Tsallake zuwa abun ciki

Israel

1,007 ayoyi · 20 'yan gida

An kuma san shi da: Jacob

Ayoyin da suka ambaci Israel

Tace bisa littafi
  1. Sa’an nan dukan Isra’ilawa daga Dan zuwa Beyersheba kuma daga ƙasar Gileyad mutane kamar mutum guda suka fito suka taru a gaban Ubangiji a Mizfa.

  2. (Mutanen Benyamin suka ji cewa Isra’ilawa sun haura zuwa Mizfa.) Sa’an nan Isra’ilawa suka ce, “Gaya mana yadda wannan mugun abu ya faru.”

  3. To, dukanku Isra’ilawa, sai ku yi magana ku kuma yanke hukuncinku.”

  4. Yanzu fa sai ku fitar da waɗannan ’yan iskan da suka aikata wannan abu na Gibeya don mu kashe su mu kawar da mugunta daga Isra’ila!” Amma mutanen Benyamin ba su saurari ’yan’uwansu Isra’ilawa ba.

  5. Daga biranensu suka tattaru a Gibeya don su yaƙi Isra’ilawa.

  6. Sai Isra’ilawa suka haura zuwa Betel suka nemi nufin Allah, suka ce, “Wane ne a cikinmu zai fara fāɗa wa mutanen Benyamin?” Ubangiji ya ce, “Yahuda ce za tă fara.”

  7. Kashegari sai Isra’ilawa suka tashi suka kafa sansani kusa da Gibeya.

  8. Isra’ilawa suka haura suka yi kuka a gaban Ubangiji, har yamma, suka nemi nufin Ubangiji. Suka ce, “Mu sāke koma yaƙi da mutanen Benyamin, ’yan’uwanmu?” Ubangiji ya ce, “Ku haura ku fāɗa musu.”

  9. Sai Isra’ilawa suka matsa kusa da Benyamin a rana ta biyu.

  10. A wannan lokaci, da mutanen Benyamin suka fito daga Gibeya don su yaƙe su, sai suka sāke kashe Isra’ilawa dubu goma sha takwas, dukansu ɗauke da takuba.

  11. Sa’an nan Isra’ilawa, dukan mutane, suka haura zuwa Betel, a can suka zauna suna kuka a gaban Ubangiji. Suka yi azumi a wannan rana har yamma suka miƙa hadayun ƙonawa da hadayun salama ga Ubangiji.

  12. Isra’ilawa suka nemi nufin Ubangiji (A kwanakin nan akwatin alkawarin Allah yana can,

  13. Suka haura su kara da mutanen Benyamin a rana ta uku suka ja dāgā a Gibeya kamar dā.

  14. Yayinda mutanen Benyamin suna cewa, “Muna cin nasara a kansu kamar dā,” Isra’ilawa kuwa suna cewa, “Mu yi ta jan da baya mu janye su daga birni zuwa kan hanyoyi.”

  15. Ubangiji kuwa ya fatattake mutanen Benyamin a gaban Isra’ila; a ranar kuwa Isra’ilawa sun kashe mutum 25,100 na mutanen Benyamin, dukansu ɗauke da takuba.

  16. Sa’an nan Isra’ilawa suka ce, “Wace kabila ce cikin kabilan Isra’ila ba tă zo taro a gaban Ubangiji ba?” Gama an yi rantsuwa cewa duk wanda ya kāsa zuwa taro a gaban Ubangiji a Mizfa lalle a kashe shi.

  17. To, Isra’ilawa suka yi juyayin ’yan’uwansu, mutanen Benyamin. “Yau an hallaka kabila daga cikin Isra’ila.

  18. Ba za mu iya ba su ’yan matanmu su zama matansu ba, da yake mu Isra’ilawa mun riga mun yi wannan rantsuwa cewa, ‘La’ananne ne wanda ya ba da ’yarsa aure ga mutum Benyamin.’

  19. A lokacin, Isra’ilawa sun bar wurin suka tafi gida zuwa ga kabilansu da zuriyoyinsu, kowane zuwa gādonsa.

  20. Na zaɓi mahaifinka daga cikin dukan kabilar Isra’ila yă zama firist nawa don yă yi hidima a bagade, don yă ƙona turare mai ƙanshi, don kuma yă sanya doguwar riga a gabana. Na kuma ba wa iyalin mahaifinka dukan hadaya ta ƙonawa da Isra’ila suka miƙa.

  21. Sai Isra’ilawa suka rabu da gumakan Ba’al da Ashtarot suka bauta wa Ubangiji kaɗai.

  22. Sa’ad da suka taru a Mizfa, suka kawo ruwa suka zuba a gaban Ubangiji. A wannan rana suka yi azumi suka tuba, suka ce, “Mun yi wa Ubangiji zunubi!” Sama’ila kuwa ya zauna a Mizfa ya yi mulkin Isra’ilawa.

  23. Da Filistiyawa suka ji cewa Isra’ila sun taru a Mizfa, sai shugabanninsu suka zo don su yaƙe Isra’ila. Da Isra’ilawa suka ji labarin, sai suka tsorata saboda Filistiyawa.

  24. Suka ce wa Sama’ila, “Kada ka fasa kai kukanmu ga Ubangiji Allahnmu saboda mu, don yă cece mu daga hannun Filistiyawa.”

  25. Yana da ɗa mai suna Shawulu, wani kyakkyawan saurayi. A cikin mutanen Isra’ila ba wanda ya fi shi kyau, ya kuma fi kowa tsaye.