren kiwo masu kyau, yadda Ubangiji ya umarta ta wurin Musa.

  4. Jimillar birane da wurarensu na kiwon da aka ba Lawiyawa daga cikin mallakar jama’ar Isra’ila guda arba’in da takwas ne.

  5. Saboda haka sai mutanen Ruben, mutanen Gad da kuma rabin mutanen kabilar Manasse, suka bar Isra’ilawa a Shilo cikin Kan’ana don su koma Gileyad, ƙasarsu, wadda suka samu bisa ga umarnin Ubangiji ta wurin Musa.

  6. Sa’ad da Isra’ilawa suka ji cewa sun gina bagade a iyakar Kan’ana, a Gelilot kusa da Urdun wajen gefensu na Isra’ilawa,

  7. sai dukan Isra’ilawa suka taru a Shilo don su je su yaƙe su.

  8. Saboda haka sai Isra’ilawa suka aiki Finehas ɗan Eleyazar, firist, zuwa ƙasar Gileyad, wurin mutanen Ruben, mutanen Gad da kuma rabin mutanen kabilar Manasse.

  9. Sai Finehas ɗan Eleyazar, firist, ya ce wa mutanen Ruben, mutanen Gad da kuma rabin mutanen kabilar Manasse, “Yau mun san Ubangiji yana tare da mu, domin ba ku yi wa Ubangiji rashin aminci cikin wannan abu ba. Yanzu kun kuɓutar da Isra’ilawa daga hannun Ubangiji.”

  10. Sai Finehas ɗan Eleyazar, firist, da shugabannin suka koma Kan’ana daga saduwa da mutanen Ruben da mutanen Gad a Gileyad, suka kai wa Isra’ilawa rahoto.

  11. Isra’ilawa suka ji daɗin rahoton da suka ji, suka kuma yi wa Allah yabo. Ba su sāke yin maganar zuwa yaƙi don su rushe ƙasar da mutanen Ruben da mutanen Gad suke ciki ba.

  12. ga Ishaku kuwa na ba shi Yaƙub da Isuwa. Na ba Isuwa ƙasar kan tudu ta Seyir, amma Yaƙub da ’ya’yansa maza suka gangara zuwa Masar.

  13. Aka kuma binne ƙasusuwan Yusuf da aka kawo daga Masar, a Shekem a wurin da Yaƙub ya saya da azurfa ɗari daga ’ya’yan Hamor, babban Shekem. Wurin ya zama gādon zuriyar Yusuf.

  14. Bayan da Yoshuwa ya rasu, Isra’ilawa suka tambayi Ubangiji suka ce, “Wane ne zai fara tafiya don yă yaƙi Kan’aniyawa dominmu?”

  15. Da mala’ikan Ubangiji ya faɗa wa dukan Isra’ilawa waɗannan abubuwa, sai mutane suka yi kuka mai zafi,

  16. Bayan Yoshuwa ya sallami Isra’ilawa, sai suka tafi don su mallaki ƙasar, kowa da nasa gādon.

  17. Sai Isra’ilawa suka yi mugaye abubuwa a gaban Ubangiji suka kuma bauta Ba’al.

  18. (ya yi haka ne domin yă koya wa zuriyar Isra’ilawa waɗanda ba su taɓa yin yaƙi a dā ba),

  19. Isra’ilawa suka zauna tare da Kan’aniyawa da Hittiyawa, Amoriyawa, Ferizziyawa, Hiwiyawa da kuma Yebusiyawa.

  20. Isra’ilawa suka aikata mugunta a gaban Ubangiji; suka manta da Ubangiji Allahnsu suka kuma bauta wa Ba’al da Ashera.

  21. Fushin Ubangiji kuwa ya yi ƙuna a kan Isra’ila har ya sayar da su ga Kushan-Rishatayim sarkin Aram-Naharayim, a wurinsa ne Isra’ilawa suka zama bayi shekara takwas.

  22. Amma da suka yi kuka ga Ubangiji, sai ya tad musu da mai ceto, Otniyel ɗan Kenaz, ƙanen Kaleb wanda ya cece su.

  23. Isra’ilawa suka sāke aikata mugayen ayyuka a gaban Ubangiji, saboda sun aikata wannan mugunta sai Ubangiji ya ba wa Eglon sarkin Mowab ƙarfi a kan Isra’ila.

  24. Isra’ilawa suka zama bayin Eglon sarkin Mowab shekara goma sha takwas.

  25. Isra’ilawa suka sāke yin kuka ga Ubangiji, ya kuwa ba su mai ceto, Ehud, wani bahago, ɗan Gera daga kabilar Benyamin. Isra’ilawa suka aike shi da haraji wurin Eglon sarkin Mowab.